Skip to content
Part 21 of 33 in the Series Asabe Reza by Fulani Bingel

Fakriyya

“Haba ki zauna mana tunɗazu kike ta zirga-zirga, zai fito fa.”

Linda ta furta tana jawo hannunta danta zauna.

“Ban san yadda zan yafe miki ba idan wani abu ya same shi sanadin wannan tunanin naki. Ki duba awowin da aka kwashe ace har yanzu suna asibi…”

Wayarta da ta ɗau ƙara ta katse ta. Da sauri ta ɗaga.

“Yah Bio har yanzu ba wanda ya fito?.”

“Yanzu ya fito Madam cikin baƙar motar da suka je, sai dai shi kaɗai ne.”

“Yawwa bi shi duk inda ya shiga kaima ka shiga, har ka samu damar da zaka sha gabansa, ka masa koma menene dan ya yadda ya bika.”
“Okay Madam.”

Ya furta yana sauke wayar.

Komawa gefe ta yi ta zauna tana jijjiga ƙafa.

Falon ya yi tsit! Sai duba agogo da suke yi a kai-akai, har zuwa lokacin da  Sa’a guda ta shuɗe Bio bai kira ba.
Ɗaga wayar ta yi ta kira shi.

“Wai Nigeria za ku bari hala? Na jika shiru har sa’a guda.

“Sorry Madam, wani irin Sha tale-tale yake yi. Ya bi ta Kundila ya ɓullo Zaria Road, yanzu kuma ya hau Bypass ya dawo Hadejia Road inda zai sada shi da Cheesy Bar.”

“What! Cheesy Bar?”

“Haka dai na gani.”

“Daidai ke nan, Allah yasa karya kauce. Ci gaba da binsa ka ga inda zai tsaya. Bari na yi waya da wata a gurin.”

Ta sauke wayar tana latso number Pencil.

“Kina Ina?”

“Idan samuwa ce ina Cheesy Bar Madam, idan kuma ba ita ba ce bana nan. Wait! Ya a kai kika san na dawo, alhali ban shigo A Watse ba?”
“Oh god! Pencil barni da surutanki kiji zancena. Akwai wani gaye da zai shigo a baƙar mota nan wurarenku, duk da ban da tabbas zai zo ɗin.

Amma idan ya zo ki ba shi koma menene da kika san zai gusar da hankalinsa ki kawo min shi.”

“A nawa?”

“Haba mana kinsan zan baki ai.”

“Fara faɗa mini tukun.”

“50,000, ya yi?”

“Haba Madam Ree, ya fi in sai tissuen goge abin da su?”

“Ba na son iskanci Pencil, yaushe rabon ki yi harka da wani sai yanzu za ki ce wani tissue, to 70,000 fa?”

“Ki cike su zama ɗari mana ki huta.”

“Zan cike idan aikin ya yi. Buɗe whatsapp naki na turo miki hotansa.”

“Okay to.”

Tura mata ta yi, ta jira har Bio ya sake kiranta.

“Madam, ya tsaya jikin bishiya kusa da Cheesy Bar, in ƙarasa aikin nawa?”

“A’a barshi anan ɗin, ko bai isa ba akwai wacce nasa za ta ja shi ciki. Dawo kawai ka karɓi haƙƙinka.”

“Okay.”

Mintuna ashirin suka ƙara shuɗe wa, kiran Pencil ya shigo.

Shiru ta yi tana saurararta.

“Ya sha ne?”

“Ki bari ya sha to za ki ji alert, ki yi iyakar ƙoƙarin ki fa.”

A haka ta sauke wayar tana jin zuciyarta na washewa harta juya ta nama Linda murmushi.

“Duk kin wani damu da ya zo, kin kuma ƙi gaya min amfanin da zuwan nasa zai miki.”

“Ƙoƙari zanyi ya kwanta da ni tunda ba ya hayyacinsa. Zan yi Videon da shi kaɗai ya isa ya sa shi aure na ko bai so ba idan yaga zan watsa media.”

“Ree!”

Ta furta da gargaɗi mamaki na bayyana a fuskarta.

“Ina ɗayan, shi bai isa ba?”

“Bai isa ba, son samu na samu irinsu goma.”

Murmushi ta yi tana ƙara kishingiɗa saman kujerar. Kallon yarinyar take tana tuna kamar yau aka haifeta a gabanta, amma ta zo ta doke su a iya ƙulla kaidi. Wannan shi ne So Da Ramuwa.

