Skip to content
Part 47 of 67 in the Series Aminaina Ko Ita? by Rasheedat Usman

Cike da fara’a ya shigo cikin gidan nasu, Momy ya samu zaune ita da Aknam suna kallo cikin falon gefenta ya zauna yana murmushi.

“Barka da shigowa ya Abbas, tun ɗazu Aunty safiya take jiranka baka shigo ba.”

“Oh kinsan na manta da tazo gidan nan yau eh lallai nayi laifi, ba damuwa gobe insha Allah zanje gidan nata.”

Ya ƙarisa Maganar yana kallon Momy da hankalinta ke kan tv tana jinsu bata tanka musu ba, murmushi Abbas yayi tare da kwantar da kansa a kafaɗarta yace.

“Momyna wai yau laifi nayi ne kam aka shareni ni.?”

Sai yanzu ta dubesa tana yamutsa fuska kafin ta fara magana cikin alamun faɗa.

“Abbas kwana biyu da suka wuce wacce yarinya ka ijiye a gidanka na osokoro ta kwana?”

Murmushi ya saki dama ya sani dole akwai wanda ke saka masa ido cikin ma’aikatan gidan.

“Momy shine yasa kike fushi saboda kawai ance miki mace ta kwana a gidana, amma fa karki manta kullum a gida nake kwana wai meyasa kike tuhuma tace Momy kamar wani ƙaramin yaro just 34 fa ina da hankali da kuma Right ɗin kaina, Tabbas ta kwana a gidana ne saboda taimakon rayuwarta nayi binta ake za’a kasheta shiyasa ni kuma na taimaketa.”

Turesa daga kafaɗarta Momy tayi tare da gyara zamanta tana riƙo hanunsa cike da damuwa da kuma ƙauna irin ta ɗa da uwa Momy tace.

“Har yanzu yaro nake kallonka Abbas dole na kula da shige da ficenka, domin gudun jawowa rayuwarka matsala, kaine kaɗai ɗan da muke dashi a duniya kula da kai wajibi ne a garemu mahaifinka yana taka tsantsan da abinda zai jawo masa magana saboda shi ɗan siyasa ne jagoran al’umma, ɗan abu ƙalilan zai iya tarwatsa masa gobensa shiyasa nake kula da kai.

“Momy nifa ba karamin yaro bane da za’ace za’a kula da rayuwata sai dai ni na kula da rayuwar wani, da hankali na babu ta yadda zan jawowa Abba abin magana, ni gaskiya na fara gajiya da wannan rayuwar kawai a daina sawa ana bibiyar lamurana.”

Yayi maganar a fusace yana tashi tare da barin wajen ya fice yana nufar sashin sa wanda yake mallakinsa a cikin gidan Momy kanta ta girgiza cike da damuwa ta tsani rayuwar yahudawa da Abbas yake yi tafi son taga yana rayuwa na ƴaƴan Hausa Fulani sai dai ina mahaifinsa ya lalatasa da rayuwar turawa acan yayi rayuwarsa tun yana ɗan shekara takwas bai dawo gida ba sai da yayi digree ɗinsa har PhD, kafin ya dawo da rayuwa Nigeria, shiyasa komai nasa yake a murɗe ɗabiarsa sam batayi kama data Hausawa ba, Aknam ce tace.

“Momy nasan bakya jin daɗin tsawa da Ya Abbas yake miki, kiyi hkr insha Allah wata rana zai sauya, Momy meyasa kika saka a dinga lura da abubuwan da yake aikatawa sai kace baki yarda da tarbiyyar sa ba, Momy dole bazaiji daɗi ba ana bibiyar sa kamar wani marar gaskiya.”

Hmmm! Aknam kenan bazaki fahimta ba, Rayuwar da Abbas yayi a Turkish rayuwace tasu sam bashi da ɗabiar ƙasar mu, sannan bada tarbiyya ta ya tashi ba, shiyasa nake saka masa idanu domin kuwa zai iya aikata abinda zai lalata goben mahaifinsa.”

