Skip to content
Part 44 of 67 in the Series Aminaina Ko Ita? by Rasheedat Usman

Gagara magana yayi sai idanunsa da sukayi jajur zuciyarsa tamkar zata faso ƙirjinsa ta fito, wani takaici da haushin Al’ameen yake ji tare da danasanin haɗa Al’ameen da Nafeesa wannan wacce irin mummunan ƙaddara ce take neman yiwa rayuwarsa ƙawanya lallai rayuwa cike take da ƙalubale, a matuƙar fusace ya juya ya shige cikin motar sa, yaja motar da ƙarfi, tuƙi kawai yake ba tare da yana kallon gabansa ba, babu abinda suke amsa kuwwa a kunnen sa sai maganganun Nafeesa idanunsa ya runtse yana tuno maganar Al’ameen a duk sanda ya kawo masa maganar Nafeesa ƙoƙarin kauda maganar yake yana nuna masa cewa lallai ya rabu da Nafeesa, ashe so yake ya rabu da ita shi ya aureta.

Tabbas Al’ameen ya masa butulci ya masa MUMMUNAR CIN AMANA idanunsa ya runtse, yana cigaba da tuƙi cikin rashin cikakkiyar nutsuwa fasa nufar Companyn yayi ya nufi gida idanunsa na zubar da hawaye jefi jefi.

Can kuwa Al’ameen ya kusa isa Companyn ya tuno da takaddar daya saka hanu wanda za’a fitar da waken suya, hakanne ya sashi yin ribas ya juyo gida domin ya ɗauka, Haidar shigowarsa cikin Estate ya hango motar Al’ameen a fake, burki yaci tare da fitowa a fusace fuskarsa tayi jajur abunka da farin mutum, ya nufi part ɗin su Al’ameen ko motar tasa bai rufe ba, Rufaida da itama ta fito zata shiga wajen Maimu ne taga Haidar fusace yabar mota a buɗe ya bata mamaki ƙarasawa tayi ta rufe masa motar tare da bin bayansa da sauri, tun daga cikin falon ya ke ƙwalawa Al’ameen kira babu ko Sallama cikin ɗagowa da ƙarfin gaske babu abinda yake amo acikin falon sai muryar sa, cike da tsoro kowa ya fito harta Inna Jumma, Al’ameen dake cikin bedroom ɗinsa ya sunkuya zai ɗauki takadda yaji sautin kiran da Haidar ke masa a fusace, cikin karkarwar amo, fasa ɗaukar takaddar yayi cikin tsinkewar zuciya da tsoron meke faruwa da Al’ameen ya fito cikin sauri domin kuwa ko a cikin zuciyarsa bai kawo maganar Nafeesa ba ce.

Ganin Al’ameen ya na sauƙowa daga step yasa Haidar nufansa gadan-gadan yana huci tare da cin kwalar Al’ameen, zaro idanunsa Al’ameen yayi cike da munguwar mamaki Inna Jumma ma da sauri ta nufosu bakinta sake cike da mamakin meke faruwa abinda basu taɓa gani ba a cikin gidan, Aunty Amarya ma haka take a gareta domin kuwa wannan baƙon abune da ya girgiza kowa Rufaida bakinta ta rufe cike da tsoro tana zaro idanunta, Al’ameen yafi kowa mamaki cikin nauyin murya yace.

“Haidar meye haka me yake damunka kwalata fa kaci.?”

“Naci kwalarka Al’ameen, saura kuma duka domin banga amfanin mutum irinka ba mungu Al’ameen ashe dama kai butulu ne ɗan akuya ban sani ba, wanda baka san mutuncin aminta ba, duk Abotar dake tsakanin mu da shaƙuwa ashe zaka iya cin amanta, lallai ka cika ɗan kunama wanda ya kasa gadon mutunci, Al’ameen idan har kai cikakken mutum ne mai amana bazaka taɓa neman budurwata ba,ko ba Aminta a tsakanin mu jini ɗaya yana gudu a jikin mu, karka manta da naka Mahaifin da nawa, Daddy da Papa uwa ɗaya uba ɗaya ne suka kawo su duniya, amma saboda zuciyarka dabbar zuciyace makahuwa ka rasa wa zaka nema duk matan da suke cikin garin nan sai wacce nake so na Aura wani irin cin amana ne, wannan, anya kuwa kai mutum ne kana son ABLAH kuma kana son NAFEESA zaka jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya saboda kana tunanin ka isa kana da isasshun ƙuɗaɗe a hanunka, lallai ka sani yadda ka tarwatsa min rayuwata na rantse da Allah kaima saina tarwatsa maka taka rayuwar, ka jira ka gani nan da awa uku sai kayi kuka kamar yadda ka sani nayi, na…”

Inna Jumma cike da ɓacin rai da ruɗani cikin mungun tashin hankali ta dakawa Haidar tsawa.