“Bari na je na yi wankan da zai ƙarasa watsa tunaninsa.”

“Ganɗoki! Bari su ce miki sun taho mana.”

“Okay”

Ta furta tana komawa ta zauna, har yanzu da murmushi a fuskarta.

Ba daɗewa wayar ta ƙara ringing.

“What!”

Ta furta tana miƙewa tsaye.

“Waye wannan ɗin da ya ja shi.”

“Ina na sani, ni ma tunda na dawo na ga yana zuwa wurin.”

“Kai, me ya sa to baki bi su ba?”

“Oh kina so su gane ke nan? Duk da suna cikin maye baki san suna gane komai ba, Ni abin da bangane ba, ba dai Reza tamu yake cewa akai shi gunta ba?”

“Ba ita ba ce”.

Ta furta, tana kashe wayar.

Kafin kuma taja tsaki mai ƙarfi  tana huci.

“Idan wannan shirin ya ɓaci, zan ɓullo musu ta hanyar da banyi tunanin zuwanta kusa-kusan nan ba. Kinji wai ya sha giya da wani  ya ce masa ya kaisa ya ga Reza.

Reza! Reza!!Reza dai!!! Gaba ɗaya na rasa yadda zanyi da rayuwar yarinyar nan. Haba! Zanje in kashe ta kowa ya huta Linda. Ita kaɗai ce mace ne?”

“Haba ki share mana, zai zo yaga ƙanwarsa dai. Idan har yadda kika gaya min halinsa haka yake, ba na tunanin akwai abin da zai hana shi yadda Reza ba ƙanwarsa ba ce. Ke kin sani, ko takaddar can da muka sa Bio ya sa cikin file ɗinsu ai ta isa rufe tunaninsa.”

“Hakane.”

Ta furta tana janye tagumin fuskarta.

*****
HAMOUD

Da ƙyar suka samu ɗan Taxi da ya yadda zai kai su A Watse Quarters.

Tun daga Bypass yake zuga gudu da su kamar  yadda suka umarce shi, ya taho titin Zaria Road, ya yanka Kundila ya miƙe sosai yana shirin sauka daga titin ya ji muryar gayen.

“Kai tsaya-tsaya me ya kawo ka kusan unguwarmu?”

“Kan daidai muke Oga, ba A Watse ka ce ba?”

Ɗan Taxi ya furta da murmushi.

“To kuma sai ka biyo damu ta nan? Salon na ga gida na huce haushina kanka. Dillah sauka daga nan ka shiga wancan layin, ina son ganin Alhaji na.”

“Oga dare na yi fa, to shi ke nan dai”

Ɗan Taxi ya furta yana juya kan motar.

“Kai, Reza na ce ka kaini na gani fa.”

“Na ji ai Romeo, bari mu ƙarasa gida kaga Alhaji na dake kora ta.”

“Da ka share shi ai, irin dads ɗin nan sun faye yawa.”

“Bari dai na ganshi, zan ƙara jaddada masa banyi komai ba, ka gane ai.”

Shiru suka yi gaba ɗaya, har zuwa lokacin da suka iso nesa da wani babban gida, ya ce ɗan Taxi ya tsaya.

Fita ya yi daga motar yana layi zai ƙara sa gate din gidan.

“Ba ka ji ba oga…”

Ɗan Taxi ɗin ya furta yana leƙowa ta motar.

“Ga ruwa ka wanke kanka da fuskarka, bai kamata ka jewa mahaifinka a wannan halin ba”

“Kai fa ka faye yawa, share shi kawai, shi da ya ce ba ubana ba ne, ina so yaga yadda ya maida ni.”

Ya furta yana watsa hannu.

“Dan Allah mana…”

Ɗan Taxi ya furta a mararaice kamar wanda za a ga ƙanin ubansa.

Dawowa ya yi ya karɓi gorar ruwan. Ya tsiyaya ta tun daga saman kansa har wuyansa.

Girgiza kan ya yi da karfi, yana jin idanuwansa na washewa.

Murmushi ya yi ya miƙa masa gorar.

“Zuba wa wannan ɗan uwan nawa kafin na fito.”

A haka ya ƙarasa ya kwankwasa gate ɗin. Maigadi ya leƙo, da yaga shi ne sai ya buɗe da sauri yana ba shi hanya.
“Karka rufe.”

Ya furta yana ƙarasawa farfajiyar gidan.

Alhajin ya gani ya fito da baƙar jaka a hannunsa yana waya.

Tsayawa ya yi yana kallonsa a hasken lantarki da ya wadata wurin.

