Skip to content
Part 8 of 15 in the Series Zuciya by Khadija Muhammad Shitu (K_Shitu)

Nafi na kwance kan gado ita kaɗai ta yi ɗaiɗaya sai dariya take yi kamar me matsalar ƙwaƙwalwa. Da ta tuna irin taɓargazar da ta danƙara a rugarsu sai ta kuma fashewa da dariyar, da kuma irin yadda Inna Hure ta saita ta lokaci ɗaya ta nutsu ta sha wahala.

Ta wani cije leɓe cike da zallar mugunta tana hararo irin rashin mutuncin da za ta shuka musu idan ta samu dama. Hinde da ke shigowa ta tsaya tana kallon ta, cikin zuciyarta tana ayyana irin yarintar da ke ɗawainiya da Nafin da rashin sanin ciwon kai. Ta ƙarasa cikin ɗakin tana girgiza kai, Sai lokacin ma Nafin ta lura da ita, ta ɗan tsagaita da dariyar tana toshe baki. “Nafi anya ba ki da Taɓin ƙwaƙwalwa ko dai kin zare ne?”. Cewar Hinde tana kallon ta.

Ta yi shiru tana sunkuyar da kai ƙasa cikin jin kunya. Matsowa ta yi kusa da ita ta zauna ta fara mata magana, “wai Nafi anya ba ki da Aljannu? Ɗazun nan kika dawo ba ki min magana ba kika shige kewaye kika fito ina ta tambayarki yadda kuka ƙare da su Hajiya baturiya, Allah ya sa ba ki musu sakarci ba, ina ta miki magana kin yi banza kin ƙyale ni, na fita Unguwa na dawo yanzu kuma kina dariya, me suka ce miki ne wai?” Cike da zallar mamaki Nafi ta ɗago tana Kallonta. Ta ɗan yi jim sai kuma ta ce “wace ne Baturiya ni kuma gaskiya ni dai ban hita ba ina nan tin shahe ban tashi ba”.

Ta yi mata wani kallo a harzuƙe ta ce, “Uwarki Nafi! Ni za ki maida sokuwa, idan ba ki fita ba tun safe har yanzu da duhu ya fara gidan uban wa kika ci abinci kika chanza kaya ke fa munafuka ce?” Ta yi Narai-narai da idanuwa ta ce, “na ranse fa..” Katse ta Hinde ta yi tana tsaki ta ce “yi mini shiru zararriya, lallai ta tabbata maganar Hure ba ki da hankali sam Mts! In ban da iskanci mahaukaciya kike son maida ni ko me?” Sai kawai ta ga hawaye na zuba daga idanun Nafin ta zabga mata harara ta miƙe ta shige toilet cike da jin Haushin ta. Tagumi Nafi ta yi har ta rufe ƙofar Toilet ɗin, ita dai Allah ya sani yau tun safe ba ta je ko ina ba tana nan zaune.

Matsalarta ɗaya ta kasa tunanin abinda ya faru bayan idonta, dan duk wani abu da ya faru da ta yi tunani sai ta riƙa ganin komai kan idonta, amma sam ita ba ta ga Hinde ta fita ba ko wani ya yi wani abu, ga shi kuma tun da ta zo ta yi tunanin Baffanta amma ta kasa ganin komai da ya dangance sa, saɓanin da tana rugarsu komai ya faru a bayan idonta ko da bai shafe ta ba da ta yi tunanin abun sai ta dinga gani kan idonta tamkar a lokacin abu ke faruwa. Ta buga uban tagumi tana ƙoƙarin tunani har da rufe idanuwa amma ba abinda ta gani. Ita dai wasu lokuta ta sha tambayar kanta ko dai mayyar ce kamar yadda Fulanin Rugarsu ke faɗi, sai kuma ta yi dariya kawai ta tuna maganganun Mahaifiyarta.

Ita kaɗai ta fara surutu cikin harshen fulatanci Babata wai kina ina ne ina buƙatarki, “Wayyo Hammana Baffana, ni fa ban tahi ko ina ba ku hiɗi ma Hinde”.

Hinde da fitowar ta kenan ta ji abinda Nafin ke faɗi har da hawayenta, sai kawai tai dariya cike da shirme ita ma ta fara tunanin me ma ya sa za ta biye ma Nafin Dan ta san ko chan ba hankali ya ishe ta ba idan tana abubuwa wasu lokutan kamar aljana.

