Skip to content
Part 9 of 15 in the Series Zuciya by Khadija Muhammad Shitu (K_Shitu)

Har dare ya ratsa sosai ba su tashi ba sai ma gaba da abun nasu ya sake yi, ganin Nafi na gyangyaɗi ne ya sa Hinde ta zame ta bar ta ita kaɗai, ta sadda kanta bisa teburin barci ya ɗauke ta.

A hankali Nafi ta fara buɗe idanuwanta da sukai mata nauyi, Cikin rashin kuzari ta miƙe zaune tana hamma saboda yunwar da ke kartar mata ‘yan hanji, sai lokaci ma ta fara ƙarewa ɗakin da take kallo, ta yi Saurin dirowa daga kan gadon tana ‘yan leƙe-leƙe gadon da tsarin ɗakin ma kwata-kwata ba nasu ba ne wanda suka saba kwanciya ba ita da Hinde, Wannan ya zarce wancan kyau fiye da misali ya haɗu An baza kayan kwalliya da na shafe-shafe kan dress mirror ɗin gwanin ban sha’awa.

Ta kalli kanta ta cikin madubin ta yi saurin zaro idanuwa waje ganin wasu fitsararrun sleeping dress a jikinta gabaɗaya babu wani abu da ya ɓuya a zubin halittarta, ta kalli ƙafafunta da suke a waje dan ɗan wandon daga gwiwa kawai ya tsaya.

Jin motsin da ta yi daga waje ya sa ta saurin komawa ta kwanta ta lulluɓe da bargo, ta yi lamo kamar tana barci. Hajiya Safeena ta shigo cikin ɗakin ita da Hinde tana mata magana “gaskiya Hinde na ji daɗi sosai daren jiya maganin nan ya yi aiki sosai, ga ragowar na barcin nan idan ta tashi zan sake ba ta, ki riƙe waɗannan kuɗin ita Hajjaju zan mata sallamarta, za mu yi waya da ita dan yarinyar nan za ta ɗan yi min ko sati biyu haka zan sake wayar da ita ni so nake ma Hajjaju ta bar mini ita, ai Rukky Kano zan tura ta kar ta ɓata min jindaɗi na, Alhaji ma kin ga Saturday ya tafi kuma zai daɗe bai dawo ba..”

Nafi na jin su ta yi tsit har suka gama surutansu suka fice. Tana ganin sun fita ta yi zumbur ta miƙe da sauri a ɗan tsorace ta fito. Daidai lokacin Hajiya Safeena ta shigo Parlourn da zai sada ta da bedroom ɗin da Nafin ke ciki, har karo suka kusa yi Nafi ta ja baya tana Hammar ƙarya Hajiya Safeena ta washe haƙora tana murmushi ta dubi Nafin ta ce “Nafeesa kin tashi ke nan, ki shiga toilet akwai brush da maclean ki kimtsa ki fito mu je mu yi breakfast”.

Ta ɗaga kai kawai ta shige cikin Toilet ɗin, cikin sauri ta yi brush ɗin ta fito saboda yunwar da ke ƙwaƙularta.

Hajiya ta miƙe tana gaba Nafi na bin ta a baya har suka fito daga ɗakin zuwa haɗaɗɗen Parlour, Nafi ta ruɗe ta sake baki sai kallon tsarin parlourn take kwata-kwata ma ba za a haɗa shi da na gidan Hajajju ba, wannan ya fi kyau nesa ba kusa ba ga wani ni’imtaccen sanyi da ƙamshi ta lumshe ido.

Sai kuma ta yi saurin buɗewa saboda tuntuɓen da ta yi da kujerar da ke dinnig area ɗin, Hajiya Safee ta juyo ta kalle ta, tana ta mata sannu ta ja mata kujerar da ke dab da tata. Suka zauna Tala ta shigo da sauri jin motsi a dinning ta ƙaraso baki har kunne tana gaida Hajiya Safee, ta dubi Nafi ta ce “Lale sannu baƙuwa ya aka kwana, bari na zuba muku abinci kar na ishe ku” ɗan murmushi kawai Nafi ta yi ba ta ce komai ba. Tala ta matso ta buɗe Kulolin da ke jere bisa teburin ta fara zuba musu farfesun ƙafar sa da Soyayyar doya marar ƙyau, sai ƙamshi ke tashi, tuni yawun Nafi ya tsinke kamar ta duma hannu ta fara kai ma bakinta ta ke ji. Allah ya yi ta da masifaffen kwaɗayin Abinci.

