Skip to content
Part 7 of 21 in the Series Ameera Da Adam by Salis M. Reza

Wani ƙatoton zagi ta lailayi ta maka ta na isowa gurin ta ture abincin gaba ɗaya ta na faɗin “Dan uban mutum yaya za’ayi ni na je gida ina haɗo wa mijina abinci amma kafin na dawo sai kawai wata ta zo ta na baka babu dalili. Ceke da mamaki Najib da Kadija ke kallon ta ganin ko sallama babu sai zagi kamar wata jikar maguzawa. Najib ne ya yi ƙarfin halin faɗin “Madam sannu da isowa” Bata ko bi ta kansa ba ta shiga haɗa wa mijinta abinci ta na yi ta hararan Kadija da har yanzu bata ce komai ba, domin tun kafin su fito Najib ya ja mata kunne a akan kar ta biye mata domin ita bata da lafiya, hakan ne yasa ta zuba mata ido tana ta kallon ikon Allah. Shi dai Adam ya na kwance wuya a ɗaure ko magana idan zaiyi bata fita. Itama Haura ta tsaya shiru kai a sunkuye kamar munafuka. Ganin haka yasa ta gai sar da Najib da Kadija, suma suka amsa ba tare da sun ƙara cewa komai ba, sai dai suna ta kallon yarinyar.

Cike da kuzari ta buɗe kulan abinci har ta na jan tsaki domin taƙi buɗuwa da wuri. Cike da tsan-tsar mamaki take kallon abincin. Ai bata tsaya wata-wata ba ta juya ta cafko Haura ta ƙunduma mata zagi haɗi da mari ta na faɗin. “A gidan uwarki na ce ki dafa min ɗan wake? Ta ya ya honey zai iya cin wannan abun shi da ke ciwon wuya? Haura ta shiga bata haƙuri tana faɗin “Wallahi Anty kece kika ce min kina son ɗan wake shine yasa nayi. Jin haka yasa Ameera ƙara arziƙa ta na cigaba da marinta. Ganin haka yasa Najib saurin ta shi ya na bawa Ameera haƙuri akan ta dai na dukan yarinyar. “Malam babu ruwanka ban saka da kai ba pls ka fita a sabga ta dan Allah na roƙeka!. Ta ƙarasa tana haɗa hannayenta a lamar roƙo, Ameera ta faɗa ba tare da ta ko kalli inda yake ba. Cike da mamaki Kadija ta ce “Kai ma wa ya kaika yarinyar da yanzu kowa yasan bata da hankali ai kawai ka bari ta kashe ta kaga sai burinta ya cika. Tana rufa baki Ameera ta shaƙo mata wuya ta fara faɗin Ubanki da uwarki sune mahaukata ba niba Kadija, wallahi ku fita a idona ina faɗa muku munafukai ƴan gulma kuma wallahi ba zai ci abincin naku ba. Ganin haka yasa Najib ƙwatar matarsa wacce har ta fara ƙaƙarin amai. Sannan ya ce su tashi su tafi ba zai iya da wannan masifar ba. Amma Kadija ta ce bazata tafi tabar yayanta a hannun wannan mahaukaciyar ta kashe mata shi ba. Ana cikin haka likitan da ya masa aikin ya shigo yana tambayar lafiya dai ko. Kafin kowa yayi magana Haura ta yi saurin cewa “Wallahi ba ni bace na soka masa ba itace ta caka masa wuƙa ɗazu wallahi babu ruwana. Ta ƙara sa tana ɓoyewa a bayan Najib saboda tsoron likitan da ta gani sanye da fararan kaya.

Chak ɗakin yayi kowa ya mai da hankalinsa kan Ameera wacce itama taji maganar daga sama. Ita har ga Allah ta manta da cewar ita ta caka masa wuƙar, sannan ita bata yarda cewar itace ba. Kadija ce ta fara magana cikin babbar murya ta na faɗin “Innalillahi wa Innalillahi raji’un! Yanzu dai kowa ya yarda da cewa wannan yarinyar mahaukaciya ce ko? Kuduba ku gani itace ta caka masa wuƙa sannan ta hana a bashi abinci wai a hakan matarsa ce, to wallahi bazamu bari ba, haka kawai ki bijiro da sabon hauka dan kawai kinyi ciki, ko a kanki a ka fara ɗaukar ciki ni banga wani amfanin ki a rayuwar Yaya ba kawai a rabu kowa ya huta da irin wannan abun, ai watarana kawai kashe mana kai zatayi. Kadija ta ƙara sa maganar tana zuwa kusa da Adam wanda ke kwance yana kallo da saurare. Da sunsan abun da yake ji da sun taimaka sunyi shiru, da sunsan abun da ke damun sa da kowa ya ja bakinsa yayi shiru. Najib ne ya fara tambayar Haura a kan tabbatar magar, Haura ta ƙara tabbatar masa, sannan ya kalli Ameera da tun ɗazu ta shiga tunani ya ce “Da gaske kece kika caka masa wuƙa? “Ameera ta kalli Haura sai taga kamar tai mata gwalo, amma da ta kalleta da kyau sai taga kanta a ƙasa a fili ta ce “Wai mai kuke nufi? Saboda yarinya tazo ta ce na caka masa wuƙa shine zaku yarda, to ai ga Adam din ku tambaye shi mana, to ba cake masa nayi ba, faɗuwa mukeyi ni da shi lokacin wuƙar tana hannuna shine ta same shi, amma ni ban caka masa ba. Kuma ita yarinyar da tayi maganar ai bata gurin yaya a kayi tasan nice. Ganin Adam na motsi da kai alamar magana yasa likitan cewa kowa yayi shiru. Ita dai Haura sai bin bayan Najib ta ke yi.