“Momy wannan ba hujja bace tunda bakiga yayi wani abu marar kyau ba tun dawowarsa dan Allah Momy ki rage yawan takurawa Ya Abbas please.”

Miƙewa Momy tayi tare da cewa.

“Ke yarinya ce bazaki hango abinda nake ƙoƙarin hangowa ba dan haka kibar wannan maganar.”

“Amma Momy…”

“Ya isa Aknam kije ki ƙarasa aikin dana saki.”

Ta dakatar da ita tana haurawa sama.

Shi kuwa Abbas a fusace ya shiga part ɗin nasa tare da zama kan tsaleliyar kujerar dake falon kansa ya dafe, zuwa yanzu ya fara gajiya da abinda Momy take masa, ta takurawa rayuwarsa bashi da sukuni, ko ta ina tasa an sanya masa idanu kamar wani ɓarawo, wallahi da yasan shegen dake zuwa ya kawo maganarsa wajen Momy wallahi da sai ya masa wulaƙancin da sai ya gwammace bai sanshi ba a rayuwarsa kuma yanzu ma a juri zuwa rafi wata rana tulun zai fashe, miƙewa yayi ya shige bedroom ɗinsa tare da shigewa tollet wanka yayi ya fito ɗaure da towel a ƙugunsa, tare da zama saman stool din dake gaban dressing mirror, wayarsa dake ijiye gefe ya ɗauka tare da buɗeta ya shiga galary pictures ɗin Ablah ne wanda ya ɗauketa ba tare da ta sani ba murmushi ya saki tare da lasar lips ɗin sa yana bala’in ƙaunar Yarinyar, yayi zaman turai yaga mata iri iri sai dai bai taɓa cin karo da macen da ta tafi da zuciyarsa ba irin Ablah, Yarinyar ta haɗu kyakkyawa ce Mace ce mai sura da kuma diri, hmmm! Duk namijin da yasan Mace bazai taɓa yadda yaga Ablah ya barta ba, still dai murmushi ya kuma saki tare da furta.

“Nayi alƙawarin shigo dake cikin rayuwata zanyi iya ƙoƙarina domin kare rayuwarki bazan taɓa bari ki cutu ba, ina sonki Soyayya ta haƙiƙa tabbas ke ƴar baiwa ce ba kowa bane zai fahimci haka sai wanda ya nutsu ya fuskanci rayuwarki, i love You.”

Yayi maganar yana sakin murmushi tare da mannawa picture ɗin kiss, Vaseline ya shafawa jikinsa tare da feshe jikin da turare, gajeren wando da bes ya saka tare da faɗawa saman bed ɗinsa yana lumshe idanunsa, bai juma da kwanciya ba bacci ya ɗaukesa.

A matukar razane take kaiwa da komowa cikin room ɗin nata, hankali tashe, ringin ɗin wayarta ne ya sata saurin saka hanu ta ɗaga kiran tare da karawa a kunnenta.

“Ina jinki Hajiya Mansura, ya akayi.?”

“Ya naji kamar hankalinki a tashe lafiya kuwa?”

Idanunta ta runtse cike da damuwa tace.

“Ina kuwa lafiya! Mansura tunani nake anya kuwa Al’ameen bai fara fahimtar wani abu a kaina ba kwana biyu ya sauya min yana min wasu abubuwa wanda da baya min su.”

“To amma meyasa kikace haka Wacce ƙwaƙƙwaran hujja kike dashi wanda yake nuni da abinda kike zargi.”?

Numfashi Aunty Amarya ta saki tare da bata labarin ganinsa da take a bazata yayin da take magana.

Dariya Hajiya Mansura ta saki tare da cewa.

