Skip to content
Part 1 of 1 in the Series Alkawarin Allah by Matar Sadiq

Bissimillahir Rahamanir Rahim

“Acikin babban birnin kano, wanda ke cikin birinin babban yanki wato Nigeria. me dauke da mutane Kala kala yare iri iri masu al’adu daban daban. Mafi yawa daga cikin su musulmai ne kuma hausawa ne, da ma mabiya addinin maban-banta ra’ayi”.

Kano kasace babba daga cikin manyan yankuna mafiya girma acikin Nigeria.
Duk wanda yasan garin kano, yasan cewar sun tara kabilu kala kala wadanda suke zaune a cikinta, mafi yawansu daga ciki hausawa ne

Haka kuma garin kano garine mai albarkatun kasuwanci kala kala. Basu da rena sana’a duk kaskancinta hakan yasa Allah ya wadata wasu daga cikinta dunbun arziki mai tarin yawa wasu daga ciki talakawa ne masu rufun asiri da yawa daga cikin su masu ilimin addine hakama na zamani ba’a barmu a baya ba.

Kano ta dabo tunbun giwa ko dame kazo anfika. Garin sarki sunusi lamido mai masoya da yawa. Garin governor ganduje.

Alhaji Usman Ibrahim matawalley: dan asalin garin yolah karkashin local government Jumaita wanda neman kudi ya kawo shi cikin garin kano, Alhaji Usman yana da mata guda daya Asma’u tare da ‘ya’ya mata guda biyu,

Maryam itace babba, sai kanwarta Fatima.

Alhaji Usman Ibrahim matawalley’ talaka ne amma suna da rufun asiri..
Alhaji Usman Ibrahim cikakken bafulatani ne, usul wanda har yanzu Hausa bata gama zama a bakinsa ba. Farine sosai tamkar balarabe.

Dukkan ‘ya’yan gidan kyawawa ne sosai masu tsananin farar fata. Lallausan gashin kai irin na fulanin asali,
Musamman ma Maryam wadda tafi kowa kyau dtsananin mai tsantsi tare da farar fata.

Maryam doguwa ce, amma ba can sosai ba, tana da cika kadan amma bata da wani kiba
Tana dogon hanci sosai, tare da madaidaicin karamin bakinta irin ma kyawawan ainihin fulani
Suna zaune ne ne acikin gidajen nan ne irin na gomnati, duk da cewar mafiya yawan gidajen unguwar na gomnati ne. Haka nan bawani girma ke gare shi ba, amma suna zaune ne cikin walwala da farin ciki tare da wadatar zuci

KANO ➡
MARAYAM POV.
Cikin sassanyar murya tayi sallama, sanye take da dogon hijabinta maroon color, do gone hijabin har kasa wanda yay matukar kara fitowa da tsamanin kyawun halittarta musamman yalwatacciyar baiwar kyawun dake kan fuskarta..Mahaifiyarta dake zaune a saman yalwatacciyar barandar tasu tana gyaran shinkafa

Fuskarta dauke da murmushi ta amsa mata sallamar Cike da annuri ta dago tana fadin, “Sannu da hanya maryam. Ya makarantar, yau kam da dukkan alamu kin gaji sosai!”
Dariya tayi tare da zama agefenta, sai da ta ajiye katon alkur’anin dake hannunta, ta juyo tana fadin

Wallahi mama kamar kin sani.

Amma duk da haka naji dadin zuwa tilawata yau sosai, amma duk da haka bangaji ba, inasa ran gobema zan koma.

Murmushi maman tayi’ tare da cewa hakane maryam, ai dama ba’a gajiya da neman ilimi’ Allah ya bada sa’a.

Ameen mama!! Ina kuma fatima taje da yammacin nan?.
Wallahi na aiketa nan gidansu mariya kawar ki.

Ai yanzun zaki ganta dan ta dade da fita a gidan.

maryam kin gaji sosai, ya-kamata kije danyi wanka ga can ruwan zafi, idan kin kammala ki shiga kitchen ki debo abinci.

Mikewa tayi tare da cewa, mama!! Da kanki kika dafamun ruwan zafin ko fati ce ta dafamun?

Murmushi ta dan saki tare da cewa “nine na miki momy nah”
itama fuskarta dauke da murmushi tace, “Allah sarkin mamana ma gode Sosai, gaskiya ni ‘yar gaban goshin kice”.

