Skip to content
Part 2 of 25 in the Series Bakar Kaddara by Haiman Raees

Karshen Alewa

An yi wata yarinya mai suna Husna. Duk da cewa gidansu ba wasu wadatattu ba ne, Husna ta samu gata bakin gwargwado a wurin iyayenta, musamman ta fannin iliminta na addini da na zamani baki ɗaya. Haka kuma sun yi iya bakin ƙoƙarinsu wajen ba ta tarbiyya irin wadda ta dace. Kasancewar ita kaɗai iyayenta suka haifa, basu da burin da ya fi ganin farinciki da annashuwa a fuskar ‘yar tasu.

Haka rayuwa ta ci gaba da wanzuwa har zuwa lokacin da Husna ta kai munzalin aure. Da mahaifinta ya ga haka, sai ya dubi mutum salihi mai riƙon addini da kyakkyawar mu’amala ya zaɓa mata shi a matsayin mijin da za ta aura. Sai dai kash! Mugayen ƙawaye sun riga sun yi tasiri a zuciyar Husna ta hanyar kwaɗaita mata wata rayuwa ta dabam da wacce iyayenta suka ɗora ta akai. Don haka sai suka yi ta zuga ta tare da hure mata kunne akn kada ta sake ta amince da wannan bagidajen da da mahaifinta ya zaɓa mata. Shi kuma Shaiɗan dama kafa yake nema. Don haka sai ya dinga riya mata tunane-tunane masu matuƙar muni. A haka dai aka samu aka ɗaura auren nan da ƙyar. Ba jima ba kuwa sai Husna ta fara samun matsala da mijinta, rikicin yau da ban na gobe daban. Zaman lafiya dai ya gagara samuwa a gidan. A wani karo da maganar ta je kunnen iyayenta sai suka kira ta suna yi mata nasiha, amma sai ta ce ita dai atafau ba za ta zauna da wannan miji nata ba. Babu Irin Lallashin da iyayen nan basu yi mata ba amma ta ƙiji. Da abu dai ya ci tura, sai ya kwashe ‘yan komatsanta tdaga gidan mijin ta faɗa duniya. Aka yi ta nemanta amma ko wanda ya ji labarinta ma ba a samu ba.

Ita kuwa Husna, yayn da ta shiga duniya, kasancewar da sauran ƙuruciya a tare da ita, ga kuma ruwan budurci bayyane a jikinta. Sai ta kama ɗaki kawai ta koma zaman kanta. Nan da nan kuwa kwastomomi suka yi mata caa!! a kanta. Kafin a jima ta murje, ta goge, ta zama cikakkiyar ‘yar bariki. Ya zamana tana fantamawa yadda ranta yake so, rayuwarta gwanin ban sha’awa, har sauran masu sana’a irin nata suka fara jin haushinta saboda kishi. Ba a jima sunan Husna na gaskiya ya ɓace, in kana so a gane wacce kake magana akai sai dai ka ce Golden Girl.

Yau da gobe ta wuce wasa, kwatsam wata rana sai Husna ta kwanta rashin lafiya, aka yi maganin duniyar nan amma ciwo ya ƙi ci ya ƙi cinyewa. Duk waɗannan siffofin kyau, dirin jiki da kuma ruwan budurcin da ta ke taƙama da su gaba ɗaya suka zube. In ba wanda ya yi mata kyakkyawan sani ba babu mai iya gane ta. Ta koma abar ƙyama, domin har wari take yi daga kwance. A cikin wannan hali ne dai Allah maɗaukakin sarki Ya ɗauki ranta amma an rasa wanda zai mata wanka, balle kuma Sallah. Sai dai aka kira wani ɗan shaye – shaye aka biya shi ya ɗauketa a baro da dare ya kaita can wani tsohon rami a wani daji ya jefar da ita. Shi kenan ta faru ta ƙare, ita kuma ƙarshen tata rayuwar kenan.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.4 / 5. Rating: 8

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Bakar Kaddara 1Bakar Kaddara 3 >>

6 thoughts on “Bakar Kaddara 2”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×