Skip to content
Part 6 of 20 in the Series Ameera Da Adam by Salis M. Reza

Da sauri Adam ya riƙe Amera da ke ƙoƙarin yin kisa. “Lafiya kike kuwa Ameera? Ba ki da hankali ne idan kika kashe musu yarinya fa, daga kawo yarinya har zaki naimi hallaka ta.

Adam ya faɗa ya na ɗago Haura dake durƙushe ta na kuka. Ita kuwa Ameera dama kaɗan ta ke jira, kafin Adam ya ƙara sa har ta yi tsalle ta shiga tsakaninsu da Haura. Cike da gadara da nuna isa ta ce “Honey wallahi wannan yarinyar bazata zauna a cikin gidannan ba domin ban yarda da ita ba. Cike da mamaki ya ce “Me ya faru? Ameera ta fara magana cikin ɗacin rai da takaici ta na jin yau sai ta nakasa wannan yarinyar. “Daga cewa ta dafa min indomin ɗazu wallahi ko minti uku ba’ayi ba wai har ta dafa, sannan yanzu na ce ta karanta min littafin da na siya ɗazu wai daga bata waya sai rubutun ya koma wani yare da ban? Ameera ta ƙara sa maganar da wata iriyar murya.

Cike da tsoro Adam ya ce “Ina indomin da littafin? Sai a lokacin suka kalli gurin da kwanon abincin ya ke, amma wayan babu abincin a cikin kwanan. Cike da sabon tashin hankali Amera ta kalli Haura ta kalli kwanan abinci ganin da gaske babu komai a ciki, ita dai tasan cokali uku tayi kawai a abincin. “Ina abincin ya ke? Ameera ta tambayi Haura cike da dakiwa alamun babu wasa. Cikin muryar kuka Haura ta ce “Ba ke ce kika cin ye ba ɗazu.

Take Ameera ta lailayo wani ƙatoton zagi ta makawa Haura haɗi da faɗin “Ubanki ne ya ce miki nine na cinye? Ina ce yanzu kenan na fara cin abincin kika mayar min da littafin wani abu da ban, shine yanzu zaki ce ni ce na cinye.

“Kunga yanzu dai duk ku dagata” Adam ya faɗa bayan ya gama jin duk abinda kowa ya ce. Sosai ya ke ta nazarin yarinyar ganin tana yin komai a nutse ne yasa bai ta da hankalinsa ba. “Yanzu ina wayar da rubutun ya koma wani iri ɗin? Da sauri Ameera ta miƙa masa wayar ta na faɗin “Wallahi ko rubutun aljannu ma iyaka kenan. Adam na ƙarɓa ya ce “To ai ga shi rubutun Hausa ne ba na wani abun ba. Ya faɗa yana miƙa mata wayar. Cike da tsoro ta ƙarɓa tana kallon komai na Hausa a cikin littafin. Adam ya ce “Duk kinzo kin tashi hankalin mutane bayan a she kece ma baki duba ba da kyau ba, ni wallahi na rasa gane miki Honey kullum sai sauyawa kike yi kamar wata wa hainiya, please dan Allah ki bari ku zauna lafiya da wannan rayinyar bata da wata matsala.

Adam na gama faɗa ya kama hannun Haura ya tafi da ita ɗakinta ya na faɗa mata cewar sai ta yi haƙuri da Ameera wannan cikin ne duk ya mai data haka, da zarar ta sauƙa in sha Allah komai zai dawo daidai. Ita dai Haura sai sun kuyar da kai take yi ta na sauraron sa har suka iso ciki ɗakin nata. Kallonta ya yi da kyau daga ƙasa har sama yana tuno ganin da yayi mata tsirara. “Gobe idan Allah ya kaimu za’a sayo miki kayan sawa kin ji? Ba tare da tayi magana ba ta ɗaga masa kai. Juyawa ya yi ya bar ɗakin ya nufi gurin Ameera.

