Skip to content
Part 1 of 6 in the Series Addininmu by Salis M. Reza

GARGADI

Tabbas wannan labarin labari ne da ya shafe mu baki d’ayanmu, labari ne mai cike da darusan rayuwa, labari ne da ya shafi ni/ke/kai/su/shi/ita, da kuma kowa. Addininmu labari ne wanda zai mana hannun ka mai sanda. 

In ka san ko kin san za ki zage ni, to dan Allah kar ki fara karanta labarina, domin ba zan juri abun da a ka yi a kan littafin Uwata Ce Sila Ba. Za ku ji sunann fitattatun mutane, to bawai dasu muke yi ba, kuma ba labarinsu ba ne. sannan labarin fuska biyu ne, wato bangarori guda biyu. Da fatan zaku fahimta. A sha karatu lahiya.

TSOKACI

Wannan labarin dole zai ta’ba ka/ki, domin kuwa ya shafi kowa, in na ce kowa to ina nufin harda ke ko kai me karantawa. Sannan ina so amin uzuri, ban yi dan cin zarafi ga kowa ba, ban yi dan ‘kas’kantar da wani ba ban yi da niyyar wula’kanta wasu ba, na yi ne domin had’in kan al’ummar mu baki d’aya.

GODIYA GA ALLAH

Ina mai sake godewa Allah daya sayake bani aron dama da kuma lafiya da dogon nazari domin sake kawo muku wannan labari. Alhamdu lillh-Alhamdu lillh,*Allah kasa yanda nafara rubuta labarin nann lafiya Allah kasa na kammala shi lfy, Amin ya haiyu ya’kaiyun.

Bissimillahi rRahmanir Rahim

Babi Na Daya

Labarin ya fara kamar haka…

Kai gaskiya innah wallhi masu kud’i suna hutawa suna jin dad’in su, kinga gidan da mukaje jiya kuws? Wallhi nidai idan na mallaki wannan gidan to nida talauci guma har a bada, yayi can nikuma nayi nann. Innah ta kalleshi cike da gajiya da wannan surutun nasa Ta ce “To dame zakayi kud’in ance kanemi aikin gomnati kace kai badomin aikin gomnati kayi karatuba, to a haka zakayi kud’in? Kuma ance kafara zuwa kasuwa ka ce kai bayanzu ba, kazama daga wancan gidan sai wannan anya kuwa rayu zata yu a haka Abdul jabari? 

Abdul jabar wanda ya komar da sunan sa izuwa A J ya ce “Innah aikin gomnatin ne babu wani samu, nikuma da nakeso na zama shahararran mai kud’i a cikin garinnan sai kawai naje na kama aikin gomnati!! Ya ci gaba da cewa, yanzu fa a cikin wannan ‘kasar tamu idan ana lissafin masu kud’i bazaki ta’ba jin sunann ma’ai kacin gomnati ba saide Yan kasuwa sabo da haka ni kasuwanci zanyi, kuma ki jira lokaci… Kinga yanzu innah bari na miki misali, yanzu a ce nasamu ai kin gomnati ace ana biyane dubu hamsin, to acikin wata d’aya menene dubu hamsin zata mana, mu uku? 

Kinga ga kud’in makarantar Nana ga kayan sawa ga abin da zamuci. Sannan ba lallai bane bafa a biyani dubu hamsin d’in, amma in kasuwancine a rana d’aya ma Sai na samu dubu d’ari uku wallhi, to kinga Mai a keyi da wani aikin gomnati, Innah ta kalleshi cikin mamaki ta ce “yanzu Abdul jabaru kana ba d’an kowaba kake irin wannan lissafin wallhi kaji tsoron duni da mutan cikinta, ka rage son gud’i dayawa, yanzu abokankama da kuka taso duk ka zubar dasu saboda tsabar alfaharin ka na banza, kaje kana abota da Yayan manya, yau kaje gidan su wannan gobe gidan su wannan, anya Abdul kana tsoran wula’kancin mutane kuwa?

