Skip to content
Part 60 of 67 in the Series Aminaina Ko Ita? by Rasheedat Usman

Ya Akayi ƴar saka ido.?”

“Aikin kine nagaa yana kyau yau kuma munafurcin me kika fita aikatawa tsakar dare.?”

Murmushi Aunty Amarya tayi tare da cewa.

“Ba kinyi video ba, ai bakya buƙatar tambayata, wato kin mai dani shasha bari ki bini a baya, to bari kiji duk wanda ya rigaka bacci zai rigaka tashi, haka duk wanda ya girmeka sai ya fika wayo, zato kike kin min video kin samu hujjar tona min asiri ko, to ki duba video ɗin da kikayi ki gani ko za’a hango inuwata.”

Tayi Maganar tana sheƙewa da dariya, Ablah saurin duba video ɗin tayi tare da zaro idanunta, ashe mai gadi ne ya miƙa jakar ba ita ba, numfashi ta sauƙe cike da kufula ta dubi Aunty Amarya tace.

“Tabbas kekam bazaki taɓa sanyi ba a rayuwarki yanzu ko wannan mutuwar bata sakaki kinyi ladaf ba, sai yaushe zaki koma ga ubangijinki, yara biyu fa kika rasa ta hanyar wannan son zuciyar taki, mekika satarwa Daddy.?”

“Hmmm Ablah kenan, zatonki shuru zanyi nayi rayuwar ƙasƙanci bayan mutuwar Daddyn Al’ameen, to bari kiji dama da nake da ƴaƴa nake tsammanin gado nayi ƙoƙarin ƙarin wasu kuɗin bare kuma yanzu da nasan bani da kowa bani da gadon Daddyn Al’ameen sai tumilin takaba, wallahi bazan yadda na tashi da iya tumilin takaba ba, dole ne na mallaki manyan kadarorinsa da kuɗaɗe masu yawa yadda bazan taɓa talauci ba harna mutu, kuɗi na ɗiba na fita dasu Ablah har kimanin 10b hmmm! Kuma sun tafi kenan kina yunƙurin tona min asiri da wannan video ɗin bani za’a zarga ba, mai gadi za’a zarga Saboda shine ya miƙa jakar bani ba, kinga zaije yayi prison a madadina muddun bakya son Wannan laifin ya shafi wanda baiji ba bai gani ba, to kiyi shuru da bakinki tamkar bakiga komai ba, domin kuwa na faɗa miki tun a baya babu mai iya dakatar dani.”

Tunda ta fara magana Ablah ke kallonta cike da baƙin ciki da takaici Al’ameen ne da ya fito shima neman ruwa kasancewar ba’a saka a fridge ɗin ɗakinsa ba ya hango su tsaya carko carko.

“Ablah! Meya fito daku kuke tsaye a wannan tsohon daren?”

Kanta Ablah ta kawar gefe tare da cewa.

“Sai ka tambayeta ta baka amsa, tunda itace mai abun faɗi.”

AUNTY Amarya murmushi ta saki tare da cewa.

“Ablah wai mena tsare miki ne a cikin gidan nan kika bi kika tsaneni, dan Allah idan wani laifin na miki ki faɗa min na gyara, kina min rashin kunya da gatsali meyasa kike zagina kike faɗa min Maganar da kikaga dama.?”

Tayi Maganar tana raurau da murya tamkar zatayi kuka, Ablah kallo tabi ta dashi, tana jinjinawa munafurci irin na Aunty Amarya, murmushi ta saki tace.

“Hmmm! To ƴar wasan kwaikwayo, gama munafur…”

“Karki kuskura ki ƙarisa Maganar da take bakinki Ablah, karki zageta a gabana,domin kuwa mummunan kalma kike da niyyar faɗa mata, Uwa take a wajena, bazan tsaya na zuba idanu naga za’a ci mata mutunci ba, kamar yadda zan kare martabar Ummina haka zan kare martabarta, ki kula da maganganun da zaki faɗa mata.”