Tun daga nesa ya hango ta ta na zazzagawa a cikin palon ta je nan ta dawo nan , kallo ɗaya ya mata ya nufi ɗakinsa bai ko bi ta kantaba. Ya na shiga ya shiga cire kayan jikinsa ya na cigaba da tunanin lamarin Ameera da Haura. Sai kuma ya ɗan saki murmushi yana jin anya kuwa Ameera bata fara ganin biyu-biyu ba kuwa. Ya na cikin wankan yaji an banko ƙofar da ƙarfi kamar za’a ɓalla ta. Tsaye yayi yana kallon ta itama ta na kallonsa cikin ido, tsabar masifa da ke cikinta har wani jaa fuskarta ta yi, shi kansa Adam sai da ya tsorata da ganin fuskar tata. Cikin tsawa da ɗaga murya Ameera ta ce “A ina ka samo wannan yarinyar!? Adam ya haɗiye wani yawu haɗe da ruwa a lokaci ɗaya sai ji kake maƙot. Tsabar rike cewa ma ya kasa cewa komai jin yayi shiru ne yasa ta sake daka masa wata tsawar kamar wata uwar sa. “Na ce a ina ka samo wannan tsinaninyar yarinyar da har ina magana zaka riƙe hannunta ku tafi ka barni a tsaye? Ta ƙara sa tana nuna masa wuƙar da ta ɓoye a bayanta tun ɗazu. Adam ya ce.

“Am am kinga honey dan Allah a jiye wuƙar muyi magana please… Kafin ya ƙara sa ta kai masa yanka yayi saurin sun kuyawa yana zaro ido ganin fa da gaske ta ke yi. “Honey please tsaya kiji wallahi ba abun da kike tunani ba”…Nan ma bai ƙara sa ba ta ƙara kai masa wani yankan ta na kuka. Ganin haka yasa Adam saurin riƙe hannunta mai wuƙar yana jawo ta jikin sa. Ita kuwa Ameera ganin haka yasa ta fara ƙoƙarin ƙwacewa tana so taga ta luma masa yasan da gaske take. Da ƙarfi Adam yake so ya ƙwace wuƙar amma saboda ba riƙon wasa tai masa ba yasa ya kasa ƙwacewa kuma idan ya dage wani zaiji ciwo a cikin su, hakan yasa ya jawo ta jikin ƙofar ya buɗe yayi waje a guje, itama tabi bayan sa cikin gudu.

Bai ma san ina ya nufa ba a cikin gidan shine naiman mafita yake yi, tsabar gudu har yana zamewa a palon ya faɗi, hakan ya ba Ameera damar kamashi, tazo kusa dashi itama ta zame sai kawai ta nifo kansa kuma wuƙar tana hannunta kuma bata nufi ko ina ba sai cikinsa kasancewar ta reƙe wuƙar a tsaye ne tana gudu. Ai kuwa tana faɗa wa sai a kan sa wuƙar bata tsaya ko ina ba sai daidai wuyan Adam Kasan cewar yayi ƙoƙarin kwacewa sai bata sauƙa a cikin ba sai wuya, kafin ka ce me sai jini ya fara tsalle yana malale palon. Cikin sakan ɗaya Ameera ta dawo hankalinta kallon yadda jine ke fitowa daga jikin mijin nata tayi ga kuma babu komai a jikinsa tsirara ya ke. Da sauri ta nufi ɗaki ta ɗauko masa wanda wanda tsabar sauri da ruɗewa ma bata san sket ɗinta ta ɗauko ba. Ta na isowa gurin taga Haura a gurin tana kuka ta ɗora hannunta a kan gurin ciwon kuma jinin ya daina fita.

Da ƙarfi ta chakumeta ta falla mata wasu lafiyayyun maruka guda uku kyawawa sannan ta ce “Ba kya ganin ko kaya babu a jikin sa ne da zaki zo ki tsaya a kansa haka dan uwarki. Ganin Adam na ƙaƙarin mutuwa ne yasa Ameera saurin saka masa sket ɗin, sai a lokacin ta lura a she wani baƙin sket ɗinta ne ma, ai kuwa bata ko tsaya sauya masa ba ta saka masa haka sai kuma ta kalli Haura dake tsaye riƙe da kunci, ta ce “Me kika masa jinin ya tsaya? Haura dai sai bin ta da kallo take yi. “Ba dake nake magana bane? Ameera ta sake faɗa cikin ihuu!

