Har ya kusa office ɗin Dr Mansur HOD ɗin su, sai kuma ya tsaya cak yana kallon Paper ɗin da ke hannun sa, wadda ya rubuta, Ko me ya tuna oho, kawai ya hau yayyaga paper ɗin tare da juyawa zuwa office ɗin sa.
Sam kasa yin komai ya yi, rufe office ɗin ya yi, ya dawo ƙasa ya kwanta, bawai dan yana jin bacci ba sai dan damuwa ta masa yawa, zaman ma wahala yake masa, yana jiyowa daga bakin ƙofa ɗaliba na bugawa, ransa a ɓace yake ji yake tamkar yaje yamiƙe ya zo bakin ƙofar ya. . .