AJ ya ce “To innah in banda abinki yaza’ayi ina talaka kuma nayi abota da y’ay’an talakawa haba ai abumma sam baiyi dai-dai ba…kinga in Nana ta dawo kice ta shanyamin kayannan ana kirana. Kafin inna tayi magana har ya tashi daga zaunan da yake ya nufi d’akin sa ya ciro wayar sa daga caji yana mai ciro wata jallabiya ya d’ora a kan kayan da suke jikinsa kafin ya kalli in na ya ce “Inna watarana sai labari amma dai tabbas zanyi kud’i in Sha Allah. Innah ta ce “Nidai bazan dena maka addu’a ba Allah ya shiryamin kai domin ni harga Allah ina tsoron wannan shegen son kud’in naka ya jefaka a damuwa.

A J kuwa yana fita ya hangota a gefen gidan su tana tsaye tana waige-waige kamar mara gaskiya, yana hangota yaji wani sanyin dad’i domin kuwa yasan an dace. da sauri ya ‘karaso gurin ta yana mai washe baki, kafin yayi magana ta kamo hannun sa suka shiga cikin wani lungu, ta ce “A J I don’t get the money. 

Kallon yayi da kyu ganinn irin shigar da ke jikinta daga ita sai riga mai siririnhannu sai wando jins wanda ya tsaya mata iya cinya, kana kallon shigarta kasan ba musilma ba ce, cikin jin haushi ya ce “what are you saying? “ai see idont have the money, jin haka yasa AJ juyawa zai bar gurin tayi saurin sake kamoshi ta ce please AJ listing to me? Kallon ta yayi cikin muryar Hausa domin kuwa yasan baji takeyi ba ya ce “in bandama ina son kud’i Mai zaisa na dinga tsayawa da ke kidubi irin shigarki in wani yazo hucewa ya gammu a haka ai shikenan, baride na samu abun da nakeso a gareki wallhi bazaki sake ganinaba.

Zarah ta ce “What are you saying? Ya ce “no is not you. Nann take suka fara magana cikin turanci domin kuwa ita bata jin Hausa ko zo in kashaka bata saniba. Zahrah ta ce “AJ saura kad’an Daddy ya kamani kuma nasan yanzu yasan nice nake sata masa kud’i, kuma duk kaine kake sakani. A J cikin rashin tsoro ya ce “kinga ni in bazan samu ba kawai a bar maganar kuma daga yau bani babu ke, na ce miki waya zan sake tawa tayi ‘karama mutane suna rainani, yanzu a ce ina da ke amma ina ri’ke irin wannan wayar! 

Ganinn ransa ya b’aci ne yasa zahrah ta ce “please I’m so sorry I well bring the money for you tomorrow, tafad’a kamar tayi kuka. Tabbas zahrah tana son A J sosai hakanne yasa bata son ‘bacin ransa, yayinda shi kuma domin kud’in iyayenta ya keson ta yana amfani da itane kawai domin samun kud’i. da sauri ya ce “Yawwa ko kefa, ta ce “To kayi dariya? Ai kuwa nann yayi dariya tazo da gudu ta rungumshi tana cewa I love you so much my A J, shikuwa bai amsaba sai son ganinn ya cireta daga jikin sa ya keyi.

Zahrah kuwa tana zuwa gida ta shiga tinanin yaza’ayi ta samu gud’in nann ta kai masa gashi Daddy na gida. Haka ta tashi ta nufi d’akin Mommy cikin sand’a amma tana zuwa taga Mommy na zaune tana cin uban ‘kwalliya kamar wata amarya, komawa tayi da baya ta shiga d’akin Daddy ai kuwa ta samu yana barci. Gurin da tasaba d’aukar kud’in ta nufa cikin sand’a kana ganinn ta kaga mara gaskiy. Wani ‘karamin kurido ne a kasan drowan kayan sa, nann take Zarah ta fara jawoshi a hankali ai kuwa tana zarowa taga kud’ad’e masu uban yawa wanda sun ci uban wanda take gani a baya…

Ai kuwa saida ta tsorata tsabar yawan kud’in tana cikin hakane wayar daddy tafara ringtone alamar kira, ai kuwa da sauri ta tura abun kud’in ciki ta rufe ta fad’a ‘kar’kashin gado wanda yayi dai-dai da shigowar Mommy d’akin sannan Kuma Daddy ma ya farka.