Ta shaƙe mata plate ta turo mata shi gabanta sannan ta zuba mata kunun gyaɗa, ita ma Hajiya Safee ta zuba mata sannan ta bar dinning ɗin bisa Umarnin Hajiyar.

Jikin Nafi har kyarma yake yi ta duma hannu duk da tururin da Naman yake yi amma ta saka hannu ko ɗar bata yi ba duk da ta ji zafi burinta kawai ta kai ma cikinta. Ganin yadda ta zage tana cin Abincim ne ya sanya Hajiya Safee yin murmushin mugunta, sai kallon ta take yi, ita kuwa Nafi ta maida hankali duk yawan Abincin ta cinye tas.

Sannan Hajiya ta ce ta wuce ɗakin da ta kwana ga shi chan Tala tana ciki, ta miƙe kamar za ta yi amai saboda cin da ta yi.

*****
Washegari Dr ya shirya yana tunanin damun kiran Abdul amma shiru, Ya shirya ya ɗauki wayarsa ya nufi Sashen Ammi. Tun da ya shiga gabansa ke faɗuwa saboda Abdul da Irfaan da Abdul da ya gani cikin Parlourn sai Ammi suna tattaunawa. Ya shiga fuskarsa a haɗe ya gaida Ammi ta amsa ba yabo ba fallasa, yana shirin Yi ma Abdul magana ya ga ya haɗe fuska ya ɗauke kansa. Ammi ta dube sa ta ce “Za ka iya tafiya” Ya miƙe ba tare da ya ce komai ba Ya fice ransa a ɓace, Ya koma ɗakinsa ya duƙufa yana amfani da system ɗinsa ko breakfast bai ba.

Ya duƙufa sosai yana aiki tuƙuru kafin ya ɗauko wani ƙaton Diarynsa ya fara rubutu ya daɗe sosai yana rubutun dan duk Acn da ke ɗakin zufa na ɗan ɗiga daga goshinsa. Yana gamawa Ya miƙe ya fito hannunsa riƙe da mukullin mota ya fito Parking lot ɗin gidan daidai lokacin su ma suka fito Irfaan ya kalle sa ya yi masa murmushi, Abdul ya kalle sa ya ɗauke kansa gefe, shi ma Dr ya ɗauke nasa kan, ya buɗe motarsa ya tada ta da mugun gudu maigadi ya buɗe masa ya bar unguwar.

Tun da ya ɗauki hanyar rugar yake jin zuciyarsa babu daɗi, tafiyar Awanni huɗu ya yi, saboda gudun da yake shararawa, Ya fara shigowa cikin Rugar saboda titin da yake marar kyau sosai me kwazazzaɓe, ga kuma Rugogin da ya fara wucewa. Wuri ya samu gefe ɗaya ya Parker Motarsa.

Tafiya ya fara a hankali cikin nutsuwar da ta zame masa jiki, ya fara shiga cikin rugar yana wuce lambuna, wani lambu me cike da ni’ima da sanyi ya zo wucewa ya ga wani tsohon Bafullatani yarinya na zuƙunne gabansa shi kuma ya kafa ƙwaryar Nono a baki yana sha, Ya sauke ajiyar Zuciya yana gode ma Allah, Ya ƙarasa inda suke yana musu Sallama. Shiru suka masa ba su amsa shi sai kallon shi da suke yi kamar za su cinye shi, Ya sake maimaita sallamar Yana matso su, Bafullatanin ya amsa masa yana dire ma yarinyar ƙwaryarta. Ko kuɗi ba ta tsaya karɓa ba ta ɗauki ƙwaryar jikinta na kyarma sai kallon tsoro take wa Dr ta kwasa da wani irin gudu sai da ta fara gudun ta buɗe murya tana ihu faɗin ‘Aljani’ shi dariya ma ta ba shi ya ɗan murmusa. Ya kalli tsoho da ke shirin barin wajen ya ce “Baba Dan Allah ɗan tsaya tambaya nake”. Ya tsaya yana ƙare masa kallo sai ya ce,“Mutum ko aljani?” Ya sake murmusawa, hakan ya sa mutumin matsawa, Dr. ya ce “Mutum!” Sai ya ɗan numfasa ya ce “ina sauraronka yi tambayarka”. Dr ya ce “Baba ina neman Nafeesa ‘yar gidan Baffa Iro”.

