Skip to content
Part 56 of 64 in the Series Mutum Da Kaddararsa by Maryam Ibrahim Litee

Mun yi nisa na ji muryarsa a saman kaina.

“Ban hana ki mu’amala da wannan matar ba? Na ce “Ka hana. Kai kawai ya girgiza duk kuma ce mishin da nake anan muka haɗu bai ce min komai ba har muka je gida.

Fushin kwana ɗaya ya yi ya sauko ranar ni zan yi girki ina gamawa kuma na shiga daki don shiryawa, na fito daidai shigowar ogan muka isa wurin shi a tare ya canza kaya muka fito.

Na zuba mishi abinci har ya fara ci Aunty Farha ta fito ta ja kujera ta zauna tana mishi maganar tafiyar ta biki Zaria.

Ban zauna cin ba kitchen na wuce don ɗauko lemon abarba da kwakwa da na yi , Hajjo na ciki har lokacin tana goge-goge ta yi min sannu na ɗauka na fita, Aunty Farha da na hango tun kafin in karasa ta zuba abincin ba ci take ba ta rafsa tagumi kawai sai na ji gaba na ya buga na karasa sai ta fara yamutsa abincin “Mene ne a cikin abincin nan Nana.” Na tsinkayi muryarta.

Cikin nutsuwa na leka abincin da take haskawa da wayarta gabana ya doka da karfi! Don abin da idona ya gano min daga kallo guda ba sai an gaya maka ba magani ne.

“Ban san ko mene ne ba.

Na fadi bakina na dan rawa. “Ban sa komai ba.
Na ƙara fadi miƙewa ta yi
“Ni ba zan yarda da irin wadannan abubuwan ba na magani, ki daina ko ma wa ya gwada miki hakan Nana. Ko kafin ki tafi da na ga kina zuba wani abu a kitchen shiru dai na yi miki amma ki bar wannan abin.”

Na dube ta cike da mamaki ina nuna kaina “Ni kika gani ina zuba wani abu?”

Ba ta ce komai ba sai miƙewa da ta yi ta shiga kitchen ina nan tsaye kamar an dasa ni ƙafafuwana sai rawa suke ta dawo ga ƙarin mamakina Sachet na garin habbatus sauda da na yi amfani da shi na rage na bar shi a falona ne a hannunta.

Kuma rabon a yi muna dawowa Kaduna har na ɓoye na ce zan bar su har sai Allah ya sa na sauka lafiya sai in yi amfani da su sai kuma kawai na ce bari in sha ko sau daya ne shi ne na dauko garin habban.

Na yi saurin ƙara kai idona kan ledar ko zan ga yar takardar da ke manne wadda ke bayanin suna da amfanin shi kaico! An cire ta ba ni da mafita na dubi ya Safwan idona na cika da hawaye na ce “Wannan sharri ne da aka shirya shi a yi min d… Ta katse ni da sauri tana faɗin.

“Ni zan miki sharri Nana? Ke ba ki kai in yi miki sharri ba, na dai gaya miki ne ba na son irin waɗannan abubuwan, kuma ki rantse wannan abin ba naki ba ne?

Cikin hasala na ce “Nawa ne Aunty Farha, kuma na kai daga ga shi kin yi min kuma Allah z…”

Tsawa ya Safwan ya yi min na ajiye jug ɗin hannuna na wuce daki.

Gado na haye na yi ta zubar da hawaye zuciyata na zafi, a duk ƙalubalen da na fuskanta a rayuwata ban taɓa haɗuwa da na kishiya ba yaushe Aunty Farha ta shigo min har ta dauka ban sani ba in an bar ni zan iya rantsuwar ko kofata ba ta kallo Hajjo kawai nasan ta kan shigo wasu lokutan in tana son yi min magana.

Yanzu dai na tabbatar da zargin da na kasa ƙarfafawa akan Aunty Farha ita ce ta ɗauki hotona da Haj Asiya.

Har gari ya waye ya Safwan bai shigo ba hakan ya sa na tabbatar ya yarda da tuggun da Aunty Farha ta shirya min.

Na shirya don tafiya makaranta saboda yau za mu fara Exam wadda za mu tafi hutun sabuwar Shekara da na Christmas. Kamar yadda ya faru a baya da yana fushi da ni bai saurare ni ba yau ma sai na fita kurum ban ko tsaya neman abin karyawa ba ballantana in yi har shi.

Sai dai abin da ya ba mamaki ina fita get bayan na amsa gaisuwar Isya mai gadi na ji ana buɗe get, ban tsaya ba ko waiwayawa ba har sai da na ji mota a gaba na na kalle ta ta wutsiyar ido ya Safwan ne a ciki, kamar in share shi in yi tafiya ta sai kuma wani tunanin ya shige ni yin banza da shi ba shi ne mafita a gare ni ba.

