Skip to content
Part 1 of 25 in the Series Bakar Kaddara by Haiman Raees

Matashiya

A wata duniyar can ta daban, akwai ƙasashe, mutane, dabbobi, addinai, al’adu da sauran abubuwa masu kama da irin namu, kuma suna da zubi da tsari irin namu. Ko da yake mafi yawancin al’amuran da ke faruwa a cikin wannan duniyar sun yi kama da irin namu, wasu abubuwan sun sha banban da namu. Akwai labarai masu tarin yawa da suka faru a cikin wannan duniya masu tarin abubuwan al’ajabi da ban mamaki, wataƙila ma mai karatu ya ji tamkar a cikin tashi duniyar suke faruwa, sai dai a zahiri al’amuran na faruwa ne a wata duniyar can ta daban. Kuma a cikin wannan duniyar ce muka kawo muku labarin Haidar na birnin Sahara da kuma labarin Malam Jatau. Yanzu kuma za mu koma wani ɓangare ne na daban a cikin wannan duniya domin kawo muku wasu sabbin gajerun labarai. Mai karatu, shigo cikin wannan duniya mai kama da tamu ka sha labari.

*****

Shiga Uku

Sani mutum ne mai fara’a da faran-faran da jama’a a kowane lokaci. Dogo ne baƙi mai matsakaicin jiki. Kusan ko da yaushe za ka taras da shi sanye da farin tabarau a fuskar shi. Allah ya yi wa Sani son jama’a da kuma son taimakon masu ƙaramin ƙarfi. Sani yana aiki ne a wani kamfanin sumunti a matsayin Akawu, kuma yana kula da aikin shi sosai.

Yau ranar Litinin ce, don haka sani ya shirya tsaf domin zuwa wurin aiki tun da sanyin safiya. Matarsa Karima ita ma a shirye take saboda tare za su fita, ita za ta tsaya ne a asibiti domin yin gwaji saboda ta shiga watan da ake sa ran za ta haihu. Saboda saurin da suke yi ko addu’a babu wanda ya yi daga cikinsu kafin su fita. Suna tafe suna hirar su gwanin ban sha’awa, Sani na zolayarta wai ta fishi ƙiba. A haka dai suka isa har ƙofar asibitin, a nan sani ya sauke ta shi kuma ya wuce wurin nashi aikin.

Ko minti biyar bai yi ba da sauke ta, yana cikin tafiya, bai yi aune ba kawai sai ji ya yi wata mota ta zo ta buga wa tashi. Nan take gaban motar ya molaƙe, fitilun suka farfashe. Rashin saka seat belt ya sa kanshi ya bugu sosai da sitiyarin motar. Allah dai ya kiyaye bai ji rauni ba. Nan fa mutane suka zo aka taimaka mishi ya fito daga cikin motar da ƙyar. Daga nan aka kwashe su sai ofishin ‘Yansanda inda aka ba wa wancan direban rashin gaskiya, domin shi ne ya shigo hannun Sani da nufin ya yi overtaking. Bayan an yi wasu ‘yan rubuce-rubuce sai ‘Yansandan suka kulle wancan direban shi kuma Sani ya roƙi alfarmar a bashi dama ya tafi wurin aiki in ya so sai ya dawo daga baya. Hakan kuwa aka yi.

Tun daga ƙofar shiga kamfanin ya fahimci cewa akwai matsalar da ta faru, domin kuwa ga wasu daga cikin abokan aikinsa nan da yawa sun yi cirko-cirko kamar zakaru. Yana ƙarasawa kuwa ya ga ashe mai kamfanin ne da kanshi ya zo, kuma duk waɗanda ke tsaye a wurin su ma makarar zuwa wurin aiki suka yi. Suna gama taruwa kuwa ya kira manajan kamfanin aka yi lissafin kwanakin aikin da suka yi aka ba kowa nashi sannan ya ce ya kore su gaba ɗaya daga kamfanin. Sani ya yi magiyar duniyar nan kan cewa shi bai taɓa makara ba sai yau, amma ina, ko kula shi bai yi ba.

Haka nan ya fito daga kamfanin jikinsa duk a sanyaye. Yana fitowa ne kuma sai ga kira daga asibiti, matar shi ta fara naƙuda, haihuwar ta zo mata da wuri. Nan fa ya yi maza-maza ya nufi asibitin kamar zai haukace. Da zuwa aka ce mishi ba za ta iya haihuwa da kanta ba dole sai an yi mata aiki. Nan take ya sa hannu a takarda aka yi aikin. Bayan an kammala aikin, matar Sani ta rayu, amma ɗan ya zo babu rai. Abun duniya fa duk ya taru ya yi mishi yawa. Yayar shi Marka da wasu daga cikin ‘yan uwan matarshi suka yi ta mishi jaje, wasu kuma dama sun zo asibitin Haka nan ya ɗauki gawar jinjirin ya nufi gida da shi domin a binne shi. Yana zuwa gidan ya taras da wata tifa ta ƙwace tun daga kan hanya ta zo ta daki wani ɓangare na gidan ya rushe. Direban motar ya gudu kuma wasu daga cikin ‘yan ɓata gari har sun shiga gidan sun yi mishi sata. Abin kuma ya wuce tashin hankali yanzu. Sai dai salati kawai. A daddafe dai da taimakon jama’a aka yi jana’izar yaron kuma aka dangace sashen gidansa da ya rushe da tamfol.

Ana cikin hakan kuma, kwatsam sai ga kira daga ofishin ‘Yansanda akan ya je wai sun duba motar shi basu gani ba. Abubuwa dai sai ƙara rincaɓewa Sani suke yi. Ya ma kasa hawa ko da Napep ko mashin. A ƙafa kawai yake tafiya tare da lissafa irin munanan abubuwan da suka faru da shi daga safiyar yau zuwa yanzu. ‘Wannan wace irin baƙar ƙaddara ce ta faɗo min haka?’ Ya tambayi kansa ba don yana da amsar bayarwa ba. Yana cikin tafiya sai ya ga wata ‘yar bishiyar mangwaro a gefen hanya, sai ya je ya zauna a gindinta da nufin ya ɗan huta. Zamansa ke da wuya kuwa sai wata kunama ta ɗana mishi harbi. Cikin firgici ya miƙe zumbur yana salati, bai ankara da wata mota da ke zuwa ba kawai ya faɗa kan titi yana soshe-soshe. Bai ankare da me ke faruwa ba kawai sai ji ya yi wani abu ya yi gaba da shi, yayin da wani irin duhu ya mamaye ganinsa.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.3 / 5. Rating: 8

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Bakar Kaddara 2 >>

10 thoughts on “Bakar Kaddara 1”

  1. ammarharunagumau@gmail.com

    Lallai wannnan labarin cike yake da ban tausayi,Allah ya raba mu da baƙar ƙaddara, hakika rayuwar Sani akwai ban tausayi….amma anya ba duk rashin addu’a bane sanadi?

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×