“Hum! Nafi ke dai wallahi ba ki gajiya da shiririta yarinta na damunki. Ke ma da laifinki fa ai ba abun da hankali zai ɗauka ba ne, ɗazu ki dawo daga wajen su hajjaju yanzu kuma ki kawo man wani busasshen rainin wayaunki wai ke kina nan tun da sahe, wallahi ba ‘yar rainin wayau irinki, kin ga dole raina ya ɓaci ai ba wasa nake maki ba ah to, ni ta shi in shirya ki mu je ayi maki kwalliya”.

Sumi-sumi ta miƙe Hinde ta buɗe Trollyn da Hajjaju ta ba ta, ta duba riga da wandon da ta ce Nafin ta sanya ta fiddo su wando baƙi sai rigar fara da kaɗan ta wuce cibi sai bazarta da ta ƙawata rigar. Wandon kuma ya yi kyau me yanka Crazy da kuma High-hills takalma ‘yan daidai. Ta tsare ta ta shirya ta, sai wani sussune kai take cikin jin kunya.

Ita kanta Hinden sai da ta ce wai dan tsananin kyan da Nafin ta yi, kayan sun zauna ɗas kan fatarta me haske, duk da har lokacin da ka kalle ta za ka fahimci rashin wayewa tattare da ita, da kuma fatarta da ba ta ida washewa ba. Ta kama hannunta tana nuna mata yanldda za ta yi tafiya da takalmin da gargaɗin da ta yi mata kan nutsuwa, sannan suka fice, Nafi na tafiya da ƙyar da wandon da rigar sun bayyana ƙirar jikinta ga kuma kayan da Hinden ta ba ta ta sanya sun sake ƙara mata girma da na jiki, Suka fito zuwa ɗakin da Dee me Makeup ɗin take, suka shiga Nafi sai gurɗewa take dan takalman sun fi ƙarfinta, saboda ita tun da take a rayuwarta ba ta taɓa ganinsu ba sai yau ɗin.

‘Yan matan wurin sai chaɓa mata maganganu suke yi a kaikaice, abun kuma ya ƙona mata rai musamman yadda suke kushe gashinta saboda hassada da baƙin ciki, ita dai ta yi shiru ranta a ɓace. Dee ta matso ta fara mata light makeup me nutsattsen kyau. Nan fa ido ya sake yi mata yawa duk ta yi bala’in tsarguwa har aka gama kwalliyar zuciyar ‘yan matan da yawansu baƙiƙƙirin saboda jarababben kishin tsiya, sai yatsina suke suna abubuwa.

Ta yi matsanancin kyau sosai fiye da tunani ga idanuwanta da suka sha eyeliner da light eyeshow sun yi kyau me zautarwa da rikita ɗanAdam sam ba ta yi kama da bil’adama ba, Ga ƙaramin madaidaicin bakinta da aka saka lipstick sai sheƙi yake da maiƙo kamar wata aljana.

Tana ɗebo idanuwa ‘Yanmatan da suka santa suka tsorata sosai a sace duk suka fice cike da fargaba dan ta yi wani irin kyau sosai kamar ba ita ba dan dama Dee ta iya kwalliya kamar hauka, ba ta yi ma ƙananu sai jiga-jigai yarinyar Hajjaju ce ita kanta me kuɗi ce sosai. Aka sake gyara mata Gashi aka saka Ribborn me ƙyalƙyali aka yi packing gashin ta fito gwanin ban sha’awa ita kanta Sai da ta ɗan tsorata da irin kyan da Nafin ta yi shi ya sa ko photo ma ba ta yi mata ba. Hinde sai washe haƙora take yi, saboda farinciki, suka miƙe tana ma Dee godiya suka koma nasu ɗakin.

Gaban madubi ta tsaya da ita, Nafi tun da ta fara kallon kanta ta ruɗe sosai sai zare idanuwa take cike da jin tsoron kanta, sai ta nuna ta cikin mirror ɗin ta tambayi Hinde wacece ta ba ta amsa ita ce, amma sai ta shiga girgiza kai. Faɗi take Wai duk abinda ta yi sai wannan Aljanar ta yi, ta fiddo harshe sai kawai ta ga ita ma ta cikin mirrorn wacce take faɗi a matsayin ba ita ba wata ta yi. Sai da Hinde ta yi mata bayanin yadda Mirror yake da yadda za ta ga kanta sai kuma ta ƙara ma da faɗi mata to mi ya sa ɗazu ba ta ƙi yarda ita ba ce sannan ta ɗan nutsu, amma ta yi zuru sai kallon kanta take yi cike fa tantama.