“Oh amarya kina da damuwa wallahi ta yaya Al’ameen zaisan waɗannan maganganun yayi shuru ya ƙyaleki, hmmm! Kema kinsan abinda bazai yiwu bane, bai jiki ba mubar ma wannan maganar, kin san meye, nayi dukkan bincike akan wannan Yarinyar Nafeesa kinsan ƴar bariki ce karuwa, sai dai abinda ya ɗaure min kai har yanzu na kasa fahimtar son da take yiwa Al’ameen da kuma dalilin da yasa ta rabu da Haidar, domin kuwa fuska biyu nake mata kallo ta wani ɓangaren gani nake son gaskiya take masa ta wani ɓangaren kuma sai naga kamar kuɗin sa take so, har yanzu ban gama tantance ta ba ina buƙatar ƙarin lokaci domin akwai abubuwa da yawa da ya kamata mu sani a kanta abinda na iya bincikowa akanta shine karuwa ce tana bin maza.”

Kanta Aunty Amarya ta dafe tare da cewa.

“Hmmm! Mansura abubuwa sai tsananta suke har yanzu bamu samu rabi daga cikin cikar burinmu ba, ina gudun karmu tura mata ta tashi ta barmu da ƙura.”

“Amarya ki daina mana mungun baki, insha Allah sai burinmu ya cika, ki bari zanzo cikin satin nan wataƙil ma ko na shigo gobe zamuyi magana akan wannan ƙaramar tantiriyar ABLAH ki kwantar da hankalin ki.”

“To shikenan sai kinzo.”

Tayi maganar tana ijiye wayar, tare da sakin ijiyar zuciya zama tayi cike da munguwar damuwa domin kuwa tunda ta samu labari akan wannan Nafeesan taji zuciyarta na tsinkewa, ta yaya zata juma tana shuka sanda bishiyarta ta fara zara ta fara fidda yabanya sannan wata tazo tace itace zata girbe wannan BISHIYAR domin ta amfana dashi, wannan ba abu bane da zai yiwu ya zamo dole ta kawo ƙarshen wannan Yarinyar, Afnan ce tayi Sallama tana shigowa, amsawa tayi kusa da ita ta zauna tare da duban Aunty Amarya tace.

“Aunty wai meke faruwa ne a gidan nan.?”

A ɗan razane Aunty Amarya ta kalleta tace.

“Meke faruwa kamar yaya me kika gani.?”

“Hmmm! Aunty ɗazu ina cikin kitchen naji kamar Inna Jumma tana waya da Daddy naji tana ta mita akanki.”

“A kaina ni kuma to me tace na mata?”

Duban Aunty Amarya tayi sai ta tuntsire da dariya tace.

“Kai Aunty har kin razana, ni fa wasa nake miki babu wata waya da Inna Jumma tayi.”

Haɗa ranta Aunty Amarya tayi domin kuwa zuciyarta ta tsinke sosai cike da ɓacin rai tace.

“Afnan ni Abokiyar wasan ki ce dan ubanki daga yau ya zamo na ƙarshe da zaki kuma zuwa kimin irin wannan wasan uban me ma ya shigo dake?”

Cike da mamaki ta kalli Aunty Amarya daga wasa shikenan ranta ya ɓaci.

“Kiyi haƙuri Aunty banyi zaton ranki zai ɓaci haka ba, na miki wasa ne kawai saboda nishaɗi, Inna Jumma ce tace kije ki tana bedroom ɗinta, sannan wai ki tafi mata da maganin.”

Tayi maganar tana tashi cikin sanyi jiki tabar room ɗin tsuka Aunty Amarya taja itama cike da ɓacin ranta da damuwar Nafeesa da ta Ablah, tashi tayi ta ɗauki maganin ta fita.

*****

Shi kuwa Al’ameen da sallama ya shigo part ɗin su Haidar Madina ya samu zaune cikin falon.

“Sannu da shigowa yaya Al’ameen.”

“Ina Momma?”

“Tana kitchen.”

“Kitchen kuma ina mai aikin naku da Momma zata shiga kitchen da kanta?”

“Yaya Al’ameen bata da lafiya tana can gidan su.”