Mutumin ya yi bala’in tsorata ya ɗan zaro idanuwa ya ce “Nann…Nafi kake nufi??” Ya ɗaga masa kai alamar E Mutumin ya ce “Amma miye haɗinka da ita kai din nan??” Ya Dan yi shiru kafin ya ce “Ina siyan Fura gun ta ne” “To maganar gaskiya ni ba zan iya faɗa maka komai game da ita ba” ‘’Dan me?’‘ ya tambaye sa cike da ƙuluwa, Ya ba shi amsa a hankali “wataƙila tana sauraren mu yanzu haka ma, ni zan tafi” Ya Kalle sa cikin rashin fahimta ya ce “Ban gane ba” Mutumin ya yi shiru sai kuma ya ce “Ai ba mutum ba ce ita ɗin Mayya ce!” “MAYYA!!” ya faɗa zuciyarsa ta yi wani irin bugu, kafin ya samu zarafin magana mutumin ya fara tafiya dan har ya fara kutsawa cikin daji, Ya bishi cikin sassarfa yana haɗa shi da girman Allah ya tsaya yana faɗin, “dan Allah ɗan saurayi ka bar ni ba na son ka ja mini fitina.”

Ya ce “Baba dan Allah ka taimake ni, in sha Allahu babu abin da zai same ka, so na ke ka sada ni da wani makusancinta ko ka sanar da ni dangane da ita” Mutumin ya yi shiru sannan ya ce “ba zan iya faɗa maka komai ba yanzu, ka dawo gobe da safe nan, amma kai jinin Sarauta ne ko?” Ya yi Mamaki sosai Amma ya maze ya amsa masa, sai kawai mutumin ya yi murmushi yai tafiyarsa. Dr Ya koma inda motarsa take jiki a sanyaye Yana ta tunani barkatai.

“Waziri cewa na yi ina son ganawa da Abdul’aziz!” Wani irin kalllo wazirin ya yiwa gimbiyar Ya girgiza kansa ya ce “Kamar ya??” Ta ja masa tsoki wannan karon rai ɓace ta ce “so nake ka kira shi yanzu” Ya yi mata kallon banza ya ce “A matsayinki nawa??” A fusace ta nuna kanta da yatsa ta ce “Ni kake faɗawa haka Yusuf?” Bai ba ta amsa ba ya miƙe ya fice daga ɗakin.

Gimbiya Zubaida Ɗiyar sarki mai ci a yanzu ta miƙe ranta a ɓace ta fito daga ɓangarenta ita ma, ta fito, tun da ta nufo sashen UwarGida masu hidima a bayi suke ta gaishe ta, amma babu wanda ta kula, a bakin ƙofar shiga ma babu wanda ya yi mata iyaka ko ƙoƙarin yi mata iso ta shige ciki.

Uwar gida na kishingiɗe Bayi guda biyu suna mata fita da tausa sai murmushi take yi, Gimbiya Zubaida Ta shigo ɗakin fakam-fakam. Babu Sallama bare neman izini ta iso gaban uwar gida tana huci. Ganin a yadda ta shigo ne ya sanya Uwargida sallamar dukan masu mata hidima ya rage da ita sai Gimbiyar. Ta kalle ta tana jawo ta jikinta ta ce “wa ya taɓa min auta?” Ta ɓata fuska sosai cikin tsananin fushi ta ce, “Mammy Waziri ni zai..” Ta girgiza kai ta ce “Ya isa haba Auta mi ya sa ba ki jin magana ne wai, taurin kanki ne ya janyo miki, ba sai da na faɗa miki kar ki saka kanki cikin wannan wasan ba, kin ƙi bari na da su bare ki ga yadda ake buga ainahin wasan kin tsaya shirme, yanzu ki haƙuri ni zan ɗauki tsattsauran mataki a kan al’amarin tashi ki je.” “Amma Mammy..” Ta girgiza kanta “na ce ki bar komai a wajena tashi” Ta miƙe tana zumɓura baki cike da rashin tarbiyya ta nufi ƙofar fita. Sunfar da ke laɓe ta bayan ɗakin ta yi gaggawar barin inda take laɓen ta nufi ɓangaren Galadima kamar za ta kifa dan sauri.