Bayan ya amsa wayar ne ya kalli Mommy ya ce Eliza we are you going In this time? Cikin yaransu na tibi ta ce “Sorry sar yanzu I’m coming back now…ta ci gaba da cewa wai dama kana gidane baka fitaba? Daddy ya ce “okay bari nima nashirya mufita munada mitin on this time, da sauri ya shirya Mommy na tsaye har suka fita a d’akin Daddy ya kalli Mommy ya ce “Bari na ‘kulle d’akin nann domin kuwa na daina yarda da kowa a gidannan kullum sai an d’auka min kud’i kuma arasa waye ya ke d’auka. Mommy ta ce “Ni kaina ana d’aukar min kud’i Kuma na tabbayi Zahrah ta ce ita ba itaba ce shima Samuel ya ce bashi bane to kaga wazamu zarga acikin su?

Daddy ya ce “Samuel ne yake d’aukar kud’in in bashiba to ita zahrah me zatayi da kud’i masu yawa? Mommy ta ce komade waye zamu kamashi. Haka Daddy ya rufe gofar ta waje ya murza ki har sau uku kafin ya saka kin a aljihun…ya d’ago kai ya kalli Mommy ya ce “We zahrah? Mommy ta ce “taje gidan su Usha, ta bashi amsa tana mai rufe gidan gaba d’aya.

Zahrah kuwa bayan daddy ya fitane ta zaro abun kud’in sannan ta fara d’iba Saida ta kwasa da yawa domin kuwa sunfi Wanda ta saba d’iba a baya, sannan cikin sassafar tayi hanyar fita daga d’akin, tana zuwa taji ‘kofar a ‘kulle, ta buga amma taji ko motsi batayi, nann fa ta zubar da kud’in a gurin ta fara rusar kuka.

 Kano State 

 Zainab Ambato 

Shahararriyar mawa’kiyar Annabi Muhammad sallalahu a w s, wacce tayi fice sosai a harka yabon Annabi Muhammad sallalahu a w s, wacce kowa yasan da zamanta a wannan ‘kasar tamu domin kuwa tana lokacin ta. Kallon wani video da abokin takun sa’karta yayi nayau Wanda yake caccakar bidi’a da kuma masu yinta takeyi, kallon sa takeyi ganinn yanda ya dage yana bayani akan wa’kar da ta sake jiya, cikin tsananin b’acin rai da jin d’acin abun da yake furtawa ta ce “Yau kuma wanann mutumi harda cikin mutunci a cikin baton nasa!! Kafin tayi magana taji ya sake cewa…

“Al’umma wallhi ku guji ai kata bidi’a kuma ku guji masu ai katata, jiya naji wata daga cikin su ta saki wata sabuwar wa’ka, tana cewa…(bagudu baja dabaya kan ‘kwanar shehu maulansu). Ya rera wa’kar cikin bar kwaci, ai kuwa nann take Jamar gurin suka kwashe da dariya sannan ya ce “kutsaya kuji, dan Allah wannan begen annabine kodai begen wani? Nann take suka amsa da cewa begen wanine… Kafin ya sake magana Zainab ta kashe wayar cikin tsananin b’acin rai tayi hurgi da wayar tana maijin d’acin abun da yake mata. Tashi tayi ta bar d’akin ta nufi d’akin mahai fiyar ta kamar zata kamar zata tashi sama.

Da sallama ta shiga d’akin kamar yanda ta saba, amma taji ba’a amsa mata ba, hakanne ya bata damar shiga cikin d’akin, tana shiga ta tarar da ita tana sallha sai kawai ta juya izuwa d’akin yayan ta, ai kuwa tana shiga ta tararr dashi shima yana kallon wannan video d’in, cikin sauri ta isa gareshi ta ce, “Isa kaga abun da wannan gayan ya sake min ko? Ni bansan mai na tare masa ba, ni bana shiga har karsa amma shi kullam yana bibiyata, in anyi magana ya ce shi Wai mau ilimine, cikin ‘bacin rai ISA ya ce “to Ina ilimin yake a nann mutum kullum saide ya tara mutane yana cin zarafin wasu saboda basa bin gungiyar su, in anyi magana kuma suce wai su sunnha sukeyi haka sunna take? 

