Skip to content
Part 1 of 1 in the Series Zuciya Da Hawaye by Aisha Faruk

Yanayin garin ne yayi tsit kasancewar daukewar motsin mutane. Ba wani sauti da kake ji face sautin kukan  tsuntsaye, da wasu halittu da ke neman abincinsu a cikin dare.

A dai dai wannan lokacin ne, ta rika jin saukar hannayensa, suna yawo a sassan jikinta.

Wani abu ta riƙa ji yana taso mata tun daga ƙasan zuciyarta har zuwa illahirin gangar jikinta.

“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un!. ” Ta furta can a ƙasan maƙoshinta.

Wasu irin hawaye  suka riƙa zirarowa daga idanuwanta masu tsananin zafi da ƙuna. 

Wani sautin marayan kuka ne ya kufce a bakinta mai tsananin bada wahala a ƙasan zuciya.

Ta ɗauka ta yi bankwana da wannan mummunar baƙar ƙaddara, tun wani lokaci da ya shuɗe, a lokutta mafi muni na rayuwarta.  Ashe tana nan ba ta tafi ba. Tana nan biye da ita har sai ta fidda tsiro mafi muni a duniyarta.

Sosai take ƙoƙarin ganin bai cimma ƙazamin burinsa a kanta ba. Sai dai ta fahimce wahala kawai take baiwa kanta, dan kuwa ko gizau bai yi ba sai ma ƙara ɗora mata dukkanin nauyinsa da ya yi a kanta, yana mai yi mata magana mai cike da gargaɗi a hankali a cikin kunne.

“Idan kika bari kukan nan ya fito wani ya ji, I will kill you.” Ya faɗa cikin sautinsa da ke fitar da wani irin wari na giyar da ta zame masa wata ɗabi’a maigirma tun kafin wanzuwarta duniya.

Dafe bakinta ta yi, da dukkanin hannayenta, tana mai jin wani irin zafi da raɗaɗi a duk inda hannayensa suka sauka a jikinta.

Tana cikin haka ne taji lokacin da ya zare marufin da mata ke rufe mutuncinsu da shi ya yi wurgi da shi a tsakar ɗakin. Tun lokacin kuma zance ya canja, abun da ke faruwa da ita a duk lokacin da wani ya yi niyar aikata wani abu makamancin wannan yau ma shi ya faru da ita, dan kuwa tuni ta manta  saman duniyar da take rayuwa a kai…….!

Wani irin zufa mai yawa yake sharcewa a ko wace kusurwa ta jikinsa. Tun tana ‘yar ƙanƙanuwar ta yake ɗauke da buri a kanta, yake so ya biya buƙatarsa gareta dan cimma wata manufa ta shi guda ɗaya da yake rayuwa domin ta a doron ƙasar nan.
Amma ko da yaushe ya yi yunƙurin cimma burinsa a kanta komai sai ya taɓarɓare masa.

Shin hala bata san ta hanyarta kaɗai ce dukkanin burikansa za su cika ba? Shin hala bata san ita kaɗai ce shamaki ga dukkanin buƙatunsa ba? Har sai yaushe ne zai cika burinsa? Har sai yaushe ne zai samu biyan buƙatarsa? Shin har sai yaushe ne dukkanin mafalkansa za su zamo gaskiya?

Kallonta ya yi a karo na farko da ya kunna wutar ɗakin.

“Me ke tare dake ne da ke min katanga da buƙatuna Rumana?, Me ke tare dake ne?.” Ya faɗa yana mai kafeta da manyan idanuwansa da suka zamo sak irin nata. Kasancewar ita ɗin kanta daga garesa aka sameta.

Tsaki ya ja, tare da shafa sumar kansa cikin wani yanayi na jin haushin kansa da kuɗaɗensa da aka cinye a banza ba tare da buƙatarsa ta biya ba. Dole ne ya koma wurin mutuminsa na farko. Dole ne ya koma dan ya samo masa wata mafita, saboda lokacinsa yana tafiya ba tare da ya aiwatar da komai na daga ƙudurinsa ba.

Miƙewa ya yi tare da kinkimar ta, ya nufe ɗakinsu da ita in da Hajja ke kwance.

A hankali ya tura ƙofar ɗakin ya shiga ba tare da ya kunna wutar ɗakin ba. Direct makwancinta ya nufa da ita ya ajeye ta. Kafin ya juya ya kalle gefen da Mahaifiyar tasa ke kwance tana sakin munsharin da sam bai yi kama da na jin daɗin bacci ba.