Ya yi kusan mintuna goma cikin motar bai fito ba, kansa ne ke masa wani irin azababben ciwo, ƙofar ma a buɗe take amma ba shi da niyyar fitowa, da ƙyar ya zuro ƙafafuwansa waje yana dafa motar, Ya fara tafiya yana jin jiri na ƙoƙarin kada shi, Ya ƙwanƙwasa ƙofar Parlourn, Imaan ta leƙa ta gan shi, cikin sauri ta buɗe tana kallon shi za ta fara surutu ta ga ya dafa ta dan yana shirin faɗuwa. Ta riƙe hannunshi tana jera mashi tambayoyi, “Yaya me ke damunka, ko jikin ne ka yi tafiya a hankali??” Ammi na kallon su har Imaan ta taimaka masa ya zauna kan kujera. Ganin yadda idanuwansa suka yi ja sosai ya tsorata su, Imaan ta ci gaba da tambayar sa “Ka yi magana Please yaya what’s wrong with you?” Ya yi mata murmushi kawai. Ya kalli ammi cikin daddaɗar muryarsa ya gaishe ta, ta kalle shi tana sake haɗe fuska ta ce “Lafiya! So nake ka kira Abdulrahim ka ba shi haƙuri ya amince zai turo mana da maganinka”.

Ya ɗan waro idanuwansa sannan ya lumshe su, Jikinsa sai wata irin karkarwa yake ya zamo daga kan kujerar ya matsa gabanta, cikin nutsattsiyar muryarsa wacce take ƙunshe da tsananin Tashin hankali da damuwa ya kamo hannayenta cikin dakiya yana magana “Ammi do Allah kar ka saka ni aiwatar da abu da zai yi silar barina duniyar nan, I can’t! He’s our enemy Please try to understand what i mean!!” Yadda ya ƙarashe maganar muryarsa na rawa yanayin hausarsa kuma da ta jagule saboda tashin hankali ne ya sa jikin Ammi yin sanyi Imaan ma har ta fara hawaye. Cikin dakiya Ammi ta sake faɗin, “Umurni ne nake ba ka ba shawara ba!” Ya saisaita muryarsa Ya sake cewa “Please Ammi, ki rabu da shi.. nd he’s Very dangerous more than..” ta katse shi cikin fushi “Ya isa tashi ka fita!”

Irin tsawar da ta yi masa tana nuna masa ƙofa har cikin ƙwa-ƙwalwarsa, ya kalle ta irin kallon mamakin nan, Ya miƙe da ƙyar ya fice, bai kula kowa ba ya shige Parlournsa, kawai ya zube bisa kujera. Ya dafe kansa jikinsa sai wata irin karkarwa yake yi, ya abubuwa suke neman chaɓe masa ne haka gabaɗaya komai ya fita daga ransa abinda Ammi ke ƙoƙarin tursasasa shi ya aikata ba ta san yana iya zama ajalinsa ba, da a ce shi Ahmaad Abubakar Yusuf Lamiɗo ya kira Abdulrahim gwara a ce ya rasa rayuwarsa ya furzar da huci me zafi cikin tsananin baƙin ciki yana lumshe idanuwansa, gabaɗaya ba ya jin daɗin komai ya rasa me ke damunsa wani irin zafi yake jin zuciyarsa na masa.

Shi kam ya gama sarewa ya san ba shi da sa’a kwata-kwata a rayuwa, Amma da zarar ya tuna da cewa ba zai wani daɗe ba yana ƙunsar baƙin cikin duniya ba sai ya ɗan murmusa. Ya daɗe sosai a nan ga yunwa da yake ji ga kuma jikinsa da ya ɗau zafi sosai.

*****
Tala me aikin hajiya Safee ta kalli Nafi a karo na biyu ta sake kecewa da wata dariyar ƙeta kamar za ta shiɗe tana riƙe ciki, Ta faɗa kan gadon gudun kar ta faɗi, sai da ta yi me isarta sannan ta yi shiru tana matse ƙwalla, Nafi ta yi zuru tana kallonta hawaye duk sun bushe a kan fuskarta. “ ‘Yan’mata adon gari! Lallai Nafi kike ko? Yo idan kin san ba za ki iya wannan harkar ba tun farko uban me ya jawo ki cikin ƙungiyar, ni kin ba ni mamaki ma ina ganinki yarinya ɗanya shakaf amma ki ce rayuwar da kika zaɓa ke nan chaɓ wallahi in dai Hajiya ce sai ta more ki son ranta kafin ki samu sassauci, in kin dace ta ɗan sa an ɗan koyar da ke ilimi to alhamdulillah amma babu abin da za ki samu sai wasu kuɗaɗen banza amma darajarki za ta ragu kuma kin ɗauko hanyar kashe rayuwarki ne bakiɗaya, ni dai iyakacina da ke kallo.”