“Addu’a nai masa” Haura ta faɗa cikin kuka. Jin haka yasa Ameera cewa taje waje ta kira mai gadi. Ai kuwa take mai gadi ya zo wanda shi kaɗai ya kama Adam ya kaishi mota sannan Amera ta ja mutar izuwa asibiti duka bar Baba mai gadi da jimami da mamaki.

Suna tafiya Haura ta shiga gyara gidan abisa umarnin da Ameera ta bata, sosai ta wanke gurin da jinin ya ɓata, sannan sai yanzu ta shiga ko ina dake cikin gidan, ta tsaya ta ƙarewa komai na gidan kallo tana mamakin duk abinda ta gani. Sosai ta baiwa idanunta hakkinsa wajen kallon sabbin abubuwan da bata taɓa gani ba. Tana cikin haka idanunta ya hango wani hoto a palon, da sauri ta ɗauko ta na kallon mutanen cikin hoton. Adam ne da Ameera sun sha kayan ƴen booll riga da wando koraye sun yi kyau sosai wanda Adam ke riƙe da hannun Ameera suna sakarwa kan su murmushi, kallo ɗaya za kai musu kasan suna cikin farin ciki, take yanayin da ta gan shi ɗazu ya dawo mata, sai kawai yanzu ma take kallonsa kamar babu kaya a jikinsa, take ta kai hannu ta na shafa daidai gurin a hoton . Ta daɗe a haka kafin ta mayar da hoton ta koma ɗaki tayi zamanta tana jiran tsammanin warabbika.

Cikin ikon Allah a ka wanke masa gurin a kai masa ƙaton bandeji wanda hakan yasa dole sai a asibitin suka kwana daga ita har shi ɗin. Washegari da sassafe ta nufo gida domin ɗaukar musu abinci. Ta na shiga ta fara kiran Haura. Da sauri Haura ta fito daga cikin ɗakinta ta na amsawa. Kallonta Ameera ta yi ta ce “Zan shiga wanka yanzu ki tabbatar kafin na fito kin gama haɗa min komai na abinci? Haura ta amsa da to.

A gurguje Amera ta shirya cikin wata ɗinkin doguwar rika Wanda kallo ɗaya za kai mata kaga hango ɗan ƙaramin cikin nan nata ya leƙo kai, mayafi mai kalan rigar ta yafa sannan ta sauƙo cikin sassarfa. Ta na zuwa ta tarar da Haura ta gama komai tana tsaye tana jiranta.

“Me keka dafa? Ameera ta tambaya tana kallon kulolin abincin.

“Abun da kika fi so na dafa” Haura ta faɗa da murmushi!

Cikin mamaki Ameeran ta ce “Ni yaushe na faɗa miki kalan abincin da nafi so? Sannan ma wani abinci ne? Ameera ta faɗa cike da tsan-tsar mamaki.

“Kin manta jiya kin faɗa min” Ta faɗa tana dariya a karo na farko tun da tazo gidan. Kafin Ameera ta sake cewa Kamai Haura ta ce “Anty ya jikin nasa?

Sai a lokacin ma Ameera ta tuno da abun da ta kwana da shi a ranta. Ta ce “Jiya kin kalli jikin sa ne lokacin da yake tsirara? Ameera ta faɗa domin tun jiya abun ya tsaya mata a rai, tana da kishin mijinta, har ƙara ma ace ita Haura ta gani tsirara ba Adam ba. Ita kuwa Haura da bata kawo hakan komai ba cikin ƴar dariya da take yi tun ɗazu ta ce “Allasarki koba jiya da babu ko kaya a jikinsa ba, nayi mamakin ganin zaki kashi shi ko ba kyau son sa ne? Hauran ta faɗa har yanzu tana dariya.

Da sauri Ameera ta ɗago kai tana kallonta. Ta ce “Kenan kinga jikinsa?

