Skip to content
Part 4 of 13 in the Series Abbakar by Fadimafayau

Kamo hannun sa Mahfuz ya yi, cikin muryar tausayi yace “Haba Abubakar mene haka, kabarni inji da zafin ciwon son da ya kamani ba sai ka haɗamun da baƙin cikin ƙin saurara ta ba.”

Shiru Abubakar ya yi kafin ya dawo ya zauna “Wai khair dai da kai ta bani labarinta, khair da kayiwa…” Rufe mishi baki Mahfuz ya yi  “ehfa ita wadda tai sanadin fa’danmu kwanaki yanzu ba sai ka sa mun kuma faɗan fa”, taɓe baki Abubakar ya ya ” You must be joking, it’s not love” Abbakar ya fa’da “wallahi Ba wasa nake ba I mean my words.” Inji Mahfouz.

Hmm Abbakar ya yi kwafa”Anman kaima ka cika tarar aradu da ka how do u think zata so ka?”

Narai narai ya yi da idanu ” Abbakar nasani nima ba lallai tasoni ba, nasani zan iya zama mutun na farko da duk duniya ta tsana, sedai ba lefi na bane kullin innai ‘ko’karin mantawa da ita se abin yaci tura kai nifa kamar ‘karan santa ake,”

Abbakar yai ‘dan murmushi irin na tausayawa “natausaya ma, anman kasan mene? alhakinta ke
‘dawainiya dakai.”

Damƙe leɓe Mahfouz ya yi yana gyada kai ” Yanzu abinda zaka ce kenan?, nagode”

Ɗaga gira Abubakar ya yi “no ai gaskiya ce nasan kuma kasani sedai kaki  kasallama. To yanzu kai sa’ace kasan inda take se kaje kace kanasanta, ko me?

Cike da kwarin gwiwa Mahfouz ya ce” me zai hana shi yasa ma nazo dan ka temakan in nemota dan in convincing ‘dinta ta yadda ta aureni”

hhhhh Abubakar yasa dariya ” lallai mutumina ka kamu da yawa inji Abbakar .

Tsuke fuska Mahfouz ya yi ” kasan Allah inkana dariyar nan mugun haushinka nakeji inbazaka temakanba ne ka fa’dan.” Ya faɗa a hasale.

Kafin Abbakar yace wani abu wayarshi tayi qara da sauri Mahfuz ya le’ka, to sarkin gulma kalli da kyau sukai dariya, tare da sallama ya Amsa gami da fa’din “lafiya lau ‘kanwata ya gida ya kike?” sun ‘dan ta6a fira kafin suyi sallama.

Kallon sa kawai Mafouz ya ke yana ƙare wayar ya ce ” Daman nafa’da u are in love fa’dan ne bazakayi wato baka yadda dani ba shiyasa bakasan fa’dan sirrinka ko”

Dafe kai Abubakar ya yi cike da ƙorafi ” oh my goodnes kanada matsala wallahi.”

Wayarsa ya ‘dauka ya kira ta, bata wani yi ringing da yawa ba ta dauka, ” hello qanwata”
” na’am Yayana, lafiya dai yanzu mun gama waya ka kuma kira?, “

“Ki bari kawai wannan abokin nawa ne da nake baki labari, yakesan magana dake wai yana fa’din muna dating junanmu ne,” tai dariya baka fa’da masa kaine ma’daurin aurena ba gashi ki fa’da masa dakanki.

Sun gaisa da mahfuz kafin tace “abokin yayana be fa’da ma inada miji bane? yai dariya taya zai fa’dan?”

“Ga mijin nawa to ku gaisa” kafin yace wani abu yaji muryar namiji ya amsa suka gaisa ” ai kullin inajin labarinka gun Khairi se yau Allah yai zamu gaisa,” mahfuz yace ” bama Abbakar ‘din bane abokinsa ne,”

” oh to bashi mu gaisa sun gaisa ya kashe wayar batare da baima khairiyyan ba.”

Kallon sa Abbakar ya yi bayan ya mayar da wayar sa aljihu “Hope u are now convince?”

yai dariya ” sosai ma,”

” kaga daga yanzu nagane wallahi u don’t trust ne” inji Abbakar

“What harfa rantsewa kake?” Mafouz ya faɗa daɗa alamun shock

“eh wallahi inma ka yadda dani not like I do, a wurina u don’t have to prove what u said is gaskiya ko qarya, what I need na yadda shine kawai kace ‘din in yadda.” Ya faɗa da Serious face.

