Skip to content
Part 42 of 67 in the Series Aminaina Ko Ita? by Rasheedat Usman

“Hmmm! Yaya Haidar kenan, ashe matsala ce ni a rayuwarka, bansan ƙiyayyar ta kai haka ba, a kaf dangi ina mutumtaka fiye da kowa kuma badan saboda ina sonka bane Saboda gani nake kai mutumin ƙwarai ne mai tausayin na ƙasa dashi gani nake kafi kowa kirki, hmmm!

Ashe kuskuren fahimta nayi, Tabbas ina sonka amma bazanyi amfani da son da nake maka ba dan ka zauna dani dole ba. A aure ana buƙatar kulawa da cikakkiyar nutsuwa to meye ribata idan har ka aure ni na gagara samun nutsuwa, a halin da ake ciki Allah shine shaidata sannan Maimu shaidata na fidda tsammani da auren ka har na bawa zuciyata haƙuri saboda na fahimci baka buƙatata a cikin rayuwarka, duk da ina sonka amma haka na danne saboda nasan ƙaddara kuma ina musulma dole zan rungumeta bani da burin haɗaka faɗa da mahaifiyarka, ban taɓa furtawa Momma ina sonka ba, ra’ayinta yasan taji tanason haɗa mu aure, Kuma nayi ƙoƙarin dakatar da ita saboda bana son muyi auren tirsasawa, sai ta kasa fahimta ta, a ƙarshe ma ta tari numfashina, dole yasa nayi shuru, ka sani Ubangiji da kasan acikin littafinsa mai tsarki yace zaku so abu ya zamo ba shi bane alkairi a gareku haka zaka ƙi abu sai ya zamo shine alkairi a gareka. A ko yaushe alkairi shi nake nema saboda ina sonka bashi yake nuna cewa dole zanyi rayuwa da kai ba, ni da sauƙi na ɗauki rayuwa ina haƙura da abu muddun na fahimce bazan samu ba koda kuwa hkrn zai zamo min matsala, kaje ka dakatar da momma daga haɗamu aure ni kuma na maka alƙawarin zan hkr da kai, bansan baka ƙaunar ganina ba da na juma da bar muku part ɗin ku, kuma yanzu ma daga yau bazan ƙara kwana a sashin ku ba, zan koma namu nikam bazan ƙara zuwa gareka ba saboda waii kaga fuskata, sai dai kuma idan hanya ce ta haɗamu, wannan bazan ce bazaka ganni ba, saboda hanya ta kowa ce babu wanda aka shata masa layi akace ga nasa, kayi hkr da takuraka da nayi a rayuwarka ina mai baka hkr, ba laifina bane laifin soyayyace.”

Tayi maganar tare da sunkuyar da kanta ƙasa tana goge hawayenta, Haidar shuru yayi yana ƙare mata kallo, wani sashin a jikinsa na ƙoƙarin jin tausayin Rufaida yayin da wani sashin ke raya masa neman yaudararsa kawai take da kalamanta saboda ya tausaya mata bakinsa ya cije cikin tsawa yace.

“Bazaki taɓa yaudarata da waɗannan kal….”

Hannu ta ɗaga masa idanunta jiƙe da hawaye ƙirjinta na suya tace.

“Ba sai kace komai kabi shawarar zuciyarka duk abinda ta yanke maka shine dai-dai. Tabbas son zyciya da ƙawa zuci yana kai bawa ga turbar baƙin duhu, hmmm! Ka fara dakatar da jinin da ke zuba daga hanunka.”

Tayi maganar tana juyawa ta fice da sauri tana toshe bakinta da kuka ke ƙoƙarin kufce mata, tabbas Haidar shine rayuwarta sai ƙaddara na neman shata musu layi a tsakani, Haidar hanunsa ya ɗago yana duban yadda jini ke zuba tare da jan tsuka, a bakin gado ya zauna tare da jawo tisue ya yaga hanu yasa zai goge jinin maganar Nafeesa ta faɗo masa a ransa (Rashin bayyana maka muradin ruhuna kuma farin ciki na a tunanina wannan shine kwanciyar hankalin ka, domin kuwa daga ranar da kasan wanene daga lokacin tashin hankalin ka zai hauhawa, baccinka zai zamo na wucin gadi, sannan bugawar zuciyarka zai kuma yin sama, hmmm ba tausayinka nake ba amma tunda ka matsa bara na sanar da kai muradin rayuwar tawa, HAIDAR dan uwanka Al’ameen shine wanda nake so kuma yake sona, a yanzu muna tare da Al’ameen kuma muna son junanmu, kasan meye tun ranar da kazo dashi wajena daga ranar ya fara bibiyar rayuwata, ya kuma sanar dani mugayen halayyar ka, wanda kake boye min daga lokacin na fahimci kai ba mutumin kirki bane naga kuma ya dace na rabu da kai, ban taɓa tsammanin kai mashayi bane, kuma mazinaci ba sai da ɗan uwanka ya sanar dani gaskiya kuma ya nuna min shaida ta gani da ido.) Wurgar da tisue ɗin yayi tare da toshen kunnuwansa yana furta.

