Wani ƙatoton zagi ta lailayi ta maka ta na isowa gurin ta ture abincin gaba ɗaya ta na faɗin "Dan uban mutum yaya za'ayi ni na je gida ina haɗo wa mijina abinci amma kafin na dawo sai kawai wata ta zo ta na baka babu dalili. Ceke da mamaki Najib da Kadija ke kallon ta ganin ko sallama babu sai zagi kamar wata jikar maguzawa. Najib ne ya yi ƙarfin halin faɗin "Madam sannu da isowa" Bata ko bi ta kansa ba ta shiga haɗa wa mijinta abinci ta na yi ta hararan Kadija. . .