Sai da ya gama zantukansa na ce "Ka shirya aurena Hassan? Ya dube ni da idanuwansa da suka canza don damuwa ya ce "E" Na ce "To ka je ka zo da abin da Allah ya hore maka ka aiko gidanmu, ba komai nake gudu ba a aure ni a sake ni." Sai na fara mishi kuka. Rarrashina ya shiga yi da alƙawura na irin ruƙon da zai min matuƙar ya dace da samu na.
Muka yi sallama na koma ciki sai dai na kasa faɗi ma Gwoggo shawarar da na yanke ta har sai da. . .