Karamin murmushi Mahfouz ya yi “Am sorry nima ai bance dole se ka kirata ba, impact ma bani nace ka kirata ba”

mtss Abbakar yaja tsaki ” kaji dashi yamiƙe yai cikin gida.

Gabaki ɗaya abun duniya ya ishi Abbakar dan ya rasa wazai fa’dama abinda ke damunsa gashi ‘dan ganin ummun da yake ma ya dena kwata kwata.

Yau yana zaune gabaki ɗayadaya duniyar ta masa zafi yarasa me zaiyi kamar daga sama idea tazo masa ya miqe yana murmuahi nasan me zanyi.

Wayarsa ya duba kaf babu number ‘din da yake nema can ya tuna a littafin da ya rubuta ya’dauko ya kira ringing ‘daya ya ‘daga.

Daga ‘daya bangaren aka yi sallama ya amsa yawwa ina magana da ” Mas’ud ne?” Ya tambaya bayan an daga wayar “eh” aka bada amsa to ka fa
sanar da class members ‘dinka ranar litinin zanyi C.A ‘dina kana magana da Abbakar muhammad Abbakar” ok sir nagane zan sanar dasu” ya kashe wayar.

Shi ka’dai yasan dalilin yin hakan ada be ma da niyar yin test ‘din a ‘yan kwanakinnan.

Zaune su Fatima suke suna karatu Fatima ta ɗago daga sunkuyen rubutun da take “Wallahi Aisha narasa yazanyi kinsan monday mutumin nan zaiyi test gashi Ummu bata da lafiya nasan kuma in nayi mata zai iya ganowa tunda yasan sunanta” ta faɗa cike da jimami.
” kumafa haka ne yanzu ya zamuyi to kinsan baya make up, we need to do something.” Inji Aisha

Mas’ud ne yace ” kawai kuzo muje office ‘dinsa inyaso se mu masa bayani in anyi sa’a in taji sauqi in yaso Allah se ya mata “

“Ni wallahi tsoronsa nake ji” inji Fatima daurewa “zakiyi muje” Mas’ud ya faɗa yana haɗa kayan sa “yazanyi haka zani ai.” Ta faɗa a langwaɓe.

Sunyi sa’a kuwa yananan bayan sunyi nocking yace su shigo, suka kuwa shiga da sallamarsu, sun gaisheshi, kafin captain yace “daman sir game da test ‘din dakace zakayi ne”

” ok wata matsala ta farune?” ya fa’da yana duba takaddunsa “a’a daman ɗaya daga cikin student dince ba  lafiya shine mukazo mu fa’da ma ko in taji sai’ku za’a mata make up.”

“Wace kenan?” Abbakar ya fada har lokacin hankalin sa na kan takardun sa, ” Ummulkhairi Yasir Mahmud” Aisha ta faɗa, saida gabansa ya’dan kafin yace ” meke damunta?”

“eh daman an mata CS ne tazo haihuwa” Mas’ud ya fada yana fatan Abbakar ya duba yaji tausayi, a’dan ratsane ya ‘dago “what CS?” ya fa’da a yanayin dashi kansa besan sanda ya shiga ba, ” eh” suka ce. “

“ok Allah ya bata lafiya” suka amsa da ” amin.”

” Ungonan ya miqo paper rubutan sunanta da registration number ‘dinta, “

“ok sir” Ma’au ya amsa ya yi rubutu kafin ya ce “gashi na rubuta”

Amsa Abbakar ya yi ” to intaji sau’ki sai tazo ta sameni ta tawo da shaida ‘din tabbas bata da lafiya”

” ok to sir mungode” suka fuce.

Hankalinsa gabaki ‘daya ya tashi tausayinta duk ya kamashi ashe Aiki akai mata yadda ya damu wani 6arin na zuciyarsa ke faɗa masa matar wani ce fa kake damuwa akanta subhanallahi ya fa’da yai saurin miqewa ya shige toilet.

*Zancigaba insha Allah*

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Abbakar 3Abbakar 5 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×