Yayi Maganar cikin fushi.

“Hmmm! Har abada kai a cikin kuskure kake yaya Al’ameen, shiyasa na zaɓi rabuwata da kai domin kuwa ƙwaƙwalwarka bata taɓa fahimta sai ɗaukar zafi da fushi gami da zuciya kawai ka iya da kai mai kulane daka juma da fahimtar wasu matsalolin cikin gidan nan, mtsss!”

Tayi Maganar tana jan tsuka tare da barin Wajen Aunty Amarya hawayen munafurci ta share tare da dafa Al’ameen tace.

“Bansan mena mata ba, bata sona,ni ƴa na ɗauketa amma ita zuciyarta akwai wata manufa a kaina, Al’ameen, wataƙila zato take koni na shiga tsakanin ku a baya.”

Kansa ya girgizawa Aunty Amarya cike da so da ƙauna yace.

“A’a Aunty babu abinda kika mata bansan meyasa Ablah ta sauya ba ɗabiunta sun sanja tana wasu abubuwan tamkar ba ita ba, amma karki damu zan mata Magana insha Allah zata gyara, bara naje na sameta.”

“Shikenan Al’ameen, na gode sosai, Tabbas yau na tabbatar da cewa bazaku taɓa bari nayi kukan rashin ƴaƴana ba, Allah ya maka albarka amma yanzu kaje ka kwanta ka barta sai da safe dare yayi sosai.”

“Shikenan Allah ya kaimu kije ki kwanta.”

Kanta Aunty Amarya ta ɗaga tare da shigewa bedroom ɗin ta.. 

Zama yayi a ɗaya daga cikin kujerun dake cikin falon ya dafe kansa cike da damuwar Sauyawar da Ablah tayi wannan wacce irin rayuwace Ablah ta ɗaukarwa kanta, halayenta masu kyau ne a baya tana da hkr da yafiya to meyasa yanzu ta sauya?”

Yayiwa kansa tambayar yana dafe kansa ya juma sosai zaune a wajen kafin ya koma bedroom ɗinsa.

Washegari da safe bayan sunyi breakfast Al’ameen ya fito da niyyar shiga Wajen Momma sai ya hango Abbas tsaye shida Faruq a mungun zuciye Al’ameen ya ƙarisa Wajen tare da nuna Abbas da yatsa.

“Uban me ya kawoka cikin gidan nan, ko kana da gado a ciki ne.?”

Bakinsa Abbas ya taɓe tare da yamutsa fuska ya furta.

“Faruq Ko da shekara dubu zakiyi bakaga mutum ba, randa kuka haɗuwa karka tambayesa halinsa ka tambayesa kawai ya yake domin kuwa mai hali baya fasawa sai dai ya ɗauki hutu, ka faɗa masa cewa ba maula nazo yiba.”

Cike da kufula Al’ameen yace.

“Maula kazo yi mana idan ba maula ba meya kawoka, ko bibiyar Ablah da kakeyi ba maula bace, ka sani Ablah tafi ƙarfinka nesa ba kusa ba, domin kuwa haramunce a gareka.”

Murmushi Abbas yayi sosai tare da duban Faruq yace.

“Shirmen banza da kishinsa ns banza da naso aureta tun kafin ka dawo hankalinka na ɗauketa, wai meyasa kake da zargi ne Al’ameen, ka sani cewa ni alkairi na maka, kuma bana nufinka da sharrri sai dai abinda na lura da kai shine ka cika zargi a kaina abinda ya haɗamu a baya na juma da gogesa a ƙwaƙwalwa ta, dan haka ka daina tantama a kaina, Faruq wajenka nazo naji me kuka yanke akan Nafeesa Saboda har yanzu ba’a taɓa fuskarta ba, wankewa kawai akayi aka ɗaure da bendeji, shin ka amince a biya kuɗin aikin nata ne.”

Al’ameen cike da ɗaurewar kai yace.