Ba maganar salla daga Hinden har Nafi, ƙarfe 7:20 ƙarar shigowar motoci ta cika gidan har cikin ɗaki su Nafi ma na ji.

Kafin ka ce wani abu gidan ya cike da motoci, babu abinda ke tashi a harabar gidan da aka ƙawata sai kiɗa ‘yan matan sun yi gayu na gani na faɗa.

Manyan mutane me masu muƙami da Arziƙi suka kawo ziyara Mata da maza, an ƙawata inda za su zauna sosai.

“Dalla Nafi ki yi sauri ki fito wannan wane irin abu ne Mts! Kin san kowa ya taru amma kin tsaida mu dan tsabar rainin wayau, in kin ga dama ki ɓata kwalliyar” Hinde da ke tsaye tuntuni ta gama shirinta Nafi kawai take jira ta fito daga bayi amma shiru ta faɗa cike da masifa tana jan guntun tsaki. Ba ta ƙara jimawa ba ta fito tana ba ta haƙuri, ta sake fesa mata tsadaddun turaruka suka fito a tare.

Yadda Nafin ke tafiya a hankali saboda takalman da ke ƙafarta ba ƙaramin ba da chitta ya yi ba, Hinde ma ta yi kyau ita ce ta ruƙo hannunta, har suka fito harabar gidan, idanuwa suka dawo kansu sai kallon Nafin ake yi kamar za a cinye ta, ga gashinta a waje parking ɗin shi kawai aka yi ya bazo har kafaɗunta, ga wadataccen hasken da ya haska su gabanta sai faɗuwa yake yi, Hinde ta sake damƙar Hannunta suka nufi wani teburi suka zauna, me zuba abinci ya kawo musu abinci da snacks da Lemu sai ruwa. “Nafi dan Allah kar ki kunyata mu, kuma ki saki jikinki” Hinde ta raɗa mata a kunne. Kaɗan suka ci snaks ɗin masu rawa suka fara sai liƙi ake musu, suna sake dagewa.

Wata Hamshaƙiyar mace ce ta matso kusa da teburin su Nafi ta zauna tana ƙare mata kallo, ta matso da kujerarta dab da ta Nafi tana murmushi ta ce, “Beauty sunan ki fa” cikin jin tsoro ta ba ta amsa “Nafi”.

Ta kamo hannayen Nafi ta ɗan matsa cikin nata tana aika mata da wani shu’umin kallo. Sai kuma ta miƙe ta fara tafiya ta ƙarisa inda Hajjaju da Hajiya Baturiya suke ta yi ma Hajjaju raɗa a kunne, sannan ta koma ta zauna ta kasa ta tsare ta sa ido kan duk wani motsin Nafin.

*****

Cikin jin haushi Abdul ya biyo bayanshi ya fiddo key ɗin mota daga Aljihu ya shiga ya buɗe motar Dr A na nan tsaye, ya tada motar ya yi banza ya ƙyale shi, ya shigo ya zauna seat ɗin me zaman banza shi ma bai kula shi ba, ya ja motar har suka iso gidan ya yi Parking bai tanka masa ba, ya buɗe motar ya fice shi ma bai tanka masa ba, ya ja motar ya bar Gidan.

Har zai shiga Sashensa sai kuma ya fasa ya nufi parlourn Ammi da sallamarsa ciki-ciki Ammi da ke riƙe da kofi ta ɗebo ruwa ta sake shi ƙasa saboda mamaki, ta zaro idanuwanta duka waje tana kallonsa, shi ma ita yake kallo ya kasa ƙarasowa ciki sai kuma ta sauke ajiyar zuciya ta nuna shi da yatsa “Ahmaad kai ne Abdul ɗin ne ya kawo ka wai me ya sa kake son ɓata mini rai ne??” Ya yi shiru bai ce komai ba, Ya ƙaraso inda take yana ba ta haƙuri “sorry Ammi shi ne ya kawo ni”. Ta sauke ajiyar zuciya dan sai lokacin Hankalinta ya kwanta, ta nuna mishi kujera tana faɗin “shi kenan da asibitin za mu zo yanzu ya kake jin jikinka.”