Na ɓalle murfin na shiga ban gaishe shi ba har ya hau titi “Meye kika sanya a cikin abincin? Ya jeho min tambayar da na ji kamar in yi ta zunduma ihu.

“Ban sa komai ba, Allah kuma shi ne shaida ta.”

Na yi ɗan shiru, jin kuma ba shi da niyyar magana na ƙara da cewa “Ka karbi ledar maganin a hannunta ka ziyarci Islamic Chemist su suke saidawa ka tambaye su mene ne meye kuma amfaninsa.”

Me zan sanya ma wani a abinci me zan nema wanda ba zan nema wurin Allah ba da ya ce ku roƙe ni zan amsa muku?

Daga haka na yi shiru har kuma muka kai ba wanda ya kara ko tari illa da ya sauke ni ya ba ni kudi, komai kuma kasa ci na yi don ban cikin yanayin da zan ji yunwa.

Abin da ke cikina sai wutsilniya yake kirjina kuma na suya.

Mun fito mu uku na ji shigowar sako, abin da tun tarewa ta ya Safwan bai taɓa mun ba ya min yau. Cewa ya yi idan na tashi in wuce. Na dubi uban cikin da ke gaba na sai na fara kiran lambar Hafsah cikin sa’a ta daga na ce ta gama? Ta ce in ba ta 10mnt.

Sallama na yi ma wadanda muke tare na kama hanyar Department ɗin su, zama na yi na jira ta har ta fito sai muka tafi tare a motarta.

A hanya ta tambaye ni lafiya nake ? Na ce me ta gani? Ta ce ta ga na yi zuru-zuru.
Na ce ƙalau nake.

A bakin get ta sauke ni gabaɗaya na ji raina ya ɓaci tuna zan shiga in ga Aunty Farha matar da na gane sharri take nema na da shi, shi ya sa ta zo ta miƙe ƙafa, ba ta ko tuna za ta tafi.

Ina shiga falon bakina ɗauke da guntuwar sallama na hango ta zaune tana ganina ta fara wata fara’a da har ta fi ta kullum, “Nana an dawo kun sha rana?

Ni ban yi ko murmushi ba na ce “Na dawo.
Na shiga falona na samu kujera na zauna ina ƙullawa da kwancewa kan zaman Aunty Farha da na gane ba alheri ya kawo ta ba niyyarta ta kashe min aure, ko ta gurgunta yardar da ya Safwan ya yi min.

Idan ya dawo zan gaya mishi Aunty Farha ta koma gidanta ko ni in bar mata gidan idan ba za ta tafi ba.

Sai kuma na dubi cikina haihuwa ko yau ko gobe ina zan tafi da shi?

Amma dole in nemi yadda zan wanke kaina daga ɓata zamantakewa ta da mijina da take son yi.

Take Mami ta fado min sai kuma wata zuciyar ta kwaɓe ni da kul! Zancen fa sanya magani a abinci ake yi, duk son da Mami take miki in giyar wake kike sha ba za ki kusanto da wanda take wa tilon ɗanta ba. In ranta ya ba ta za ki yi abin da za ki mallaki ɗanta ne domin dai sheɗan ba rago ba ne.

Nutsa na yi duniyar tunani har na samo ma kaina mafita in yi hakuri in ta addu’a har wannan turka-turkan ta wanye alabashi in yi fatan in sauka lafiya da na ji garau Aunty Farha za ta ga tsiya, dama kara nake mata daga ba ta sani ba da ƙafarta ko ba a gama gyaran ba za ta bar gidan.

Daga haka alwala na tashi na ɗauro na yi sallar a falon, har zan shiga in kwanta cikina da ke ta motsi ba ƙaƙƙautawa na gane kwanciyar ba za ta yiwun min ba, ga shi ban son fita don ko ganin Aunty Farha ban san yi.

Ina fita kuwa wannan fara’ar ta fara min “Ga shi kin dawo Nana ba mu yi abinci ba.”
Na ce “Ba komai Aunty Farha.

Na wuce kitchen ina tuna wata mata da muka zauna da ita a Gombe tana yawan faɗin ka kiyayi mutumin da ya cika maka fara’a.
Ruwan zafi na tafasa na zuba wani a flacks na hada Tea zan fara sha Hajjo ta shigo “Haj ba abin da za a yi miki ?

Kai kawai na daga mata, ganin yadda fuskata take a cinkushe duk da alamun ta akwai tsegumi me yawa da take son yi sai ta juya sum-sum na harari bayanta.

Na ci gaba da kurɓar Tea na shanye tsaf na fita kitchen ɗin dauke da flacks na shige ɗakina, ban kara fitowa ba dama girkin aunty Farha ne, ya Safwan bai leƙo ni ba yau ma har gari ya waye.