“Ban fahimta ba, me kake nufi meya faru da Nafeesan.?”

“Acid aka watsa mata a fuskarta tayi damage fuskar, basu da kuɗin da zasuyi jinyarta mahaifin ta kuma yaƙi zuwa kanta, shine ake buƙatar taimako.”

“Taimako! Hoo! Wannan matsiyaciyar wa zai taimaka mata ku barta da ciwonta ai duk wanda yace cuta yasa a ransa ya dinga ganin iftila’in rayuwa kenan, Abbas dan zan tambayeka, meyasa Ablah take yawan zancenka tafi fifita ka fiye dani hakan yana ƙona mini rai, dan Allah ka fita a rayuwarta ka yanke ko wacce alaƙa tsakanin ka da ita.”

“Shikenan Al’ameen karka damu zan yanke alaƙa da ita amma dole sai na fahimtar da ita dalilin hakan tukunna.”

“Shikenan na gode idan kamin haka shine zaisa na yadda da kai a rayuwa.”

Murmushi Faruq yayi tare da cewa.

“Yanzu abinda za’ayi Abbas kaje ka basu dubu ɗarin da suka nema, a treatment ɗinta ku barmata fuskarta haka ya zamo mata izna a rayuwarta.”

“To shikenan bara naje ASIBITIN.”

Yayi Maganar tare da miƙa masa hannu sukayi musabaha sannan ya shiga cikin motarsa yaja.

Cikin gida suka koma, basu juma da shiga ba Haidar ya shigo, Al’ameen zamewa yayi ya shige bedroom ɗin Ablah tana zaune tana assignment ya shigo gefen gadonta ya zauna tare da cewa 

“Ablah na roƙeki da girman ubangiji kiyi haƙuri ki yafe min, kuskurena gareki ina sonki bazan iya jure fushinki ba, dan Allah kiji tausayina na yadda nayi kuskure ki amshi wannan wayar ki duba waɗannan videos ɗin dake ciki idan har kin gamsu dasu na Tabbata sune hujjar da zaisa ki yafe min.”

Yayi Maganar yana ijiye mata wayar tare da tashi yabar ROOM ɗin sanda ya fita sannan ta kai dubanta ga wayar hannu tasa ta ɗauki wayar tare da danna video ɗin, kaf sanda ta kallesu Tare da sauraron recording ɗin Jamila, numfashi ta sauƙe, tare da sakin murmushi ta furta.

“Dama na sani bazaka wulaƙanta ni haka kawai ba, na yafe maka masoyina.”

Tayi Maganar tana murmushi tamkar Al’ameen ɗin yana gabanta wayar ta ijiye a gefe wayar Faruq ne ma, kusan awa biyu taga bai dawo ba hakanne ya sata ɗaukar wayar ta fito falo, carko carko ta gansu tsaye ƙarasawa tayi ta tsaya tare da duban Inna Jumma tace.

“Me yake faruwa Inna Jumma?”

Cike da masifa Inna Jumma tace.

“Wani rainin wayo ne yake faruwa a gidan nan Ablah, wai jiya Ali ya shigowa da Amadu kuɗi cikin gidan nan a jaka, ya ijiye akan yau da safe zaije banki ya ijiye su, shine yanzu aka nemi jakar aka rasa,sai kace fukafuki ce da jakar bare tayi tsuntsuwa ta tashi, karo na farko kenan yau da aka fara sata a cikin gidan nan.”

Kanta Ablah ta ɗaga ta dubi Aunty Amarya da take tsaye tamkar ba ita bace ɓarauniyar, numfashi Ablah ta saki zatayi Magana taji Aunty Amarya na cewa.

“Jiya naga Ablah ƙarfe biyu na dare tabar falon nan ta fita waje, meya fitar dake, domin kuwa Al’ameen kai ka gammu sanda na fito zan nemi ruwa na tsaida ta ina tambayarta take tsayar min da rashin kunya, ya kamata a bincike ki?”