“Ya isa haka Aliyu! Wani irin mummunar Magana kake faɗa masa, akan mace ka haukace ne ko kayi shaye shaye ne, AMININKA ne fa kuma ɗan uwanka wanda baka da tamkar sa, meyasa baza ka tsaya kayi bincike ba kake ƙoƙarin yanke masa hukunci, dan kawai ta faɗa maka son ranta, waima wannan wacce shaiɗaniya ce ja’ira take neman shiga tsakanin ku, waye…”

Shima a fusace ya tari numfashin Inna Jumma Wanda sai da yasa Maimu da Rufaida suka razana, cikin tsawa da kuma zafin rai Haidar yace.

“Ya isa haka inna Jumma! Nafeesa ba shaiɗaniya bace Al’ameen shine shaiɗani , babu ruwanki cikin wannan maganar Inna Jumma ki barni na faɗa masa abinda ke cikin raina nayi nadama wallahi da kuma mungun danasanin kasancewar ka ɗan uwana kuma wai aminina wanda yasan komai nawa na rayuwa wanda na basa yarda ta ashe shine zai iya aibata Rayuwata ya ɓata sunana a duniya ya dangantani da mazinaci kuma mashayi saboda kawai ya samu cikar muradinsa na son zuciyarsa, tir da halinka, da baka biyo ta wannan hanyar ba da ka min magana kace min kana sonta da zan bar maka ita koda kuwa rabuwa da ita zai zamo min mutuwa tace, Saboda kafi ƙarfin komai a wajena zan sadaukar maka da rayuwata, amma saboda kai butulu ne ɗan akuya sai ka biyo ta hanyar tarwatsa min mutunci! Karki ƙara kiransa da sunan ɗan uwana Inna Jumma, domin ya zubar da Amintar dake tsakanin mu, da ƴan uwantaka yayi watsi dasu gami da fatali, yayi katangar ƙarfe ya kuma saka mata wuta mai ruruwar gaske, zaifi idan kika kirasa da sunan butulu kuma maci Amana.”

Yayi maganar cikin huci yana sakin kwalar Al’ameen tare da turasa baya, Al’ameen gagara magana yayi sai riƙe ƙarfen step ɗin yayi, sosai idanunsa sukayi jajur sai yanzu ya fahimci fushin Haidar a kansa, Tabbas yasan Nafeesa makira ce zata iya aikata komai yasan dole akwai mummunan abinda ta sanar da Haidar dama ya sani duk sanda Haidar yasan wannan maganar ba lallai bane ya fahimce sa saboda soyayya ta makantar dashi har take sashi yin abinda ba dai-dai ba, amma Tabbas da yasan ko wacece Nafeesa, dole ya ƙyamaceta komai son da yake mata, Aunty Amarya ce zatayi magana Al’ameen yayi saurin ɗaga mata hanu tare da girgiza mata kai cikin mungun ɓacin rai ya fara magana.

“Makahuwar zuciyarka ne tasa kake zargina har kake kirana da waɗannan mugayen sunayen da sam bai dace da rayuwata ba, Haidar ko cikin ban taɓa tsammanin zaka furta min munanan kalamai ba saboda mace,, amma ka sani ni ban kasance koda ɓangare ɗaya daga cikin sunayen da ka kirani dasu ba, Haidar ka dawo hankalinka ka nutsu kayi nazari da hallayata hakan zai baka damar gyara kalamanka a kaina domin kuwa kana kan kuskure ka farga tun kafin lokaci ya ƙure maka, a yanzu na maka uzuri saboda naga alamun kana cikin haukar Soyayya, amma fa ka sani karka kaini ƙarshe, har kasa na tunzura, domin kalamanka suna yawa kuma sunyi muni da yawa, idan har na tunzura maganar da zan faɗa maka sai tafi wacce kai ka faɗa min ciwo, nayi baƙin ciki da akace duk tsawon rayuwar mu da yarintar mu baka fahimci abinda zan iya aikatawa da wanda bazan iya ba, a tunanina kai mai bada shaida a kaina ne ashe abun ba haka bane, kai kasan wata Nafeesa har kake daga jijiyoyin wuya a kanta, ni da ka ganni nafi ƙarfin wannan yarinyar.