Kafin kuma ya toshe hanci yana kusantarsa.

“Giya ka sha Hammad? Giya fa?”

Baya ya yi ganin yadda yake tahowa a fusace.

Yana isowa gabansa, ya zube yana riƙe ƙafafuwansa.

“Wallahi wa billahil azeem ban satar maka komai, ka yi haƙuri.”

Kafar yasa ya dake shi kamar kwallo haka ya koma baya.

“Kana haukane zan yarda da rantsuwar ɗan giya? Kwana nawa na yi ina nemanka shi ne da ke ba ka da mutunci ba ka haihu cikin jinina ba, jiya ka ƙara shiga ka ɗauke min ɗayar jakar?”

A gigice ya ɗago yana kallonsa, ko da yake shan giya baya manta abubuwan da ya yi cikinta. Ta ya ya yanzu zai gaza tuna ya zo nan har ya yi sata, kai ƙarya ne.

“Wallahi ba Ni ba ne,  wannan sharri ne…”

Marin da aka zuba masa ne ya sashi yin shiru. Riƙo rigarsa ya yi yana miƙarsa akan ƙafafuwansa.

“Wa ne yasan lambobin sirrin da ake buɗe makzan ɗi na idan ba kai ba? Wancan karan na ga agoganka a ɗakin ka ce ba kai ba ne shi yaje da ƙafafunsa.

Yanzu kuma wannan da na gani jiya, tsuntsuwa ya yi ya shiga ta window halan?”

Ya furta yana tura hannunsa a aljihu, ya zaro zoben azurfa.

“…Ko kuwa ba azurfar da na kawo maka daga Saudiyya ba ce?”

“Ita ce, amma ba ni ba ne, karka kore ni, ka ba ni kwana uku na maka alƙawarin zan kawo maka ɓarawon, idan ban kawo shi ba ka min duk abin da kake so…”

“Ka mini shiru Hammad! Gwara da kazo ai, dama yanzu na gama waya da waɗanda za su koya maka hankali. Ina nadamar ɗaukan ka da na yi na riƙe wallahi, da na sani na barka acan ka zama sarkin noma. Shashasha kawai”

Shirun ya yi, yana jin yadda gabaɗaya kansa ya kwance. Tabbas  Zoben sa ne, sai dai shi kansa ya rasa yadda akai ya bar hannunsa.

Ko shekaranjiya da yake Cheesy Bar ya kula da shi a hannunsa, sai dai bai san kuma ta yaya shaf ya mance da shi ba, kai ba ma wannan, da gaske ke nan Alhaji riƙe shi ya yi? Ba shi ne mahaifinsa ba. Ɗagowa ya yi yana kallonsa da idanuwansa da suka kaɗa jawur kamar gauta.

“Ba kai ne mahaifina ba?Shi ya sa Hajiya ta mini haka?”

Fasa kai wayar kunne ya yi ya tsaya yana kallon yanayinsa. Lokaci ya yi da ya kamata ya san asalinsa duk da bai zo ta yadda yake so ba. Ya so sai ya ga mahaifiyarsa da yake jin tana  raye, amma shegen yaron ya zo ya ɓata masa shiri. Ya taɓa dukiyarsa da baya haɗa komai da ita.

Tausayinsa da yake ji ya kawar, ya sai ta idanuwansa kan nasa yana hura hanci.

“Dan kwal ubanka wane uba ne zai kori ɗansa? Ko kuma wane ɗan ne da ya haifu cikin ubansa zai masa sata?Me Hajiyar ta maka? Ka fito da duk jakunkunan da ka ɗauka, na faɗa maka komai a nutse. Idan ba haka ba yau kwanan kanta za ka yi. Ka ji dai na rantse.”

“Ban ɗauka ba.”

Ya furta da ƙyar yana danne baƙin cikin dake taso masa.

“Ka gaya mini wanene Mahaifina? “

“Ubanka ne, na ce ubanka ne mahaifinka, kai kaji ɗan gwafar uba, ina cewa ka fiddo min da jakunkunan kuɗi na, kana tambayata wani da ƙasa ta rufe. Bari dai ka gani.”

Ya furta, yana ɗora wayar sa a kunne.

“Hello! Officer, ga yaron nan ya dawo. Ka turo yaran naka su wuce da shi.”

“Okay, ba za a bari ya tafi ba.”

Baya-baya Hammad ya fara yi, babu yadda za ai ya tsaya ‘yan sanda su tafi da shi kan lefin da ya san bai yi ba.

