Har dare ya ratsa sosai ba su tashi ba sai ma gaba da abun nasu ya sake yi, ganin Nafi na gyangyaɗi ne ya sa Hinde ta zame ta bar ta ita kaɗai, ta sadda kanta bisa teburin barci ya ɗauke ta.
A hankali Nafi ta fara buɗe idanuwanta da sukai mata nauyi, Cikin rashin kuzari ta miƙe zaune tana hamma saboda yunwar da ke kartar mata 'yan hanji, sai lokaci ma ta fara ƙarewa ɗakin da take kallo, ta yi Saurin dirowa daga kan gadon tana 'yan leƙe-leƙe gadon da tsarin ɗakin. . .