Isa ya ci gaba da cewa “wallhi wannan yaron haushi ya ke bani, mutum Dan Allah ya baka ilimi sai kuma ka dinga kallon kowa a banza! in ilimin nanne yasan mun sha kansa domin yaje yayi bin cike a kan wannan gidannamu. Zainab ta ce “Sai su dinga fakewa da cewa mu yan bidi’a ne sukuma yan sunah, Kuma sune suke ai kata bidi’a d’in a bayan ‘kasa. Isa ya ce “yanzu to yaza’ayi? Ta ce “Nima zan fara mayar masa da martanine domin in ba hakaba bazai san cewa nima niceba.

Cikin jin dad’i ISA ya ce “toma wai meye wannan yaron zai nuna miki in banda dogon gemu kamar bunsuru, Zainab ta ce “Toma wai yaushe a ka san dashi? Shifa albarkacin mahaifin sanema yasa jama’a suka san dashi amma har zaizo yana min habaici to wallhi ina dai-dai da ubansama ba shiba. Haka dai ISA da Zainab suka dinga zagin sa saboda abun da ya musu.

Abdallah 

Cikin tsananin b’acin rai yake kallon ‘kanwar tasa cikeda jin aushin abun da tayi ya ce “Waye wannan? Itama cikin dubur-burcewa ta ce “Shine wanda nake fad’a maka zai zo gurinka tin…”tin kafin ta ‘Karasa ya katseta da cewa… “Wannan d’an bidi’ar zaki kawo mana gida kice wai shine zaki aura!? Bakiji abun da nace mukuba ko Maryam ta ce “Yaya wallhi bad’an bidi’a ban… “Zakimin shiru ko saina fasa miki baki yanzunnan?

Abdullha ya kalli Maryam ya ce “Dabansan ko shid’in wayeba da saiki min ‘karya, to bari kiji wannan yaron har ubansa na sani saboda haka daga yau bake bashi karna sake ganinn ku tare kinji na fad’a miki ko?. Ta gyad’a masa kai sannan ya bar d’akin cikin ‘bacin rai.

Maryam kuwa cikin kuka ta nufi d’akin mahaifiyar su domin sanar da ita komai, tana zuwa ta tararr da sauran Yan uwan nata dukkansu a gaban maman nasu suna d’aukar karatu hakanne yasa ta share hawayenta itama tabi layi domin kuwa tasan babu wanda zai kulata har sai in sun kammala karatun.

Abdullha kuwa part ‘dinsa ya nufa yana jin mamakin taurin kai irin na Maryam, duk cikin ‘kanyansa tafi kowa taurin kai ga rawar ‘kafa ba kamar Sadiya da Nusaiba ba. Cikin zuciyar sa ya ce “ni na had’a jini da yan bidi’a a’a bata isaba akan wannan maganar zan iya mugun ‘bata mata rai sosai.

Zainab VOP

Da sauri ta shiga gurin Mama lokacin ta idar da sallah hakane yasa ta kwashe komai ta sanar Mata abun da abdullha ya sake mata, Mama ta kalleta ta ce “Zainab ke mace ne shikuwa na mijine kinga in kina biye masa zaku zubar da girmanku a gurin al’ummar garine dukkanku, gashi kuma dukkanin ku jagororine a gurin al’ummar ku saboda haka kibar shi karki biyewa wance yayan naki mai zigaki.

Farkon labarin kenann. Dan Allah kar ku zargi ko ina yi don cin zarafin wata gungiyar ne; ku kalle lamarin da Kyu zaku fahimci Ina na dosa.

S. Reza

First Class Writers’ Association

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Addininmu 2 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×