Dan haka ya juya a guje yana dosar gate ɗin dake buɗe.

“Kai! Kai!! Kai Hamza karka bari ya fice, rufan ƙofar!!!.”

Inaaa! Tuni ya bangaje ɗan jemammen maigadin, ya ƙarasa ga Taxi ɗin da suka zo.

“Kai tayoyinka masu kyau ne.
“Eh oga sabbi ne.”

“Fito ka koma baya, ba Ni na ja mu.”

Da sauri ya fito jin muryar wani na doso su.

Shiga ya yi mazaunin direban ya bawa motar wuta, ya fige ta da wani irin gudu.

Alhajin ma direbansa ya kira, ya shiga tasa motar suka rufa musu baya.

Wayarsa a kunne yana jaddadawa ‘yan sanda su yi sauri su iso, shi ya fara bin bayan yaron.

Yana sane da motar Alhaji dake binsu, dan haka ya dinga musu yawo da hankali. Har sai da yaga kamar sun ɓace mata, tukunna ya saita hanyar, yana nufar A Watse Quarters.

A hankali ya ƙara so daidai gurin da ya ɗauki motarsa rannan. Parking ya yi, ya waigo yana kallon Hamoud da duk abin nan da suke yi ƙansa na ƙasa, ya dafe shi da duka hannuwansa biyu. A tun lokacin da ɗan Taxi ya zuba masa ruwa.

“Abokina mun iso, fito”

Ɗagowa ya yi yana hango gidan, gidan da matar da aka kira da mahaifiyarsa ke ciki.

Ji ya yi kamar ma ƙafafuwansa sunyi sanyin da ba za su iya ɗaukar nauyin sa ba.

haka ya daure ya fito yana dafe motar. Yana jin kamar kansa zai tsage biyu.

Hammad ma ya fito yana kallon ɗan Taxi ɗin, bai san kalar godiyar da zai masa, dan haka kawai ya miƙa masa hannu, shi ma ya miƙo suka jinjina. Hannu ya sa a aljihu ya zaro wallet ɗinsa. Kuɗi ya zaro ya kai dubu biyar (5,000)ya ba shi.

“Ka yi hakuri, na sani abin da ka mana ya fi ƙarfin wannan abin, sai dai suke nan gare ni.”

“Ah haba Oga, sunyi yawa ma ai. Godiya nake fa.”

“Yawwa, karka koma ta inda muka shigo nan, ka miƙe can, ka fita ta baya.”

“Ba damuwa Oga.”

Ya furta yana mai komawa cikin motarsa.

Hamoud ya tallafa ganin kamar ba zai iya tafiya ba. A haka suka doshi gidan.

Gate ɗin a buɗe yake, duk da kuwa dare ya yi sosai. Ba su damu  da ganinsa hakan ba suka ƙarasa ƙofar falon.

Tun kafin su kwankwasa ƙofar ta buɗe. Matashiyar budurwar ta fito  kamar an koro ta, suka tsaya cirko-cirko suna kallon juna.

Idan ba ƙarya ta yi ba, tana jin ta kira wayar Hamoud sau ɗari da cas’in da biyu, amma ba ta same shi ba. Ta gama fidda rai, yanzu kuma da Ikon Allah ta juyo motsi. Da fitowarta kuma gashi a gabanta.

Jikinsa ta faɗa ta cukwikwiye shi tana sakin wani rikicaccen kuka.

“Na gama fidda rai, ina jin kamar ba zan ƙara ganinka ba.”

Ƙoƙari yake ya zare ta daga jikinsa amma ya kasa, ji ya yi ta masa wani irin nauyi.

Hammad da ya yi tsaye gefe yana ganin ikon Allah ya matso.

“Juliet, ni fa a siraɗi nake, maɓoya nake so.”

Ɗagowa ta yi tana kallonsa jin ta san Muryar. Ga mamakinta kuya shi ne, mutumin nan dai data taimaka ya kwana gidansu, ya tafi ba ko godiya.

Damuwar da take ciki ba za ta barta magana ba, dan haka ta nuna masa ƙofar, ya shige.

Ita kuma ta jawo hannun Hamoud, tamkar raƙumi haka ya bita.

Idanuwansa yake watsawa a falon, a haka har ya hangota can gefe zaune saman kujerarta.

Bai san yana takawa zuwa gabanta ba sai da ya ji ya zube kan gwiwowinsa a saitinta.