“No mafarki nake! Ina hakan bazata faru ba.”

Hanu yasa ya danne saitin zuciyarsa tare da furta.

“Tabbas ba mafarki bane da gaske Al’ameen shine ya kashe min rayuwata, shine yake neman ɓata min suna a duniya, meyasa Aminina zai zamo ƙalubalena saboda Mace kawai, ka ci amanata Al’ameen kaci amanar Aminta ka yaudari ƴan uwantaka Tabbas ba’a gane mungu a fuska, hmmm! Me na yiwa rayuwa take garari dani, meyasa Al’ameen zai min haka meyasa zai ci amanata mena masa a rayuwa mai muni wanda harna cancanci wannan hukuncin, wa zai amsa min wannan tambayar?”

Yayi maganar yana sakin kuka tamkar ƙaramin yaro tare da kwanciya rigingine, rayuwa ta masa zafi kansa ya kulle ya rasa menene zaiyi yaji daɗi, da wannan tashin hankalin Haidar ya kasance da kuma nauyin ƙirji.

*****

Ita kuwa Rufaida da gudu ta ƙarisa bedroom ɗinsu tare da rufe ƙofar da key tana sakin kuka mai cin rai, zama tayi bakin door ɗin ta saki kuka mai sauti, sosai take kukan tamkar ranta zai fita, kanta ta jingina jikin door ɗin, Tabbas tana cikin gararin rayuwa da kuma dakon da bata san ranar sauƙesa ba, “shin menene aibuna me na gaza dashi a rayuwa wanda Haidar zai ƙyamace ni, Soyayya guba ce mai dafin gaske dafinta yafi na maciji haɗari, hmmm! Soyayya tasa har namiji ke wulaƙanta ni, meyasa bazan so Khalid ba domin kuwa shine mai sona da gaskiya, matsalar daga zuciyata ce itace bazata amince da hakan sai dai bazan yadda zuciyata ta azabtar da wanda ke ƙaunarta ba, domin kuwa nasan zafin ƙiyayyar masoyi zan nuna maka kulawa ko da kuwa zuciyata bata so, dole na nisanci Haidar zan masa nisa ko zuciyata zata samu salama.”

Ta furta maganar a fili tana miƙewa tsaye tare da shigewa tollet tana goge hawayenta, wanka fuskarta ta wanke gudun kar Momma ta fuskanci wata matsalar ba tare da ta ɗauki kayanta koda guda ɗaya bane ta fito falo da niyyar komawa sashin su domin kuwa alƙawari ta ɗaukarwa kanta bazata ƙara kwana cikin wannan sashin ba, a inda tabar Momma anan ta sameta, ɗan murmushi ta saki cikin danne damuwarta ta zauna a hanun kujerar Momma ce tace.

“Yanzu nake cewa kin juma a ciki, meya faru da Aliyun?”

Murmushi Rufaida tayi, sai dai duk ɓoye damuwarta sai da Momma ta fuskanci tana cikin damuwa domin kuwa wanda ya fika bazaka taɓa iya masa dabara ba.

“Damuwar ƙarama ce kuma anyi maganinta, daga yau babu wata fitina da zata sake tashi yama kwanta yace bacci zaiyi ya gaji, kansa ke masa ciwo.”

“Ba dole kansa yayi ciwo ba yana ɗaukar ƙaramar damuwa yana sanyawa a zuciyarsa, kinga Rufaida naga kamar kina cikin damuwa ya miki wani abun na rashin kyautawa ko?”

“A’a Momma babu abinda yamin, kawai dai idanunki ne tun na haihuwa sun tsufa shiyasa kikaga kamar ina cikin damuwa, amma ni babu wata damuwa da nake ciki saima farin ciki.”

Murmushi kawai Momma tayi domin kuwa tasan karya Rufaida ta mata cewa tayi.

“Ja’ira ai kuwa waɗannan idanun nawa sunfi naki gani.”

“An Momma bara na shiga wajen part ɗin mu.”

“Okay to shikenan sai kin dawo.”

Murmushi tayi tare da cewe.

“Ina sonki Momma I love you too.”