Likitan ya ɗago daga sauraron Adam dake magana a hankali ya ce “To yace dukkanku ku tafi gida a bar iya Najib. Likitan ya faɗa yana kallon Najib wanda yasan shine Najib ɗin domin shine kaɗai na miji a ciki. Cikin tsananin mamaki Ameera take kallon Adam wanda ya kafe ta da ido. Afili ta ce “Hardani za’a tafi a barka? Adam ya gyɗa mata kai. Ai kuwa bata ƙara cewa komai ba ta kalli Haura ta ce kwaso mana kaya. Take Haura ta kwashi kaya suka fita. Sosai ranta ya ɓaci da abun da Adam yayi mata, wai ita Adam yake kora saboda abun da ya faru, ita da yayi wa laifi amma itace mai laifi.

Kallon Haura ta yi ta ce “Ke yarinyar nan a kwai ayar tambaya a kanki! Bari muje gida wallahi yau sai kin sanar dani uban waye ya turoki gidan nan kuma me ya kawo ki. A wani ƙaramin gurin sayar da kaya ta tsaya suka shiga tare ta ce ta tsaɓi kayan guda shida riga da wando sai hijabi guda uku da taƙalma guda uku sai mayafi. Haura ta ce “Ai mu bama saka hijabi” da mamaki Ameera ta ce “Me yasa?

Haura ta sake cewa “Ai mu ba musulmai ba ne addininmu da ban da naku”

Ameera ta ce “To koma meye daga yau zaki koma addininmu na Musulunci in dai kina son zama damu. Sannan ma ku wani addini kuke yi?

“Addinin garin Garuk “

Ameera ta yi shiru tana son tuno a ina ma ta taɓa jin gari mai irin wannan sunan, ganin ta kasa ganowa ne yasa ta ce “A wacce ƙasa?

Haura ta ce “Nigeria mana”

Ameera bata ƙara cewa komai ba har suka iso gurin biyan kuɗin, ta miƙa ATM ɗinta aka cere sannan ta juya suka fara tafiya. Kaman daga sama taji ana kiran sunanta “Anty Meera. Da sauri ta juyo tana kallon mai kiran nata, cikin mamaki take kallon Nana da Nasiru riƙe da hannun juna suma sun fito daga gurin kayan.

Da sauri ta ƙara so tana kallon Haura tana neman ƙarin bayani. Kafin suyi magana Ameera ta fara kallon hannunsu dake cikin na juna ta ce “Nana dan ubanki wannan mijinki ne da har zai riƙe miki hannu? ke kuma gaki ƴar daɗi soyayya kina ganina ma ko a jikinki ko, shi kuma babban ɗan iskan harda ƙara danƙe hannun ko? Ameera ta ƙara sa tana zabga wa Nasiru harara domin ita har ga Allah bata son ƙanwarta da wannan yaron kawai ita baya burgeta.

Nasiru yayi saurin sakin hannunta wanda gaba ɗaya ma shi mantawa yayi. Itama kanta Nana bata ma lura da hannunsu na cikin na juna ba har sai da Ameera ta yi magana.

“Ku dai wallahi kun ji kunya ace kuna ƴaƴan musulmai amma kuma ɗabi’un arna, kalleka kamar mutumin kirki a fuska ashe ƙaton ɗan iska ne, ke kuma wallahi idan kika sake riƙe hannun wani ƙato wallahi sai Abba yaji kuma Nima sai na ci ubanki. Da sauri Nana ta ce “Anty Meera mana” Ta faɗa tana kallon yanda Nasiru ya sauya fuska, ita tasan halin kayanta bashi da haƙuri ga zuciya, kuma yanzu gaba ɗaya suran nasu wata ɗaya ne da kwana biyu.