Tana kai nan ta nufi yalwataccen falonsu wanda yake dauke da manyan kujeru masu kyau sosai, irin na masu karamin karfi.

Hijabin jikinta ta zare tare da ninke shi ta ajiye a gefe, tare da yin doguwar mika. A kasalance ta fito ta nufi madaidaicin bayin nasu me cike da tsafta da kuma abun sha’awa

Cikin sassarfa ta fito daga wankan Saboda irin tsananin sanyin da takeji wanda yake ratsa dukkan bargon jikinta. Bata tsaya ba kai narabaka tsaye ainihin dakinsu ta wuce, wanda yake malale da cafect maroon color, gefe kuma katuwar katifarsu ce wanda itama aka kawata ta da duniyar kule mai kyau sosai,”

Wardrobe ta nufa ta ciro wani dan material mara nauyi mai cike kyau sosai.
Dinkin doguwar rigace eshap. Sosai tayi mata kyau da yake material din dark blue ne.
Bakin kwalli ta daura akanta tare dan shafa lotion mai kamshin dadi.

“Tunda ta fito bata zauna ba, aikin da mama keyi ta amsa duk da farko taki amincewa”. Sai da ta kammalla komai hatta shara kafin ta nutsu ta zauna zaman cin abinci.

“Shinkafa da wake ne tare da man kuli sai wadataccen salat da yake lokacin sane”.
A daidai lokacin fati ta shigo,

“ha’a aunty nah kin dawo kenam?. Sannu da hanya!” “Yauwa fati daga ina kike haka meya hanaki zuwa haddah?”.
“Kai aunty amma kinsan bana fashi a makaranta, yau din ne naji ina so na huta!”

“Hmm my blood kin cika shirme, yanzu banda abinki ina gajiya ko neman hutu a neman ilimi”.

“Dan Allah ki dage yanzun fa izunki arba’in da-wani abu, nima ina so naga kinyi saukar nan kamar kowa”.

“In sha Allah aunty amma ku tayamu da addu’a.
Kullum muna yi muku sai de kema ki kara himma, mai bema yana tare da samu”.

“gaskiya ne Aunty a tayamu da addu’a”
“Murmushi kawai tayi tana fad’in in-sha Allah”

“Yanzun ki shiga ki kai wa mama sakon ki fito muci abincin tare, idan mungama’ sai na doramaki karatun daga inda kika tsaya”.

Dariya tayi tare da cewa “ok aunty bari na shiga na fito dama yunwa nakeji”.
Ajiyar zuciya ta sauke tare dayin murmushi wanda yasa dimple dinta ya lotsa kadan.

“Tana shiga bata wani dauki lokaci ba ta fito, tare suka ci abincin, tare da wasa a tsakaninsu.
Cikin ikon Allah suka kammala, bayan sun gabatar da sallar magariba, daga bisani tai mata daurin kamar yanda ta kudurta. Bata sha wani wahala ba da yake itama fatin nada kaifin haddah sosai”.

I“sun dade acikin wanna daren suna hira kamar yanda suka saba kullum, amma dadewar da sukayi bai kai na kullum ba, da yake yau Abban nasu ya dawo gida da wuri.
Yau itama da wuri ta kwanta, tare da nufin tashi da wuri saboda yau suna da lecture a makaranta”.

“Washe gari da wuri ta farka tun asuba bata koma bacci ba, gari dan karayin haske ta kammala dukkan ayyukan da tasan nata ne,
Misalin karfe takwas da rabi ta kammala abun Karin kumallo”.

Dai dai lokacin mama ta fito daga daki.
Murmurshi tayi tare da cewa “sannu da kokari maryam”. “ina kwana mama?” Ta furta fuskarta cike da annuri.
“Ya gajiya”.
Dariya kawai tayi ba tare da tace komai ba, boket din karfen dake dauke da ruwan wankanta, kai tsaye bayan gida ta shiga, cikin kankanin lokaci ta kammala wankan ta fito.

“A gaggauce ta shirya saboda ganin lokaci ya danja kadan. Cikin riga da skirt na atamfa ta shirya bakace a tamfar mai touching din blue.”
Katon hijabinta ta zura Wanda yake jan kasa shima blue color.
Sauran takardunta ta dauka wanda a iya yau take tinanin zata bukace su, cikin karamar jaka ta sanya su, wanda yawancin mata ‘yan jami’a zaka ga suna yawan amfani da ita.