Kamar jiya yau ma tare ni ya yi ya kai ni Sch.
Da muka tashi gidan Mami na wuce, ina zama kuma saƙon shi ya shigo idan mun tashi in wuce gida shi ya wuce Ibadan.

Na haɗiye wani abu mai ɗaci na miƙe zuwa ɗakina na da da yanzu ya zama na Sakina.
A bathroom na yi kukana mai isa ta na yi alwala na yi sallah na roƙi Allah ya ba ni mafita.

Kamar in yi banza da shi sai kuma na yi mishi Text na addu’ar Allah ya kiyaye hanya, ko tambayar yaushe zai dawo ban yi ba.

Mami na ganin yamma ta yi ta ce “Ki tashi Gamandi ya mayar da ke gida kar magrib ta yi.”

Na ce “Kwana zan yi Mami.
Ta ce “Kwana kuma don Sadauki bai nan? Kuma ya yarda? Na ce “Kar ki faɗa mishi Mami.”

Ta ce “Shi kenan.”

Mafari na yi zama na gidan Mami na kuma samu sauƙin damuwa, na kashe wayoyina gabaɗaya na ajiye su.

Ina jin su koyaushe suna waya da Mami ko Daddy,Mami kuma ba ta taɓa ce mishi ina nan ba.

Ranar da ya ce mata zai dawo ranar kwana biyar, na fito zan tafi makaranta ranar kuma za mu yi takardar karshe.

Mami ta dube ni cikin tausayawa “Daga can za ki wuce gidanki ki taryi mijinki ko?

Na girgiza kai “Ba ni zan tare shi ba Mami aunty Farha ce, idan ya zo sai mu tafi tare.”

Ba dan ta ji daɗin yadda na ce ba ta ƙyale ni na wuce ɓacin raina na dawo min sabo don gani nake don kar ya ci abincina ya sa ya tsiri tafiya.

Karfe daya muka fito na kuma samu direban Mami na jirana muka tafi ina cin abinci daki na yi shigewa ta na kwanta barci mai nauyi kuma ya ɗauke ni.

Farha bayan ƙare wayarsu da Safwan ya tabbatar mata zai dawo a ranar. Wani irin daɗi ya ziyarce ta tuna har yau Bilkisu ba ta dawo ba da yadda ta ƙara kwantar da kai da ta yi ranar da abin ya faru ta yi ta kara cusa mishi illar abin da Bilkisu ke yi.

Wani farin ciki ke dawainiya da ita a haka ta yi wanka ta sheka kwalliya ta fita

Ganin Hajjo a kitchen ta zaburo ta kawo gaisuwa, kamar ta sanya ta aiki sai kuma ta ja tsaki ita indai fannin girki ne ba abin da ta iya, ko ita da ta tashi inda ba girkin take ba ta yi aure nan ma sai dai a yi mata amma na ta ya fi na Hajjo ɗanɗano sau dubu.

Tsaki mai ƙarfi ta kuma ja ta fara dafa ruwan zafi ta soya ƙwai ta fita tana gama ci ta koma daki ta kara gyara kwalliyarta sai ta fito ganinta da mayafi da jaka Hajjo ta gane fita za ta yi.

Ta dan bi ta a baya “Ranki ya dade. Ta fadi tana dan sunkuyawa Farha ta waiwayo “Dama na ce watan ya kare.

Wani banzan kallo ta watsa mata “Wata ya kare me za a yi?

“Dama kudin nake so ina so in yi aike gida.”
Kallon da ya fi na ɗazu ta maka mata “Ku wai mutanen ƙauye me ya sa ba ku da tunani, ba ku san komai ba sai kudi.”

Ta kara jan tsaki ta yi ficewar ta.

Hajjo ta mike daga sunkuyon da ta yi tana jijjiga kai

“Lallai ma matar nan ta isa butulu, don ta samu biyan buƙata shi ne za ta hana ni hakkina in kuma zama abin wulaƙantawarta? Ta yi ƙwafa ta ɗaga ƙafa da niyyar tafiya wurin Isya ko ta samu ya rage mata takaicin da wannan ja’irar mai ƙafa uwa burugali ta ƙunsa mata. Sai kuma ta tsaya cak tuna alkawarin da ta yi mishi ta ba shi dubu goman, in ta je babu kuma ba zai saurare ta ba.
Ɗakinta ta koma ta shiga ta kwanta lamo cikin matsanancin takaicin abin da Farha ta yi mata.

Farha kuwa gidan su ta tafi ta shiga cikin yaran Auntynta suka yi ta sharholiyar su sai dai masu aiki su kawo wannan su dauke wannan, nan ta shashance har la’asar saurin duban agogo ta yi tuna yau Safwan zai dawo koma ya dawon oho.

Ta dauki dan mayafinta ta rataya jakarta ta ce musu ta tafi gida.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Mutum Da Kaddararsa 55Mutum Da Kaddararsa 57 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×