Cike da tsawa yace mata.

“Shine dan ubanki zaki barta ta shiga kitchen da kanta meye amfanin ki da baza kiyi aikin gidan ba, wato na fahimci ɗan banzan ganda yana damunku to ki tashi kije ki amshi aikin idan har kika kuskura na sake shigowa na samu Momma a kitchen ke kina zaune kina danna waya sai na sauya miki kammani shasha.”

Tashi Madina tayi jikinta na rawa ta nufi kitchen ɗin, shi kuma sama ya haura bedroom ɗin Haidar hanu yasa ya buɗe door ɗin ya shiga da Sallama yana kwance yayi shuru yana kallon celine cike da tunani domin kuwa har Al’ameen ya shigo ya zauna a bakin bed ɗinsa baisan ya shigo ba.

“Haidar! Haidar! Haidar!”

Ya kira sunansa kusan sau uku shuru Haidar bai jisa ba, hannu yasa ya taɓa sa tare da cewa.

“Haidar!”

Sai yanzu ya dawo hayyacinsa da kallo yake bin Al’ameen cike da haushinsa idanunsa ya runtse tare da miƙewa a fusace yace.

“Meya kawoka bedroom ɗina kazo ne ka kasheni sai ka huta?”

Kansa Al’ameen ya girgiza tare da cewa.

“Haidar ni ne zan kasheka wai meyasa ka kasa fahimtar AMININKA, ka yarda dani Haidar bani da alaƙa da Nafeesa wannan Yarinyar makirace shiyasa tun farko nake ce maka ka rabu da ita meyasa zaka yadda da ita fiye dani ɗan uwanka da muka taso tun yarinta, meyasa ka nacewa Soyayya meyasa ka kashe zuciyarka akan mace take wulaƙanta ka, ba a kaina ya kamata ka gwada zuciyarka ba akanta ya kamata ka gwada kana kan kuskure Al’ameen abinda nake son ka fahimta.”?

“Ƙarya kakeyi Al’ameen bana kan kuskure, kaine kake kan kuskure domin kaine maci Amana butulu wanda baisan hallaci ba, ai kama kasheni mai yayi saura gangar jikinane kawai bai fadi ba, tunda harka rabani da numfashi na aika gama kasheni sai dai abinda nake son ka gane shine yasarwa maƙiyi makami domin saranda wannan babbar asara ce da kuma mummunan faɗuwa, idan har kana son mace da zuciyarka kuma da gangar jikinka to Tabbas zaka jajurce ka kuma shanye duk wani wulaƙancinta ka nace mata yau da gobe dole zata fahimci gaskiya ta dawo gareka ba rashin zuciya bane ba kuma kashe zuciyata nayi ba Soyayyata nake jawowa kuma zata dawo gareni Nafeesa itace rayuwata muddun ina numfashi bazan bari ka mallaketa ba.”

Yau Haidar ya ƙara tsorata Al’ameen domin kuwa a yanda ya fahimcesa zai iya aikata komai saboda wannan Nafeesan.

“Haidar ka dawo cikin…”

“Ya isa haka babu abinda zan ƙara saurara daga gareka, na tsaneka na tsaneka ka fita min daga bedroom ɗina na daina ganin wannan mummunar fuskar taka.”

“Haidar ni kake kora daga bedroom ɗinka.?”

“Ƙwarai kuwa na koreka ba iya bedroom ɗina kawai na koreka ba har cikin rayuwata domin kuwa a yanzu bani da maƙiyin da ya fika ka fice min da gani kafin na wulaƙanta ka.”

Murmushi mai ciwo Al’ameen yayi tare da cewa.

“Ba sai ka wulaƙanta ni ba zan fice sai dai ka sani akwai ranar da zakayi danasanin kalamanka a kaina.”

