Yanayin garin ne yayi tsit kasancewar daukewar motsin mutane. Ba wani sauti da kake ji face sautin kukan tsuntsaye, da wasu halittu da ke neman abincinsu a cikin dare.
A dai dai wannan lokacin ne, ta rika jin saukar hannayensa, suna yawo a sassan jikinta.
Wani abu ta riƙa ji yana taso mata tun daga ƙasan zuciyarta har zuwa illahirin gangar jikinta.
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!. " Ta furta can a ƙasan maƙoshinta.
Wasu irin hawaye suka riƙa zirarowa daga idanuwanta masu tsananin zafi da ƙuna.
Wani sautin marayan kuka ne ya kufce. . .
Ma Sha Allah