“Idan kika ƙara magana Allah sai na mareki, banziya mara wayo, an faɗa miki su maza abun yarda ne a irin wannan lokacin, bar ganin wai an kusa auran ku, to idan da gaske ne ya bari ayi auran mana gaba ɗaya. Jin haka yasa Nasiru saurin cewa.

“Na gode Nana dama kin kawo ni nan domin a ci min mutunci ko, to na gani na gode. Nana ta ce “No Nasir please ka tsaya kaji. Tayi maganar kamar tayi kuka. Da mamaki Ameera ta jawo ta ta na faɗin “Amma dai ke anyi lalaceceyar yarinya, a kan wannan ɗan iskan yaran kika son yin kuka, yaran da baya jin kunyar taba ki a cikin mutane. Da ƙarfi Nasiru ya ce “Ƙarya kike munafuka, Karki ƙara kirana da ɗan iska, aure ne ya kawoni gurin ƙanwarki ba iskanci ba idan iskanci na da ba’a zo wannan matakin ba. Kuma wallahi ki san irin maganar da zaki dinga furta min ni ba ƙaninki ba ne, dan ina neman auran ƙanwarki ba shi zai sa na tsaya ina kallo ina cimin mutumci ba.

Cikin masifa da rashin control ɗin kanta Ameera harda hawaye ta isa gaban Nasiru wanda a girme zai iya girman ta amma ta daga hannun ta sauke masa lafiyayen mari ta cigaba da faɗin. “Ƙaryane ba lalata ɗin zaka yi ba? dama ku haka munafukan samarin nan kuke ba kwason gaskiya kuma wallahi sai na faɗa kai ɗin banz…”Bata rufe baki ba taji sauƙar mari mai lafiya daga kumatunta na dama wanda hakan yasa ta tsaya tsit. Kafin kace me itama Nana ta ɗaga hannu ta saukewa Nasiru mari mai kyau. Tsit kowa yayi yayin da Nasiru ke kallon Nana cike da mamaki, itama Ameera Nana take kallo a lamar ba zata ƙara masa ba. Nana ta yi ƙarfin halin cewa “Haba Nasiru ko dan wannan cikin dake jikinta ai ka raga mata ko badan niba Please dan Allah kayi haƙur.

Nasiru ya ce “Nana ni kika mara akan gaskiya ta? Nana ta haɗe hannu tana bashi haƙuri. Nasiru ya ce “Wallahi Nana ko kece autar mata na fasa auran ki, kije ku zauna da yayar taki. Yana faɗa ya bar gurin cikin ɗacin abun da ya faru bai ko tsaya sauraron yanda Nana ke rokon sa ba. Ameera ta ce “Kinga shiga Mota mu tafi manta da shi dama wallahi bai da ce da ke ba, dubeshi ba mara kunya ga shi ɗan iska. Jin haka yasa Nana faɗin “Dalla Malama sakar min hannu, wallahi nayi dana sanin haduwa da ke a nan gurin. Tana faɗa tabi bayan Nasiru da gudu. Ameera ta yi mutuwar tsaye tana kallon Nana. Sai lokacin ta juya bata ga Haura ba, hakan yasa ta ƙara sa motar ta sameta zaune tana kallon waje.

Da sauri Nana ta riƙo hannun Nasiru wanda take bashi haƙuri amma juyowar da zaiyi ya sauke mata mari. Ya ci gaba da cewa “Daga yau karta ƙara nuna tasan shi, kuma zai tura a ƙarɓo masa kayan sa domin ya lura ashe gidan su babu tarbiyya, Allah ma yasa tun kafin ya aura aka nuna masa ya godewa Allah. Nasiru ya juya zai tafi Nana ta ƙara cewa “Wallahi Nasiru Anty Meera bata da matsala bansan mai ya mai data haka. Nasiru ya ce “To ni dai ba zan tsaya ana cimin mutumci a ban zaba, to ko uwar yarinyar da zan aura ta isa ta min wannan cin kashin na barta bare wai yayar ta, kawai kowa ya kama hanyar sa Allah yasa haɗa kowa da masu irin halin gidan su. Nana ta ce “Amin Nasiru! Na ce Amin , idan ka haifu a cikin uwarka yanzu kazo muje ka kwashe kayan ka ba sai gobe ba, in sha Allah daga yau bazaka ƙara ganina bama balle har muyi magana ka je nima na fasa auran naka. Tana faɗa ta juya zata tafi amma Nasiru da maganar da ta faɗa ya ɓata masa rai ya janyota sai gata a jikinsa wanda ita kuma ta sauke masa mari tana janye jikin ta, shima kafin ta anka ya mayar mata da marin , nan take suka fara faɗa dama sun saba.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Ameera Da Adam 6Ameera Da Adam 8 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×