Yana gama faɗin haka ya raɓa gefen Haidar tare da ficewa da sauri idanunsa na cikowa da hawaye, domin kuwa baya buƙatar amsar da Haidar zai mayar masa, Inna Jumma duban Haidar take tayi dake famar huci tamkar maciji kububuwa ya kasa maida martani domin kuwa wanda zai maidawan ya fice.

“Wai waye ne wannan Nafeesan da take neman tarwatsa zumuncin ku, wacece ita wannan shaiɗaniyar lallai zan ɗau mataki a kanku, yanzu kai abinda kayi ka kyauta, Aminu ba ɗan uwanka bane baka san abinda zaiyi da wanda bazaiyi ba, na tabbata Aminu bazai aikata wannan laifin da kake tuhumar sa dashi ba.?”

Dafe kansa Haidar yayi da yake masa nauyi, idanunsa ya ɗago tare da duban Inna Jumma, Aunty Amarya ce tazo ta dafa kafaɗarta tare da cewa.

“Haidar hankalina ya tashi banji daɗin abinda ya Faru ba, meyasa bazaka fahimci ɗan uwanka ba, duk mutum sai Allah bance Al’ameen bazai aikata ba, amma yana da kyau ka fara bincike tukunna kafin…”

Inna Jumma ce ta katse ta da cewa.

“Bama zai aikata ba, bare har yayi wani bincike, ita dai yarinyar itace makira kuma zan nemota naci ubanta ko wacece ita bata isa ɓata min zumuncin ahalina ba.”

Miƙewa tsaye Haidar yayi tare da runtse idanunsa sosai maganganun Inna Jumma suke ƙara masa suka a zuciyarsa domin bayan Al’ameen take bi ƙiriƙiri bayan kuma duk wata hujja ta tabbata ganan hoton sa na tozarci da Al’ameen ya haɗa ya turawa Nafeesa amma wai a haka gani take bazai aikata ba, babu wata hujjar da zai nema bayan wacce yake da ita, cike da huci ya fice daga part ɗin ba tare daya tanka ba domin kuwa idan yace zaiyi Magana to Tabbas bazai faɗawa Inna Jumma mai daɗi ba, Aunty Amarya murmushi ta saka cike da jin dadi Domin kuwa ta juma tana neman hanyar da zai kawo rabuwar kai tsakanin wannan ahalin lallai wannan yarinyar koma wacece ta burgeta, cikin zuciyarta ta furta (Wannan babbar dama ce da nake da ita wacce zanyi amfani wajen ƙara dagula Ahalin ku ashe akwai Soyayyar tsakanin sa da Nafeesa shine ya ɓoye min yace min babu to me yake nufi dani, dama nayi hasashen akwai ta, koma meye yanzu dai gashi ta fito kuma watan baƙin cikin ku ya kama, a tsakanin wannan fitinar da hankalin ku baya jikinku zan kammala aiki na, maganganun Haidar ta maimaita. “Na rantse da Allah kaima sai na tarwatsa maka rayuwarka, ka jira ka gani nan da awa Uku sai kayi kuka kamar yadda nayi.” To ga dai ita Ablar tana can zata shiga tarkon mu nan da awa ukun da ka ambata kuma za’a lalata mata rayuwa Tabbas idan labari ya zowa Al’ameen zaiyi baƙin ciki harma da kukan, zai ɗaura alhakin hakan a kan HAIDAR saboda ya masa Furuci daga nan zai fusata abubuwa zasu daɗa ɓaci.) Sakin murmushi tayi tare da juyowa tana haɗa fuska cikin fuskar tausayi da jimami tacewa Inna Jumma.

“Inna Wannan lamarin ya bani tsoro wallahi, to amma inna haka zamu zuba idanu bazamu ɗauki mataki ba, saboda karmu bari kuma abun ya ƙara ɓaci.”

Rufaida cike da tashin hankali ta kama hanun Maimu tana kallon ta ita kanta Maimu hankalinta yayi mungun tashi, numfashi Inna Jumma ta saki tare da cewa.

“Zan ɗau mataki a kai karki damu insha Allah abun bazaiyi tsamari ba.”

Tayi Maganar tana juyawa tabar wajen itama Aunty Amarya haurawa tayi ya saura daga Maimu sai Rufaida suma waje suka samu suka zauna cikin sanyin jiki.

Cike da farin ciki ta ƙarisa cikin school ɗin a capteria ta samu Jamila tana cin abinci kujera ta jawo ta zauna tana dariya Jamila dubanta tayi tare da cewa.

“Wannan fara’ar fa kamar wacce taci babban kyauta.”

Dariya Nafeesa tasa tare da karkacewa ta hau bawa jamila labarin abinda ta yiwa Haidar yau, wani irin firgita Jamila tayi tare da ture plet ɗin abincin gefe tana zaro idanunta tare da fe kirji ta furta.