A gaggauce ta fito, kai tsaye falon mama ta nufa tare da yimata sallama.
“Maryam kinci abincin kuwa?”.
Murmurshi tayi tare da sauke ajiyar zuciya, har ga allah ba taci komaiba, dadi da kari abincin bashi da yawa kuma ga dan lokaci yafara tafiya.
Agogon wayarta ta duba, tare da dagowa fuskarta cike da annuri cikin harshen da bata sabayin karyaba tace, “Eh mama ai naci abincin tun dazu, kafin ki fito sai da nacima na hada ruwan wanka”.

Murmurshi tayi tare da cewa, “Toh allah yayi miki albarka’ Allah ya bada sa’a, ki kula da mutanen da zakina mu’amala dasu”. “Kuma da fatan zaki zama mutumiyar kirki a ko’ina kike, bawai sai muna kallonki ba, Allah da ya halicce ki, shima yana kallonki”..
Tana kai nan a zancenta ta mike tare da ficewa a gidan zuciyarta fes bawata damuwa..

NURADEEN POV.

“Tukin motar yake cikin kwanciyar hankali, a hankali yake murza sitiyarin motar”.
Daidai lokacin ya ratso ta cikin layin, da yake akwai gosulo akan hanyar hakan ya karasa shi nutsuwa tare da maida hankalinsa kan hanya.

“Adaidai lokacin ta iso bakin hanyar, cikin nutsuwarta ta fara duba adaidaita din dake wucewa, kowanne yazo cike yake da mutane saide ya wuce ba tare da ta tsayarba.
Cikin nutsuwa ya fara waigawa bayansa tare da hannun damansa, daidai lokacin zuciyarsa tayi wani mungun buguwa da karfi”.

“Idanuwansa suka sauka a saman fuskarta. Dadai lokacin yaji wani abu yana tsarga masa har jinin jikinsa.
llokacin ya sauke glass din motar tare zare tsaddan glass din dake makale a idanuwansa”.

“Ta lura da irin kallon da yake mata hakan yasa duk taji ta tsargu, lokaci guda ta kwadaitu da tabar wurin, idanuwata ta kawar gefe”.
Zuciyarta sam ba dadi. Takai seconds uku a haka daga bisani ta Kara juyowa.

Daidai lokacin taga yana daga mata hannu fuskarsa dauke da murmurshi. wanda shi kansa baisan hakan ta faru ba!
Neman hanyar da zeyi mata magana kawai yake yi, duk da suna kan titi, bai kamata ba’ amma wannan itace kadai damarsa.

“Cikin ta kura da kallon da yake mata kuma gashi suna daf da juna har suna iya juyowa kamshin turaren junansu.
Farin hankicif dake hannuta ta jefa masa, ya sauka dai dai fuskarsa. Badan komai tayi masa hakanba saidan ya dena kallonta”.

“Da sauri ta juya ta barshi a wurin ta fara tafiya cikin sassarfa”.
Shikuma tun lokacin da ta jefeshi bai zare abun daga idanuwansa ba, illah kamshin turarenta da yake shaka a wannan kyalan.

“Zuciyarsa ce tabashi wani kalan yanayi hakan yasa shi dagowa da sauri”.
Can nesa dashi ya hangota tana tafiya cikin yanayi na sauri, saida yaga tana shirin bacewa daga ganinsa, sakamakon tasha kwanar wani karamin layi.
“Ya salam!!”

Ya furta cike dajin tsoron kar ta bace masa da gani gaba daya.
Motarsa yaja tare da saka wani azababban sauri, saida yazo daidai da ita.
Ya dannah burkin motar saida yayi wata kara, wanda yasata juyowa da sauri ta tsaya cak saboda yanda yasha gabanta.

“Zuciyarta ce ta cika da tsoro da fargabar kada ya cutar da ita gashi kuma layin da suke aciki ba kowa..
Ya lura da yanayinta sosai hakan yasashi sakin wani yalwataccen murmurshi saboda yanda ya gano tsananin tsoronta a fili”..

Haka kawai ya karajin ta burgeshi daga bisani ya fara mata magana cikin narkakkiyar muryarsa.
“Sunana Nura Deen!”