Yar fitilar wayarsa ya kunna ya haskata da ita. Tana nan kwance kamar yanda ya barta ko motsawa bata yi ba. Murmushi ya yi wanda iyakarsa fatar baki kafin ya kashe fitilarsa ya rufo musu ɗakin ya fito………!!!

*****

A razane ya miƙe daga nannauyan baccin da yake yi, saboda mafalkin da ya yi, idan bai manta ba, wannan ne karo na biyu  yana mafalki da shi tare da yarinyar. Zufar da ta tsatsafo masa a goshi ya shafe tare da kai dubansa kan Hajiya Falmata da ke ta sharar baccinta hankali kwance zuciya zaune. Wani irin haushinta yaji ya cika masa ciki tamkar ya shaƙeta ya kaita lahira, sai dai ko yatsa ba zai iya nuna mata da sunan abunda ta aikata a garesa ba.

Wayarsa ya lalubo ya danna masa kira da lambobinsa. Tunda yana da tabbacin ƙasar da yake safiya ta riga ta waye. Sai dai har wayar ta ƙarashe ringing ɗin ta ba a ɗaga ba. Dama ya san ba ɗauka zai yi ba, karambani ne kawai irin na zuciyarsa da ba zata iya haƙura ba har sai ta kirasa ko da ba zai dauka ba.  Amma ya zai yi da jarabawar Ubangiji tunda shi ne  ya jarabce sa da ƙaunar sa mai yawa a cikin zuciyarsa.

Ajiyar zuciya ya sauke yana tuna irin ɗimbin kuskuren da ya tafka a rayuwarsa. Kuskuren da sosai ya bada gudummuwa mai yawa wurin taɓarɓarewar tarbiyyar Jabeer.

Sai dai yanzu sosai yake so ya ga ya tallafe sa, so yake ya ga ya zama normal irin ko wane yaro da al’umma za su yi alfahari da shi.
Amma ta ina zai fara?

  Mafalkin da yayi ne ya faɗo masa a rai. Sai dai ko alama bai gane wani abu da  mafalkin nasa ke nufi ba. Ya yi  tunani da nazari game dashi amma babu wani abu ko kwara daya da kwakwalwarsa ta fahimta. 

“Alhaji ince dai ko lfy kake falke har yanzu”Hajja Falmat  ta tambayesa tana mai miƙewa zaune tana kallonsa.

Sai da ya haɗiye wani abu da ya tokare masa maƙoshi kafin ya iya bata amsa da.

“Lafiya ƙalau, kaina ne ke ciyo.” Bai faɗi ƙarya ba dan kuwa kansan ne ke masa ciyo tun lokacin da ya farka daga baccinsa.

“”Subhanallah, da fatar dai ba hawan jinin naka ba ne ya tashi ?” Ta faɗa cikin wata irin kulawar da ke nuna tsantsar ƙauna ga wanda ake yi ma ita.

“Bana tunanin shi ne Falamta. Ɓallo min dai magani in sha sai in sake  kwantawa, nasan idan na samu isasshen barci kafin safe zai daina, ina ganin stress ne kawai ya min yawa.

Bata yi masa musu ba, duk da tana da tabbacin ba hakanan ne ba, ta dai tashi ne kawai ta ɗauko masa magani tare da ruwa ta bashi ya sha.

Cikin ƙanƙanen lokaci  bacci ya kwashesa saboda maganin yana saka bacci, sai dai baccin da ya samu cike yake da al’amura masu ban mamaki a cikinsa…..

Kano

Wani irin birk  ta taka da karfi har sai da kanta ya duke sitarin motar.

“Oh my God. Zully kashemu zaki yi ne tun  ban aure Ya Saif ba.”

“You can never understand Sumayya, zuciyata tana min zafi sosai idan naga mahaifiyata cikin kunci. me yasa ko yaushe Daddy ke gallazawa soyayyarta garesa? Wani lokaci ina ji tamkar in ka…….!! kalamanta suka katse sanadiyar Hannayen Sumayya da suka sauka a bakinta.

“Don’t say it  Zully, he is your father for haven sake”

“So what dan yana mahaifina. dan yana mahaifina sai ya kuntatawa mahaifiyata. a kan wane dalili. ba zan lamunta ba wallahi”

“Ni fah gani nake kawai Wannan makirar matar ce ta gidanku ta asirce shi, kin san sharrin kishiya yawa ne da shi.”

wata kwafa Zualihat ta yi, ta sake jan motar da gudu ta bar unguwar tana jin zuciyarta kamar zata fito tsabar bakin cikin da take ji dan gane da zaman mahaifinta da mahifiyarta.

1 thought on “Zuciya Da Hawaye 1”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×