“What! Nafeesa abinda kika aikata kenan kin san me kikayi kuwa, kai innalillahi wa’inna ilaihirraji’un! Shikenan kin ɓata mana aiki, kin lalata komai wayace miki kiyi wannan aikin mtsss.”

Tayi Maganar tana jan tsuka tare da zama ta dafe kanta cike da mamaki Nafeesa ta dubi Jamila tace.

“Wani irin na lalata komai, bayan kuma kece kika bani wannan shawarar ko kin manta ne.”

“Ban manta ba, amma nace miki ki faɗawa Haidar ina ce miki nayi ki yiwa Al’ameen barazana tukunna, kafin mu kai ga Haidar ɗin, amma tsabar rashin haƙurinki shine zakiyi gaggawa, nasan yanzu haka suna can sun kwaɓa tsiya kuma kin san me zai faru iyayensa zasuyi ƙoƙarin jin tsanarki a ransu shiyasa na ce miki kin lalata komai.”

Shuru Nafeesa tayi, sai kuma ta saki murmushi tare da cewa.

“Jamila ina ruwana da iyayensu, sai me idan sun tsaneni nifa Al’ameen ne damuwata kuma kin sani kema dole zai aureni ko da izinin iyayensa ko babu.”

Murmushi Jamila ta saki tare da cewa.

“Na sani amma mu samu Soyayyar tasu ma wata dama ce amma babu damuwa itama zamu samu domin kuwa hanya bata taɓa ɓace mana, mu ƙarisa class dama ke nake jira.”

Murmushi tayi tare da ɗaukar bag ɗinta suka shige. 

Misalin ƙarfe biyu na rana suka gama lectures tana tsaye tana jiran isa driver shuru shuru bata gansa ba har kusan biyu da rabi, hakanne ya sata fitar da tsammanin zai zaizo, fita tayi domin neman abun hawa kawai ta dawo gida, ai kuwa tsayuwar adaidaita sahu ta gani a gabanta duban wanda ke cikin adaidaitan tayi tare da kaucewa zata shige, taji muryar sa yana ce mata.

“Daga gidan AMBASSADOR AHMAD GIWA aka aiko ni nazo na kaiki gida, Isa baya jin daɗi shine Haidar yace nazo na ɗaukeki.”

Duban mutumin Ablah tayi zuciyarta duk bata yarda dashi ba tace.

“Yaya Haidar shi yace kazo ka ɗaukeni, a ina ka gansa harya aiko ka?”

Murmushi mutumin yayi tare da cewa.

“A Companyn su ina musu aiki a cikin Companyn su, kinga card ɗina ma na Companyn.”

Amsa Ablah tayi ta karanta Tabbas card ɗin Companyn su Al’ameen ne numfashi ta saki tare da basa card ɗinsa ta shiga cikin adaidaitan…

INTERMISSION

Tsakiyar labari

END OF BOOK ONE

Wannan shine ƙarshen kashi na ɗaya zamu haɗu daku a Littafi na biyo domin jin ya zata kasance.

Akwai tambayoyi masu tarin yawa a cikin wannan labarin mai cike da sarƙaƙiya.

Haidar yayi iƙirarin cewa sai ya tarwatsawa Al’ameen shima rayuwarsa cikin awa uku me yake nufi da hakan wani abu ya shiryawa Al’ameen?

Itama Aunty Amarya tayi iƙrarin tarwatsa rayuwar Ablah shin tsakanin Aunty Amarya da Haidar waye ya saka a ɗauki Nafeesa a daidaita sahu, da gaske Haidar ne ko shirin Aunty Amarya ne.?

Shin za’a samu masalaha cikin sauƙi tsakanin Al’ameen da Haidar kuwa?

Nafeesa ko zataci nasarar samun Al’ameen?

 Shin burin Aunty Amarya zai cika kuwa?

Ya rayuwar Ablah zata kasance shin anya kuwa zata Auri Al’ameen?

Ya zata kasance tsakanin Rufaida da Haidar anya kuwa zai amince da maganar iyayensa domin kasancewa da Rufaida a cikin rayuwarsa?

Babban abun tambayar Papa na shirin haɗa Al’ameen da ƴar uwarsa Madina, shin me zai faru wa Al’ameen zai Aure Ablah ko Nafeesa ko Madina.?

Amsoshin waɗannan tambayoyin naku suna sarƙafe cikin littafi na biyu ku biyo ni sannu domin warware wannan zaren.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Aminaina Ko Ita 44Aminaina Ko Ita 46 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×