“A takure ta d’ago murya k’asa k’asa tace, toni mezan-yi da sunan-ka”
“murmushi ya d’an yi kafin yace, ai nayi tinanin kina safarar sunaye ne”

“Ok to banayi amma zaka iya kaiwa gaba”
“dariya yayi kad’an har saida dimple d’insa ya lotsa”
“Plz Allah kiyi hakuri nasan ba dadi, na tsayar dake a gefen hanya, dama badan kowa na fito ba gidanku nake nema, amma bansamu ba sai kuma Allah ya hadani dake.”.
“Cike da mamaki tace gidan-mu kuma?”
“Eh nan-fa”
“Dan Allah kibani address din gidan ku!”
“kara cika tayi da mamaki ta-kuma nanata tambayar gidan mu kuma?”

“Cike da k’osawa ya d’aga mata gira”

“meyasa ka fito neman gidanmu, alhalin baka da masaniya akai?”

Bata jira amsar da ze bata bata ba, tayi masa kwantance har ya gane gidan. “har ga Allah tayi tsamanin wani abun ne daban zai kaishi gidan”.
Hakan yasa taji karfin gwiwar bashi address din gidansu.
“Dariya yayi saboda yaji dadin kasancewar acikin unguwa daya suke shi da ita”.
Sai da ya bukaci yayi mata lif amma taki hakan yasa ya kyaleta.
*****

Daidai lokacin ta tare adaidaita sahu ta nufi cikin katuwar makarantar tasu, taji dadi sosai saboda haryanzun ba’a shiga class ba.
Bata wuce mintina biyar ba, suka siga lectures.
“Duk da zuciyarta na cike da tinanin wannan gayen amma hakan bai hanata fahimtar darasinta na yau ba.
Awanta biyu a makaranta ta dawo gida saboda yau lecture daya sukeda”.

Duk da yau din ta dawo cikin wata muguwar gajiya, wanka ta farayi kafin ta zauna zaman cin abinci, bata iya gabatar da sallar azahar da yake lokacinta yayi, kafin ta samu dukkan nutsuwarta.
bacci ta danyi na dan wasu lokuta kalilan karfe uku nayi, ta shirya zuwa tilawar karatunta kullum.
Duk da tana tinanin yau gaba daya ta makara, saboda duk iirin makarar fati yau ta rugata tafiya makaranta.

A gaggauce ta fito, kai tsaye gidansu mariya ta wuce, Innar mariya dake zaune a tsakar gidan ne ta amsa mata sallamar, fuskarta cike da fara’a.
Cikin risinawa tace, “Ina wuni innah?”.
“Lafiya lau maryam ya gajiya, ya su maman naki?”.
“Lafiya lau”.
“Mariya fa ko ta tafi itama?”
“A’a tana ciki, shiryawa take, kinsanta itama akwai nuku nuku”..

Dariya tayi tare da wucewa dakin da mariya ke ciki, tana fad’in
“Ayya Inna ai shirin ‘yan-matan ne sai a hankali”

Cikin farin cikin ganinta mariya tace. “Alhamdulillah wllh naki dadin ganin ki yanzu, aini a zatona kin tafi tun dazun”.
“Wllh a raina sai fargabar tafiyar kadaici nakeyi, ga makarar danayi, kuma ga fashin danayi jiya”..
Murmurshi maryam ta danyi tare da cewa “yanzu kam duk ba wannan ba saka hijabin naki mutafi”.
Tana fadin haka ta juya, da sauri mariya ta biyota a baya.
Mariya ce tace innah mun tafi da fatan za’ai mana addu’a.
Allah ubangiji ya kare,
“maryam ki gaida gida”.
Murmurshi tayi tare da cewa “In-sha Allah zasu ji”.
Cikin nutsuwa suke tafiya tare da yin firar da baza’a rasata ba a tsakaninsu.

Da wuri suka isa makarantar batare da kowa ya sani ba, saboda hirar ta musu dadi..
Misalin karfe 5:30 da rabi na la’asar suka fito daga makarantar tafiya suke cikin nutsuwa, a bakin wani katon gida kerarre wanda duk anguwar babu mai kyan shi, hango shi tsaye a jikin katuwar jib din motarsa irin ta dazu, lokaci guda ta gane shi, kai ta kawar saboda ta lura shima ita yake kalloh.