Murmushi Momma tayi kafin Rufaida ta fita idanunta na cikowa da hawaye Aunty bata nan tana can Egypt wajen Ashfat, Abi shima baya nan yaya Faruq shima haka, babu kowa cikin part ɗin nasu bata san dawa zata zauna ba, tsuka taja tare da dafe kanta tana furta.

“Dole a yau ɗin nan nabar gidan nan, gara naje Family hause ɗin su Aunty na zauna zaifi nan gidan kwanciyar hankali.”

Tayi maganar tana komawa part ɗin su Haidar Momma ta tashi a falon, bedroom ɗinsu ta shige tare da ɗaukar bag ɗin ta da gyale sai key ɗin mota ta fito da sauri, motar ta shiga tare da ja tabar gidan.

Da sauri Inna Jumma ta fito daga bedroom ɗin Ablah tana kwaɗawa Ladiyo kira da sauri ta fito daga kitchen tana amsawa.

“Ina kika gane min yarinyar nan Ablah, na shiga ɗakinta ban ganta ba.”

Ladiyo cewa tayi.

“Gaskiya ban ganta ba nima rabona da ita tun da safe da tayi breakfast ta shige makaranta, Kuma gaskiya bana tunanin ta dawo gidan nan domin kuwa banga alamun ta ba.”

Aunty Amarya dake zaune tana danna wayarta ne ta saki murmushi cikin zuciyarta tana furta (Zaku ganta amma a mummunan yanayi dama kun daina sauri) a fili kuma sai ta ce.

“Bata dawo ba gaskiya amma ina Isa driver shi za’a tambaya ai tunda shine mai ɗaukota.”

Numfashi Inna Jumma ta saki tare da cewa.

“To bata haka ma kullum akan lokaci take dawowa Allah dai yasa lafiya, kina da gaskiya, ke ladiyo je ki kira min Isa.”

Tayi Maganar cike da damuwa da to Ladiyo ta amsa tana fita da sauri, Inna Jumma mita ta hau yi.

“Ga waɗannan ja’iran yaran suna neman su ɓallo mana fitina a cikin gida, ni yau kaina duk ya ɗauki zafi dole ne na dakatar da wannan matsalar.”

Bakinta Aunty Amarya ta taɓe ba tare da ta tankawa Inna Jumma ba, Ladiyo bata juma da fita ba ta dawo da sauri tace.

“Inna Jumma Isa driver bayanan na tambayi Adamu mai bayin flower yace wai tunda ya fita ɗauko Ablah bai dawo ba.”

Cike da tashin hankali Inna Jumma tace.

“Anya kuwa lafiya, bara na kira Aminu yaje ya duba makarantar tasu ya gani ko lafiya, har 4:30.”

Tayi Maganar tana kiran Layin Al’ameen kusan 5 miss Call bai ɗaga ba cike da damuwa tace.

“Shima aminun bai ɗaga wayar ba, kinga Ladiyo kira min Idi kuje tare dake makarantar tasu ku duba ganan key ɗin mota ɗauki kawai kice ya kaiki ku dubo maza kuyi sauri.”

Da to Ladiyo ta amsa tana ɗaukar key ɗin tare da fita cikin sauri Inna Jumma bedroom ɗin ta ta koma ta zauna cike da damuwa, dariya Aunty Amarya ta saka tare da ɗaukar wayarta ta dannawa Hajiya Mansura kira tana haurawa sama, bayan ta ɗaga ne Hajiya Mansura tace.

“Ya Akayi ƙawata, kardai har mummunan labarin ya iso domin kuwa ganin wannan kiran naki akwai good News kinsan me ma akwai wani babban labari amma dai fara sanar dani meke faruwa?”

Dariya Aunty Amarya tasa tace.

“Hmmm! Mummunan labarin dai bai iso ba tukunna, sai dai har yanzu bata dawo gida ba, hankalin tsohuwar gidan harya fara tashi yanzu haka zancen da nake miki tasa aje a duba mata ko lafiya, wannan ma kaɗai ya isa ya tabbatar da cewa angama da ita dama ai maganin shegen biri karen maguzawa na juma ina faɗa mata ni ba sa’ar yinta bane amma taurin kanta ya hanata fahimta, sai yau nasan zata fahimta da yaren da ya dace.”

Dariya Hajiya Mansura ta saka cikin dariya tace.

“Ai kema kin sani bana shirya tuggu ta watse Nasara a jinina yake, kinsan me kuwa, wannan Yarinyar Ablah fa bata da gata babu wani mataki da za’ayi yunƙurin ɗauka domin kuwa yasasshiya ce, a yanda naji labari ma akanta bata da dangin uba ba’a san asalinta ba, wasu ma cewa suke shegiya ce, saboda bata da dangin Uba uwarta kawai aka sani itama Uwar ba’a san nata dangin ba, raɗe raɗi ma ake cewa abun kunya uwar tayi ta dawo da su yaran Nigeriya, buzaye ne ƴan Niger, kinga kuwa bata da gatan da za’a wani binciken suwaye suka mata fyaɗe.”