Nafi ta ruɗe sosai tana magana saboda tsananin tsoro har fullanci take mata. “Ka taimake ni, hanɗi jam`im wayyo Baffana”. Ta sake sheƙewa da dariya “Hahhhaha! Ai idan taimako kike buƙata tun farko ke za ki taimaki kanki da kanki, matsalata da ƙauyawanmu ke nan ba sa kishin kansu wasu lokutan kwaɗayin mu na jayo mana masifa mu kasa fahimta tun farko sai lokaci ya ƙure mun ga bala’in duniya.” Cikin harshen fulatanci Nafi ke faɗin Dan Allah ta kai ta gun Baffanta. Tala ta yi saurin sanya yatsanta bisa baki tana faɗin Ssh! jin kamar motsi a Parlour. Ta yi shiru tana sauke numfashi. Gabaɗaya wani irin mugun tsoro ya gama kama ta. A halin yanzun babu abinda ta fi muradi irin ta buɗe ido ta gan ta gaban Baffanta, tsoron Hajiya Safee take bala’in ji kamar mutuwarta tun da ta fara ganin alamomin iskacinta sun bayyana.

Nafi na sake tunanowa a yanayin da ta ga Hajiya Safeen lokacin da ta shiga wani ɗaki ba tare da sanin ta ba maimakon nasu, kuma da yunƙurin da ta yi na aikata mata wani abu sai ta sake ruɗewa, ga tun da ta tashi daman take jin wata irin faɗuwar gaba da rashin jin daɗi. Hajiya Safee ce ta ƙwala wa Tala kira, ta miƙe da sauri ta fice. Sai ga ta tadawo Hannunta riƙe da Kofi. Ta dubi Nafi ta ce “Amshi ki sha in ji Hajiya” Ta yi mugun tsorata ta kasa amsa, sai kawai ta rushe da kuka, Tala ta zauna a wannan karon tana ɗan jin tausayin Nafin. Ta ajiye kofin ta fara magana, “Kin san me ne a ciki?” Nafi ta girgiza kai da sauri, “Ƙwaya ce me ruɗarwa da saka barci ake ba ki don a ji daɗin amfani da ke cikin sauƙi” Ta tsaya tana kallon ta cikin rashin fahimta ba ta ce komai ba. “Hmm!. Gaskiya da alama har yanzu ƙuruciya na ɗawainiya da ke sosai ɗin nan! Kin ba ni tausayi gaskiya ba zan so rayuwarki da ke kanki ki lalace ba, ki ji ni da kyau; idan har Hajiya ta sake ba ki wani abinci kar ki ci, ki yi yadda kika yi kika san ba ki ci ba, ba tare da ta gano nufinki na ƙin cin abinda ta bakin ba.” Cikin sauri Nafi ta jinjina kanta, sannan Tala ta ci gaba da magana ta ce, “Ki yi ƙoƙari ki jure idan har na bar ɗakin nan ki kwanta ki yi kamar kina barci ko ni da Hajiya mu ka dawo kar ki kuskura ki nuna idonki biyu, duk wani abu da za ki ji ta miki ki daure idan ba haka hmm… Ki bari sai ta fara fita hayyacinta ki fara wani abu me kama da ba kya cikin hayyacinki kina abubuwa kamar kina cikin mawuyacin hali kin ji ko idan kika yi haka za ki kuɓuta daga sharrinta.” Ta sauke ajiyar zuciya ta ce “Umh na ji” Tana gani Tala ta zubdo Zoɓon da ta shigo da shi a kewaye ta dawo, kusan mintuna biyar ta ce ma Nafi ta yi yadda ta sanya ta.

Ta gyara kwanciyarta ta rufe idanuwa ta yi kamar tana barci. Tala ta fita ta bar ta ta koma Parlourn. Inda Hajiya Safee take ta je ta ce “Hajiya ta gama sha za ki yi iya shiga inda take”. Ta saki murmushi tana mata godiya ta sallame ta, ta koma ɗakinta da ke kusa da na Nafin wanda ɗaki ɗaya ya raba su, ta shige bedroom ɗinta ta kwanta, tana wasu Saƙe-saƙe cikin ranta game da Nafin. Cikin jin daɗi Hajiya Safee ta shiga ɗakin da Nafin take ta kulle ƙofa ta kashe fitila, duk Nafi na jin ta tayi lamo, ta tuɓe ta nufo gadon inda Nafi take, Ta fara mata wasu abubuwa da suke barazanar tarwatsa mata kwanya tun tana jurewa har ta fara ɗan motsi sosai, Tun da ta riƙe hannun Hajiya Safee jikinta na kyarma ba ta sake sanin a wace duniyar take ba.