Kai ta sunkuyar saboda har a ranta bata so ya ganeta balle ya tsaidata.
A hankali ya tako daf dasu fuskarsa dauke da murmurshi, ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa, gaskiya na kasance mutum mai matukar sa’a.
Da sauri ta dago, tare dafe kirjinta’ manyan idanuwanta suka gauraya da narkakkun idanuwansa,
la’i Kaine wayace maka Ina nan?.
Dariya yayi tare da Nuna mariya,
Da sauri ta juya ta Kalli mariya.
Idanuwa ta zaro tare da cewa “taya kenan?”. “bamuna tare da ita ba”.
“Toh Idan ba ita ba waye?”.

Dariya mariyan tayi tare da cewa “hakane, nine na Nuna masa”.
Hararta tayi tare da jan hannunta suka tafi. Waiwayo ta kuma yi.
Daidai lokacin ya saki wani kayataccen murmushi, itama murmushin ta sake masa, dan har-ga Allah murmushinsa yaja ra’ayinta.

Mariya dake gefenta tace, “maryam a ina kika samo wannan kyakkyawan gayen?”.
“Da alamu yaja ra’ayinki sosai?”.
Murmushi tayi tare da cewa “a’a bawai yaja ra’ayina bane, kawai mamakin haduwarta tamu nayi!!”
“Dazunfa zan tafi school na hadu dashi. Kuma yace dani gidanmu ya fito nema”.

Ina tsamamnin abokin daya daga cikin yayu nane!!.
Hmm saide abokin ki, maryam wannan gayen da alamu ya kware miki, da dukkan alamu yana da kirki sosai, na dade ina kallonsa cikin wannan unguwar da dukkan alamu bakunta yazo.
Murmushi maryam tayi!!, tare da cewa, “mariya kenan kin fiye rigima, wayasanar dake yana sona?”.
“Hmm maryam kenan, kina da kyau sosai, ba namijin da ze kalleki ya iya dauke idanuwansa akan ki, kowaye ki ka ra’ba sai yaji yana sonki”.

“Saide ayi shakkar fada miki. Hatta mu kanmu kawayen ki mata, kyawun ki na daukar hankalin mu.
marayam kina da kyau na ban mamaki sosai’ shiyasa nake kyautata zaton, tarkon ki yayi kamu”.
Hararta tayi tare da cewa “wallahi mariya halinki sai ke, dan kawai ina da kyau saiki ce a na sona”.

“Hmm idan kyaune ai kema kina da shi, meyasa bazaki tinanin ke yake so ba?”.
Dogon tsaki mariya taja tare da cewa, “No aike ya fara gani, sau nawa muna haduwa dashi a hanya bai taba sanarmin hakan ba?”.

Murmushi Maryam tayi acikin zuciyarta, dan har cikin ranta a iya yau wani d’a namiji ya fara samun wani tsaftacaccen muhalli acikin zuciyarta.
Da wannan sukai sallama da mariya, ita kuma ta wuce gida. da sauri ta dafe kirjinta, Saboda kara hango motarsa da tayi fake a kofar gidansu.
Amma ba kowa a kusa da motar, da sauri ta raba ta wuce,
Batare daya zuge glass din motar ba yake binta da wani kayataccen kalloh.
Da sallama ta shiga cikin gidan, zuciyarta cike da tsoro, allah allah take kar mama tayi mata maganar wancan, Saboda ta riga da tasan halin Abbansu’ da zafi, baya barin kowa yazo wurinsu dalilin da yasa ko sauraran saurayi batayi.
Kusa da Maman ta zauna tare da cewa, “wash!!, wash!”

“Wallahi Mama na gaji yau dinnan”.
Dariya tayi tare da cewa “yanzun aka aiko wai, ana sallama dake, a kofar gida”.
Idanuwa ta zaro tare da cewa, “ni kuma?. kai inah!!, bade ni ba!” Dagowa maman tayi ta kalleta tare da sauke kai Saboda taga tsananin tsoro a fuskar diyarta ta.
“Maryam ki tashi kije, kinsan ba kyau wulakanta dan adam, ya dad’e kuma yana jiranki a kofar gida”.
Ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa “nasani Mama, amma kin-riga kinsan halin Abbah”
Murmushi tayi wanda yasa hasken hakoranta suka bayyana tace, “Abban ku ba abun da zeyi. In-har kuma da gaske yakeyi ni zanyi magana da babanki.”

Batare da ta sake jin wata fargaba ba, ta mike ta nufi inda motarsa take.

By Matar Sadiq

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.2 / 5. Rating: 5

As you found it interesting...

Follow us to see more!

2 thoughts on “Alkawarin Allah 1”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×