Gabaki ɗaya wajen kallon su suka mayar kan Ablah, wani irin kallon tsana da takaici Ablah ke bin Aunty Amarya dashi, lallai ta raina mata wayo wato ita ce ma zata mata sharri a da taso rufa mata asiri ko Allah zaisa ta tuba sai dai ta fahimci cewa Aunty Amarya ba abar rufawa asiri bane, cike da gatsali Ablah tace.

“Kuɗin naje na sata na fita dashi, amarya kinma raina min wayo na rantse da Allah, na juma banga Uwa marar imani da adalci ba irinki, kekam ace zaki zamewa mutum madadin uwa to wallahi asara ce a gares…”

Bata kai ƙarshe ba Al’ameen ya dauketa da kyawawan maruka har guda Uku Cikin tsawa da zafin zuciya ya nunata da yatsa.

“Na ga alama baki da mutunci Ablah ɗabi’unki sun sauya tun sanda kika fara amsa sunan Ahalin AHMAD GIWA, ki sani kasancewar ki ƴar manyan mutane ba burgewa bace a gareki raina iyayenki, na faɗa miki amarya uwata ce, zan iya rabuwa da duk wanda zai rainata kasancewar ina sonki bashi zai baki damar tozartani ba, domin kuwa wannan tozarci ne, gareni, tun kafin na aureki kin fara wulaƙanta iyayena ina kuma ga kin shigo gidana,haba abl…”

“Ya isheka haka Al’ameen! Ya isheka, ina da mutunci kuma bana raina iyayen wasu ka sani cewa sai kayi danasanin marina da kayi akan wannan tsohuwar banzan, ba dai akan wannan azzalumar ka saka hannu a jiki n…”

Hannu ya ɗaga zai ƙara kai mata wani marin Cikin sauri RUFAIDA tasha gaban Ablah marin ya sauƙa a saman fuskarta, fuskarta ta dafe cike da ƙunar rai tace.

“Tabbas Maganar Ablah gaskiya ce, akan Aunty Amarya babu inda ta kuskure ni nasan gaskiya ka daina aikata kuskuren da zai saka danasani daga baya yaya Al’ameen.”

Cike sarƙaƙiya Inna Jumma dasu Haidar ke kallon su, cikin tsawa Al’ameen yace.

“Danasanin me zanyi saboda na hukunta marar kunya, hmmm! Ina iyakaci ta juyawa soyayyata baya ne, bana buƙatar Soyayyarta a gareni yanzu domin kuwa tarbiyyar da ta ɗauka ba tarbiyyar da uba zai nemawa ƴaƴansa bane zan haƙura da ita ba dan bana sonta bane sai dan Saboda samawa ƴaƴana uwa ta gari, na sani sanki bazai zuciyata kin ha’ince ni Ablah.”

“Hmmm! Rufaida ki rabu dashi, duk abinda yaga dama yayi amma bazan fasa kiran Amarya da azzaluma ba.”

Tayi Maganar tana juyawa a fusace, har taje bakin ƙofa ta tsinkayi muryar Rufaida na cewa.

“Ki fito ki sanar dasu cewa itace ta kashe Aksat da Ummi saboda son Duniyarta da dukiya, kina da hujjar hakan a hannunki Abbas ya sanar dani, akwai hujjar a hannuki, bazan zuba idanu ki ɓoye gaskiya ba, ke a miki kallon marar tarbiyya,ki bayyana gaskiya dan Allah.”

Ablah murmushi tayi tare da kau da kanta gefe tace.

“Bani da wata gaskiyar da zan furta Rufaida ki barni kawai a matsayin marar tarbiyyar.”

“Sam bai dace ba ki ɓoye gaskiya bayan kin santa kuskure ne mai girma wannan na sani tsayuwa a cikin gaskiya akwai wahala da wuyar gaske sai dai komai wahala dole a karshe gaskiya itace take nasara , ki kawo karshen wannan..”