Bubbuga filon da take kwance Tala ke yi a hankali tana kiran sunanta a hankali, da ƙyar ta fara buɗe idanuwanta da suka yi nauyi, Tala ta jijjiga ta, ta ɗan waro idanuwa a kasalance, tana kallon ta idanuwanta na ƙoƙarin lumshewa, Tala ta watsa mata ruwa masu sanyi, kawai ta fara numfarfashi tana sakin ajiyar zuciya. “Ke! ki tashi mana” sai time ɗin ta ɗan wartsake kaɗan, ta dube ta har lokacin dai mugun barci da kasalar da ke jikinta ba su bar ta ba, ta sake faɗin “Ai kun ɓata komai kin ji daɗi, kin kuma janyo ma kanki matsala tun da har ta fahimci kin san da abin da take aikata miki”.

Zumbur ta yi ta zauna tana zare idanuwanta a tsorace. “sai dai wani lokacin ko kina samun damar kuɓuta amma ba yanzu ba, maza ki tashi ki kimtsa safiya ta yi ki ci Abinci”. Ta yi fiƙi-fiƙi da idanuwa tana kallon ta, ta kasa ko motsawa dan kasala take ji sosai. Hakan ya sa Talar kamo ta ta miƙe, ganin babu kaya a jikinta ne ya sanya ta Ɗauko mata tawul ta ɗaura, suka shiga Banɗakin ta nuna mata komai sannan ta ce ta yi brush ta ajiye mata tooth paste ta fita. Ba ta wani jima ba sosai ba ta fito saboda jiƙa-jiƙa ta yi gabaɗaya hankalinta ba ya tare da ita yana chan wani wajen daban ta ma rasa me ke mata daɗi. Haka ta shirya suka Nufi Dinning ɗin. Tun kafin ta ƙaraso Hajiya Safee ke feshe ta da wani Makirin murmushi me tsoratarwa har suka zauna Tala ta zuba mata abinci, amma sam ta gaza sakewa ta ci sai motsa abincin take yi, komai ma tsoro yake ba ta..

*****
Tukwici me faranta rai Galadima ya bawa Baiwar da ta sanar da shi zancen su Abdul da Ahmaad. Tana fita ta miƙe cikin jin daɗi ya nufi Turakar Ummi, yana shigowa ta sallami bayinta su duka da waɗanda ke hidima ɓangarenta. Yadda ta ga yana fara’a ta san ba banza ba, Ya fara mata magana ya ce, “Albishir me daɗi…Aikinki ya yi ɗari bisa ɗari ko ma na ce fiye da haka! Don Wannan abin wasan ya suɓuce musu” cikin farin ciki ta miƙe zaune tana murmushi dan ta gama fahimtar inda ya dosa. Sai da ta juya idanuwanta sannan ta ce “Hmm..Kana wasa da Malika ke nan”. Ya zaro idanuwansa ya ce ‘‘Kai! Wane ni ai na karaya da al’amarinki ke ɗin gaskiya kin fita zakka fa tabbas!’’ Sun daɗe suna Ƙulle-ƙullen abubuwa tsakaninsu suna murna. Daga ƙarshe ya miƙe ya fita dan yana son samun bayani daga wajen Akarsh likitan Dr. Tana ganin ya fita ta ja tsoki tana hararar ƙofa ta kuma tuntsure da dariya a fili ta ce “Soko kawai”.


Waziri Mahaifin Abdul ya sake tsattsare sa da idanuwa ya fesar da numfashi ya ce, “Ka tabbata babu wata matsala tsakaninka da Ahmaad??” Ya jinjina kai ya ce “Eh Abba na tabbata.” Ya sauke ajiyar zuciya ya sake faɗin, “Dan Allah Abdul’aziz kar ka bari wasu su shiga tsakaninku cikin ƙanƙanin lokaci don naga abinda ake son aikatawa ke nan. Tashi ka tafi Allah ya tsare ku.” Da ‘Amin’ ya amsa ya fice daga Sashen. Haka nan yanzu yake jin ɓacin rai ko sunan Ahmaad aka kira, shi kanshi bai san dalilin da ya sa yake jin haushinshi ba sosai.

<< Zuciya 8Zuciya 10 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×