Hannuwansa ya ɗora saman cinyoyinta. Yana jin wani ƙarfi dake ta so masa da zai iya ɗora idanuwansa kan nata. Hawayen da suka daɗe da ƙamewa suka zubo, suna sauka kan hannunsa da ke cinyoyinta.

“Da gaske ke ce mahaifiyata?”

Da jin yadda kalmomin suka fito, zaka gane ba ƙara min ƙoƙari ya yi gurin haɗa su ba.

Fuskarta ke nuna zallar tausayinsa da take ji. Ita kanta idanuwan nata cikowa ta ji suna yi. Wani ƙulli ne ya dunƙule mata a maƙoshi. Godiya take ga Rabbil Izzati da ya jarrabe ta da wannan ciwon, wanda ko magana ba za ta iya yi ba a lokacin da aka fi buƙatar da ta yin. A haka ta yi ƙoƙarin juya kanta dama, tana son nuna masa shi ko kusa bai yi kalar ɗanta. Mahaifin ɗanta Wada ne, ke nan ita ma Wada za ta haifo. Ba irinsa da yake da tsayi har na siyarwa ba. Ita a ƙauyensu ta haihu, a cikin ɗakinta. Ba wai asibiti ba, asbitin ma a Ghana.

Soupy ce ta matso, ta sa hannu ta miƙar da shi tsaye tana girgiza masa.

“Ba mahaifiyarka ba ce, sharrin maƙiya ne.”

Wani watsattsan kallo ya mata da ke nuna kamar ya?

“Ka yarda, duk abin da ya faru sharrin Fakriyya ne. Ita ta yi amfani da likitan dan ta haramta auren ku…”

“Ke! Ya furta da tsawa yana matsawa daga gabanta.”

wannan ba, ko kun san  na ga shaida? Mahaifina ya saka hannun a takardar da akai yarjejeniyar saye na. Ba fa kowane zancen banza nake ɗauka ba.”

Shiru suka yi gaba ɗaya ana kallon-kallo tsakanin Soupy da Reza.

“Ku gaya mini mana!”

Da sauri Reza ta taho gabansa.

“Abin da Soupy ta faɗa maka shi ne gaskiya. Bari ka ji ta yadda muka gane, ba wai haka kawai za mu mata ƙarya ba.”

Tiryan-tiryan ta kwashe duk abin da Gisma ta jiyo ta gaya masa. Ta ƙara masa da nasu nazarin.

“Nooo! Stop it!! Please!!! Ba za ta mini haka ba, Fakriyya tana so na ba za ta tozarta Ni ba. Ƙarya ne wannan.”

Ya furta da ƙaraji yana tushe kunnuwansa.

“Ina faɗa miki na ga shaida a cikin takaddun Mamyn. Ba zai yiwu ita ba. Kawai ta ji abin da ya faru ne take so inje gunta.”

“Hmmm! Hamoud ina mamakin yadda kake ikirarin ba  Fakriyya  ba ce, wallahi ta wuce dukkan tunaninka, anji tana sonka. Menene hikimar sawa a ɗauko ka cikin  rashin hayyaci? Kana ta maganar takarda, idan na ce maka sawa ta yi a shiga har ɗakin Mamyn a duba inda take aje files ɗin nata, a ajiye takaddar a ciki za ka yarda? Ta ya ya duk kwanakin da ka share da Ree baka san kalar wayonta ba?”

“To kinga an ɗauko nin ne? Ina ce Ni na kawo kaina nan. Kina ta maganar za a shiga cikin gidanmu a aje takaddar, duk ina tsaron gidan? Duk ina camera din da suka cika ɗakin Mamyn? Kina nufin suna barci aka saka ke nan ko?”

“Eh suna barcin..!!!”

Ta furta a fusace tana ƙara takunta zuwa gabansa.

“Na ce suna barcin tunda kai ka manta lokacin da muka keta alfarmar gidan naku muka shiga. Duk ina tarin CcTVn da kake ikirarin.”

Shiru ya yi yana kallon cikin idanuwanta da suka kaɗa da ɓacin rai.

Girgiza kai ya yi kafin ya furta abin da yake son, ta tari numfashinsa.

“Kamar kafi yarda da Fakriyya a kaina Hamoud? Ni da Soupy, ka duba girman shekarunta ta faɗa maka magana ka ture. Ga na mahaifiyata ina gani ta motsa maka kai amma ka ƙi fahimtar ta. Ban za ci soyayyar Fakriyya ta toshe duk wani tunaninka irin haka ba.”

Buɗe bakin ya ƙara yi zai yi magana bugun ƙofar ya hana shi.