Haura ta ce “To mutumin da babu komai a ji kinsa ai dole a ga jikin sa”

“Gabansa nake magana kin gani? Ameera ta faɗa tana aiyana abun da zata mata idan tace ta gani domin wallahi tazo iya wuya.

Sai yanzu Haura ta gane nufin ta, lokaci ɗaya ta tsayar da dariya da ta keyi ta sunkuyar da kai ta ce “A’a ban ga komai ba” Ameera ta sauke a jiyar zuciya ta ce fine for me and you. Sai kuma ta ce “Ɗauko abincin ki biyo ni mota da shi. Tana faɗa ta wuce riƙe da jaka a hannu.

Bayan Haura ta gama saka kayan a mota ne zata koma gida amma Ameera ta ce “Shigo motar mu tafi tare. Babu musu ta buɗe mai zaman banza ta zaune suka ɗauki hanyar asibiti.Sun zo daidai gurin da mamarta suke zama bara ne ta hango mamar tata cikin ƴan uwansu mabarata. Kaman tayi wa Ameeran magana amma tasan bama zata iya ba. Daidai lokacin taji Ameera ta taka wani aban burki tana sakin ƙara. Ji kake ƙuuu! Da sauri ta fito daga cikin motar ta nufo gurin da ta kusa bige yaran mai sayar da ruwa da su biskit da abubuwan sha. Ta na isowa gurin ta kamo yaran ta sauke masa mari wanda hakan yasa kowa dake gurin ƙarasowa domin tun lokacin da ta taka burki hankalin kowa ya dawo gurin su. Haura kuwa tana ganin haka ta fita tayi gurin mamarta.

“Haba baiwar Allah me ye kuma na duka tun da Allah ya kiyaye ai sai dai muyi godiya Allah ya ƙara kiyaye wa ba sai kin dake shi ba. Ameera da yaron nan ya gama tsoratata ganin yadda ya shiga gaban motar ta har sai da hajjin cikinta ya kaɗa tsabar tsoro. “An dake shi ɗin, na ce an dake shi ɗin, yanzu da na bige shi da kune zaku fara zagina kuna cewa ban iya tuƙi ba, amma yanzu saboda na dake shi zaka wani zo kana maganar banza. “Ayi hakuri dai Hajiya yaro yayi kuskure. Ameera ta ci gaba da zagin yaron kamar zata ari baki, an bata haƙuri taƙi tafiya sai wani ya ce “Wai ke sai ka ce ba musulma ba fisabililahi! An ce kiyi haƙuri an haɗa ki da Allah amma kamar wacce ake ƙara tunzurawa, ko dai ba’a san Tauhidi ba ne? Mutumin ya faɗa yana mai jin haushin yanda ake ta fata haƙuri taƙi haƙura.

Ai kuwa ta yi caraf ta ce “Kafura mara sanin Tauhidi tana gida zaman Allah bamu, idan Kafura kake nema ka je gurinta, wawa mahaukaci, an min laifi ba zan fito na faɗa ba.. kafin ta rufe baki mutumin ya ce “Wallahi kin ci darajar wannan cikin dake jikinki amma da nasa yara sun lakaɗa miki na jaka anan banza mara tunanin da haƙuri, yana faɗa ya bar gurin dalilin mutane dake ta bashi haƙuri. Haka Ameera ta dinga zagin mutumin har ta shiga mota, daidai lokacin Haura itama ta dawo, ba tare da ta ce mata komai ba ta ja motar suka bar .

Koda suka isa asibitin cikin fushi ta ce da Haura ta ɗauko abincin ta biyo bayan ta. Ta na tura ƙofar palon taga Kadija da Najib zaune a kusa da shi Kadija na ba shi abinci a hankali. Ko sallama bata tsaya yi ba tsabar masifa da fushin da ta kwaso, sosai ranta yayi mugu-mugun ɓaci, ita ta tafi gida domin kawo masa abinci shine har wasu zasu kawo masa ya ci wato ita ta gaza ko…?

<< Ameera Da Adam 5Ameera Da Adam 7 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×