“Ki mana shuru mahaukaciya, aahe da dama da mahaukaciya muke rayuwa bamu sani ba, Rufaida bansan baki da hankali ba sai yau, ko mahaukaci ɗan uwanki aka kawo bazai yarda da wannan tatsuniyar ba, bare kuma mu lafiyayyu masu cikakken hankali, ki dawo hankalinki kafin na sumar dake.”

Cewar Al’ameen, Aunty Amarya kuwa ihu ta kawo ta danna ita a dole an mata sharri, Inna Jumma gagara magana tayi sai idanu da ta zuba musu, zatayi Magana suka kuma jin Rufaida ta cewa Ablah dake ƙoƙarin barin wajen.

“Kin sani kike ɓoyewa lallai kina hannu a cikin aikata zunubi, sannan ki sani sai Allah ya gwada miki aya,har sun fara min kallon mahaukaciya kuma kina da hujjar da zaki wankeni daga wannan haukar da suka ɗaura min, na kasa fahimtar ke wacce irin mutum ce mai gaskiya ko munafuka.”

Runtse idanunta Ablah tayi tana jin ciwo har cikin ranta bata tankawa Rufaida ba ta shige bedroom ɗinta, tana shiga Al’ameen ya zaro bell yayo kan Rufaida yana kuma cewa Aunty Amarya.

“Ko da kuwa dukka jikina kunnene bazan taɓa yadda da wannan ƙazafin da suka miki ba, Ablah ta fita a raina ta sane min a yanzu haka zarginta nake domin kuwa ita abar zargi ce, ita nake zargi da kashe min mahaifiyata da ƴan uwana a wancan lokacin na kareki amma a yanzu da kaina nake zarginta, yayi Maganar yana ɗaga belt ɗin ya sauƙewa Rufaida a jikinta runtse idanunta Maimu tayi hawaye na biyo baya da gudu ta shiga bedroom din Ablah dake tsaye ta runtse idanunta Maimu ta tsaya a gabanta tare da cewa.

“Ni bana zarginki domin kuwa nasan bazaki taɓa munafurta mu ba, sai dai ki sani Rufaida bata karya dole kin san wani abu daga cikin ɗauki ɗaiɗai da ake mana, gashi can zai illata Rufaida idan ya illatata sai kiji daɗi amma ki sani Allah zai saka mata, kina wannan ɓoye ɓoyen ne saboda ki samu ki mallaki yaya Al’ameen ko, to ki sani karya fure take bata ƴaƴa.”

Tana yin Maganar ta fita a fusace hawayene ya biyo fuskar Ablah, a hankali ta fito falon a bakin room ɗinta ta tsaya tare da riƙe ƙofa tana kallon yadda Al’ameen ke dukan Rufaida tamkar zai kasheta, Haidar runtse idanunsa yayi cike da ƙunar zuciya ya kasa jurar ganin dukan da Al’ameen ke yiwa Rufaida domin kuwa zuwa yanzu ya fara jinta a ransa, sai dai bashi da ikon dakatar da Al’ameen wajen hukunta ƴar Uwar sa a domin ta aikata laifin da ta cancanci hukunci juyawa yayi zai bar wajen sukaji muryar Daddy na cewa.

“Idan ka kuma sauƙe belt ɗin nan a jikinta sai na ka kwana a cell yau.”

Gabaki ɗaya juyawa sukayi suna kallon Daddy shida ya tafi Kaduna jiya meya dawo dashi yanzu, ƙarasowa yayi tare da ɗauke Al’ameen da wawan mari, Wanda sai da ya razana kowa dake wajen domin kuwa tunda Al’ameen yazo duniya Daddy bai taɓa saka hannu a jikinsa da sunan duka ba sai yau, riƙe fuskarsa Al’ameen yayi da mungun mamaki take idanunsa suka kaɗa sukayi jajur kal

lon Daddy yayi a zuciye ya furta.

“Daddy…”

<< Aminaina Ko Ita 62Aminaina Ko Ita 64 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×