Zaro idanunta Aunty Amarya tayi cike da mamaki tace.

“Bata da asali ashema shegiya ce, hmmm lallai kam ana kwashe kwashe a gidan nan a garin kwashe kwashe har an ɗebo mana shegiya, to ai shikenan Allah yasa ma ta samu ciki a wajen fyaɗen kinga itama zata haifi shegiya shikenan ta gado uwarta, ina ma ace na juma da sanin wannan maganar da kuwa kullum sai na mata gori, yanzu ma bata ɓaci ba, zamuje dubiya da kuma jaje.”

Dariya Hajiya Mansura tayi tare da cewa.

“Baki da dama ƙawata, kinga ina aiki, mayi waya anjuma idan labarin ya iso musu.”

Tayi maganar tana katse wayar dariya Aunty Amarya tasa tare da zama a gujerar bedroom ɗin ta ta furta.

“Hmmm! Wai shegene yake ƙoƙarin ja da ɗan halak, aikuwa ga inda kuskurenki ya kaiki.”

Gudu yake shararawa a saman titi tamkar iska zata ɗauki motar zuciyarsa kuma sai hura take masa ji yake tamkar idan yaga Nafeesa ya shaƙe mata wuya har sai mutu, ikon Allah da kiyayewarsa ne ya kawo Al’ameen ƙofar gidan su Nafeesa cikin sa’a kuwa ya ganta zata shiga cikin gidan nasu wani irin hon ya danna mata da karfi wanda yasa Nafeesa juyowa, motar Al’ameen ta gani murmushi ta saki tare da nufo motar, tana tsayuwa Al’ameen ya buɗe ya fito a zuciye hanu ya ɗaga ya ɗauke Nafeesa da maruka har guda Uku wani irin azaba Nafeesa taji sai da taga kamar wuta ya gifta ta idanunta, Al’ameen nunata da yatsa yayi tare da cewa.

“Burinki ya cika kin shiga tsakanina da Aminina, amma ki sani shine Wawa Wanda bashi da lissafi makircinki iya kansa kawai zai tsaya, banda ni Al’ameen domin bazaki taɓa nasara a kaina ba, na faɗa miki zakiyi biyu babu a rayuwarki, zakiyi baƙar danasani da nadamar wannan wawancin da kikayi, waima na tambayeki kin taɓa hauka ko domin kuwa ƙwaƙwalwarki bata masu lafiya bace duk yadda akayi kina da folda a sakatirin, Idan banda ke mahaukaciya ce a hakanne kina sona haka ake Soyayya a hakan zaki jawo hankalina har na yadda na amince da kai, tunda nake a rayuwata ban taɓa ganin daƙiƙin mutum irinki ba, marar wayo karatunki bashi da amfani domin kuwa baki da wayewa dama kin haƙura da zuwa makaranta kin cigaba da zaman jahilcin ki, matsiyaciya marar albarka duk yadda akayi akwai bakin iyaye akanki, zan zamo miki masifa a cikin rayuwarki ki ijiye wannan a ranki.”

Yayi maganar yana huci tare da buɗe motar sa ya shiga da ƙarfi yaja tare da buleta da ƙura yabar wajen, Nafeesa murmushi ta saki tana riƙe da fuskarta inda ya sharara mata mari, bata tanka masa ba, sai dai idanunta yana nuni da cewa zasu haɗu a gaba, juyawa tayi ta shige cikin gidan su, Mama ta samu zaune a cikin falon gefenta ta zauna tare da cewa.

“Mama kwanaki kince idan muka gagara karkato da Al’ameen gareni mu baki aikin, to mun gagara Mama yanzu komai yana gareki, kiyi ƙoƙari kiyi komai domin mu samesa hakan shine kaɗai damar da muke dashi na cikar burin mu, bayan ita bamu da wata damar, nasarata shine nasararki faɗuwata kuwa kema faɗuwarki ce.”

Murmushi Mama tayi tare da jawo Nafeesa jikinta tace.

“Ta yaya zanyi sake wannan damar ta wuce mu, muddun Boka Damu yana raye to dukkan burukanmu zasu cika, ki kwantar da hankalinki Nasara tamu ce.”

Murmushi Nafeesa tayi tare da cewa.

“Ina sonki mamana, na amince aje wajen BOKAN. “

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Aminaina Ko Ita 41Aminaina Ko Ita 44 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×