Yayi maganar yana ficewa da sauri idanunsa na cikowa da hawaye da sauri ya sauƙa a step ɗin, ko Momma dake cikin falon bai lura da ita ba ya fice a guje cike da mamaki ta miƙe tsaye domin kuwa idan ba idanunta bane suka mata ƙarya kamar hawaye take hangowa daga cikin idanun Al’ameen, bedroom ɗin Haidar ta haura da sauri cikin tashin hankali yana zaune shima ya dafe kansa hawaye na gudu saman fuskarsa shi kansa baya jin daɗin abinda yake yiwa Al’ameen sai dai hakan shine ya dace da maci Amana irinsa.

“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un! Me zan gani haka Aliyu kai kuka Al’ameen shima kuka, hmmm dama na sani dole wannan sauyawar taka akwai wani abu dake faruwa kullum kana cikin damuwa ka maida ɗaki wajen zamanka komai naka ya sauya meke faruwa tsakanin ka da Al’ameen?”

Ɗago idanunsa yayi sai kuma ya ƙara sakin kuka mai sauti.

Hakan ba ƙaramin razana Momma yayi ba zama tayi bakin kujerar dake room ɗin tace.

“Karka ɗaga min hankali na mana Aliyu ka faɗa min meke faruwa.”

“Momma na tsani Aminta da kuma yarda domin kuwa babu komai a cikin sa sai tsantsar cin amana da kuma yaudara, Momma ashe dama ɗan uwanka zai iya cin amanar ka, na tsani Al’ameen domin kuwa ya ha’in…”

Wani irin mari momma ta ɗauke Haidar dashi tana miƙewa tsaye tare da nuna Haidar da yatsa tace.

“Idan ka ƙara furta munguwar kalma akan Al’ameen sai na ci maka mutunci, Al’ameen kake cewa ka tsana shine kake jifa da munguwar kalma, Aliyu faɗamin dalili guda ɗaya wanda yasa kake yiwa Al’ameen waɗannan mugayen kalaman?”

Dafe fuskarsa yayi idanunsa suka kuma yin jajur hawayensa ya ƙara gudu tunda yake abinda Momma bata taɓa masa ba kenan a rayuwarsa tsawa da kuma faɗa.

“Momma ina hujja bazanƙi Al’ameen haka kawai ba, Al’ameen ya ƙwace min zuciyata Nafeesa yayi min ƙwacen budurwa ya ɓatani a idanunta ya koma yana Soyayya da ita Momma Nafeesa rayuwata ce bazan moru ba idan babu ita.”

Dariya Momma tayi tana yiwa Haidar kallon mahaukaci tace.

“Aliyu ka manta da maganar dana maka ko ka manta cewa Rufaida itace matar da zaka aura ka ɗauka maganata wasa nake maka, to bari kaji wallahi baka da wata matar Aure idan ba Rufaida ba, Nafeesan banza Nafeesan wofi shasha, ko mahaukaci ka faɗawa wannan maganar bazai yarda da kai ba ni Uwarka nasan Al’ameen bazai taɓa aikata abinda kake zarginsa dashi ba, wawa kawai akan mace har zaka juyawa ɗan uwanka ba, to bari kaji Al’ameen ba abun wulaƙantawa bane yana ƙaunarka har zuciyarsa wallahi wallahi Aliyu muddun baka dawo hayyacinka ba, lallai zan maka mummunan hukunci, Al’ameen ɗan uwanka Kuma jininka ne ruwa bazai wanke ba haka reza ko wuƙa bazai kankare ba, Rufaida itace matarka gwara ka cire wannan shashashar yarinyar a ranka.”

A matuƙar razane yake kallon Momma cikin tashin hankali meyasa akafi son Al’ameen fiye dashi kowa goyon bayansa yakeyi, cikin tashin hankali yace.

“Momma…”

“Rufe min baki karka cemin tak dan ubanka na juma da yanke hukunci zartar dashi ne kawai ya saura Rufaida itace matar ka, sannan kaje ka bawa Al’ameen haƙuri idan ba haka ba ni da kaine.”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Aminaina Ko Ita 48Aminaina Ko Ita 51 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×