Zai yi magana Wayarsa ta fara ringing ya duba sunan me kiran sai kawai ya kashe ƙara ya mayar aljihu. Kiran ya katse Still me kiran bai bari har kira uku, ya ja ƙaramin tsaki, Ammi ta ce “waye ne ka ɗaga mana” “Akarsh ne” Ta harare sa ta ce “Idan ba zaka ɗaga ba bani wayar”.

Bai iya musu ba sai kawai ya miƙa mata wayar. “Wato Doctor tsabar ba ka so na maka magana ba za ka iya picking call ɗi na ba ko? To ai shi ke nan da ma na kira ka ne na maka ya jiki. Doctor ina faɗa maka babu lokaci ka amince a yi komai kafin mu rasa damar nan, kwanaki uku kawai suka rage mana please doctor muna buƙatar rayuwarka ka kai mataki na ƙarshe fa, zaka iya rasa rayuwarka bakiɗaya. A yi magana a samu magana da Companyn da suke haɗa maganin nan ka ga kai ɗan sarki ne ko ba komai za su yi komai saboda Familynka kuma ka san suna ji da kai sosai…”

Jin tun da ya fara magana be katse shi ba ya sa shi sauke numfashi ya ce “Hello kana tare da ni?” Hawaye kawai Dr A ya gani na zuba daga fuskar Ammi ta saki wayar ta faɗi ƙasa. Sai lokacin zuciyarsa ta shiga bugawa da wani irin mugun ƙarfi ranshi ya ɓaci ya fara jin haushin kansa dan me zai ba ta wayar yanzu shi kenan ta ji komai. Jikinsa ya kai ƙololuwa wajen yin sanyi ya buɗe baki da ƙyar ya fara magana “please Ammi ki tsaya na miki bayani, ba na so a yi aikin saboda ko da an yi ba za a dace ba, kawai za mu zubar da ƙimarmu ne mu nemi alfarma wajen ma’kiyanmu kum..”

Ta daka masa wata irin fusatacciyar tsawa lokaci ɗaya idanuwanta sun yi ja ta nuna shi da yatsa hawaye na bin idanunta. “Kai Ahmaad Ashe ba ka da tunani! Me kake sha ne haka da ke ruɗa maka ƙwa-ƙwalwa wai so kake baƙin ciki ya kashe ni ne, Ni da Ƙanwarka, wai me yake damunka ne haka, anya kai ne Ahmaad ɗina me sadaukarwa gare mu??” Sai matsanancin Kuka ya ƙwace mata, ta yi ƙarfin halin ci gaba magana cikin muryar Kuka, “Yadda mahaifinka ya mutu ya bar mu, haka kai ma kake so ka mutu a banza, ka san zuciya kuwa ka san irin gaban raɗaɗin da nake ji, ka san tsawon lokacin da na daɗe ina burin haihuwar mai share mini Hawaye?? Kana wasa da abubuwa, Komai da ka ga ina yi don Farin cikinku nake yi, Ahmaad ciwon Zuciya me muni fa, zuciya! Zuciya!! kana wasa da Zuciyarka kana sakaci sosai Mahaifinka Zuci…”

Ta kasa ci gaba da magana tari ya sarƙe ta. Hankalin Ahmaad ya tashi sosai, gabaɗaya ya rasa inda zai tsoma ransa. Zuciyarsa sai ƙuna take idanuwansa sun rine saboda tsananin ɓacin rai ya kasa magana. Yai shiru ya sunkuyar da kansa ƙasa.

Ta miƙe da ƙyar ta ɗauki ruwa ta sha ta haye saman bene ta bar shi nan Zaune. Ya daɗe nan zaune da ƙyar ya iya miƙewa ya ɗauki wayarsa yana dafa bango ya isa ɗakinsa.

Numbern Abdul ya shiga kira dan ya san wajensa kawai zai iya samun mafita a wannan lokacin, ya yi masa 3miscalls amma bai ɗaga ba, ya yi wurgi da wayar cike da baƙin ciki, zuciyarsa na raya masa abubuwa da dama. Ke nan shi ma Ahmaad ya yi fushi da shi, dan ya san duk irin fushin da ya yi masa ba ya ƙin ɗaga kiransa.

Har ƙarfe goman dare bai kira sa ba ya sake kiransa bai ɗaga ba yana ƙoƙarin sake kiran ya ji wayar a kashe. Ya lumshe idanuwa kawai yana wani murmushi me ciwo.

<< Zuciya 7Zuciya 9 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×