Kafin kuma a turo ƙofar da ƙarfi ana shigowa falon.

“Gashi nan, ku riƙe min shi. Saboda tsabar ya gama lalacewa a gari kalli unguwar da ya zo. Ni da duk zamana cikin Kano ban taɓa jin ko sunanta ba.”

Hammad dake zaune gefe yana ta kallon rikici, ya yi wata irin alkafira yana komawa bayan Hamoud.

Reza ta ɗago tana ƙarewa Alhajin kallo, fari ne me tarin gashin gemu. Gajere ne sosai, dan da kaɗan yafi Wada tsayi. Sai dai, ba wadan ba ne, tunda idan suka jera da Soupy za su zo kai ɗaya.

“Oga ka yi haƙuri, ta inda ka ce na fitan na bi, ashe sun tsaya can gefen titin da muka bar su. Sun kuma gane motar tawa. Kawai ji na yi sun yi ram! Da ni, dole suka sa na kawo su nan ɗin.”

“Rufan baki algungumi. Tafi ko nasa a haɗa har da kai.

Sum-sum Direban ya juya ya fice.

Matsowa ya yi ya danƙo hannun Hammad ɗin yana jawo shi. Ya kallo ‘yan sandan biyu dake tsaye bayansa. Kan ya buɗe bakinsa Soupy ta yi saurin shan gabansa.

“Haba Alhaji, haka ake shiga gidan mutane ba neman izini ba, ba sallama, ko naka akai wa haka ai ba za ka ji dadi ba.”

Wani kallo ya mata sheƙeƙe yana mamakin kalar gajartar ta.

“Wannan wurin naku har wata sallama ake yi? Na ɗauka ai kowa ke da tikitin shiga tunda an gaya min unguwar babu wani me  igiya cikinta.”
“Amma a shari’ance ina da ikon da zan kai ƙararka kan ƙetara min gida da ka yi, ka fita daga nan, ka kuma saki yaron nan, duk sa’adda ka ganshi a waje kana da ikon kama shi, amma ba anan ba.”

Baki ya saki yana mamakin ƙarfin halinta, har bai san sa’adda Hammad ya kwace a hannunsa, ya gudu wata ƙofa da yake hange kusan Mama Ashana.
“Na faɗa maka ban ɗaukar maka komai ba, sharrin Hajiya ne kawai, bantaɓa gaya maka ba ne, amma tun ina yaro banjin daɗinta. Yanzu kuma ta zo wai na auri Humaisa, ƙanwata fa, ai wai ita riƙe Ni ta yi dama, kawai fa dan taji ka mallaka min wannan kamfanin. Shi ke nan dan naki suka fara ƙalla min sharri. Wallahi ba zan taɓa ma sata ba, ko da da gasken baka haife ni ba.

Hammad ya furta yana ƙoƙarin buɗe ƙofar ɗakin ya shige.

Da sauri Alhajin ya zagaye Soupy zai nufe shi, da ɗaga ƙafarsa da saukar idanuwansa a cikin nata, duk basu gaza sakanni ba. A haka ya yi gaggawar dafe bango, jin ƙafafuwansa na gagara ɗaukar nauyinsa

Idan har zai manta wannan fuskar, dake zaune saman Wheelchair a gabansa, to tabbas zai manta adadin shekarunsa na duniya, hatta sunansa, yana jin zai iya mantawa. Wacce ya fara sanin so a kanta, a tun lokacin da ko alwala bai gama iyawa ba, ita ce gabansa, yarinyar nan dai da saboda ita ya baro ƙauyensu, a lokacin da ya yi nauyin bakin furta mata abin da ke zuciyarsa, har ta zama halaliyar ƙaninsa, ita ce dai zaune a gabansa. Dan ita ya bar ƙauyensu, ya koma Zamfara State, bai sake dawowa ƙauyen ba, sai bayan shekaru biyar da yaji mutuwar ƙaninsa, ya zo ya ɗauki Hammad, ya riƙe, domin kawai ya rayu da halaliyar abin da ya taɓa so. Ko a labari, bai sake jinta ba, duk da ya ji ƙishi-ƙishin ta zama karuwa a Lagos, a wancan lokacin da talauci ya masa ƙatutu, ta ina zai fara nemañta?”

Da ƙyar ya iya haɗa sunan, ya furta su, suka zarce cikin kunnuwanta da wani irin kuwwa.

“Quraishiyya.”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Asabe Reza 20Asabe Reza 22 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×