Skip to content
Part 3 of 25 in the Series Bakar Kaddara by Haiman Raees

Ka Yi Wa Kanka 

An taɓa yin wani makaho a unguwar Na’ibawa da ke birnin Kano. Duk da kasancewarsa mabaraci, wannan makaho yana da wani irin abin mamaki. A duk lokacin da wani ya bashi sadaka ko kuma ya yi mishi wata kyauta, madadin ya yi godiya sai dai ya ce mishi ‘ka yi wa kanka’ kawai. Sunan wannan makaho na asali Haruna, amma saboda wannan ɗabi’a tasa ta aka daina kiransa da sunan shi na gaskiya sai dai ‘ka yi wa kanka’ kawai. Har ta kai ma dai in ba mutum ya daɗe da zama a unguwar ba ne, zai yi wuya ya iya faɗa maka sunan shi na asali sai dai Ka yi wa kanka.

Wasu jama’a da dama sun sha nuna mishi cewa wannan magana da yake faɗa kuskure ce, ya kamata ya daina cewa hakanan. A duk lokacin da wani ya faɗa mishi irin wannan batu, shi kuma sai ya ba shi amsa da cewa, ‘Duk abinda mutum ya bayar kansa yake yi wa, haka ma in ya hana. Ni kawai tunasar da shi nake yi ta wannan hanya.’ daga nan sai mutane suka shafa mishi lafiya. Amma duk da haka wasu basa son irin wannan magana da yakan faɗi.

Akwai wata mata mai yara uku da ke wannan unguwa da makahon yake. Tana daga cikin irin mutanen da ba sa son irin wannan magana da yake faɗa, amma ba ta iya yi masa magana saboda shaƙuwar da ke tsakaninsa da yaranta. Sai dai abin na ci mata rai a duk lokacin da ta bashi wani abu ya ce mata ‘kin yi wa kanki’ saboda haka ta sa wa ranta cewa sai ta yi maganin shi.

Wata rana sai ta siyo zoɓo musamman ta saka guba a ciki ta je ta ba wa wannan makahon domin in ya sha ya mutu kowa ya huta. Shi kuwa ko da ya karɓa sai ya ce mata ‘kin yi wa kanki’ kamar yadda ya saba. Ita kuwa sai ta ayyana a ranta cewa, ‘yau za mu ga wanda ya yi wa kansa tsakanin ni da kai.’ Daga nan sai ta tafi abinta. Shi kuwa sai ya ajiye wannan zoɓo a gefe da nufin in rana ta yi ya ji ƙishi sai ya sha. Yana nan zaune a inda yake, har ya ma manta da wannan zoɓon, sai ga ‘ya’yan wannan mata da ta kawo mishi zoɓon sun dawo daga makaranta. Dama sun saba tsayawa wurinsa su gaisa. Yau ma kamar kullum sai suka tsaya suna da zolayar shi suna raha. Can sai ɗaya daga cikin yaran nan ya ga zoɓon, ya kuwa nuna yana so. Shi kuma makahon ya ɗauka ya basu, suka yi godiya sannan suka wuce gida, suna tafiya suna sha.

Suna shiga gida uwar ta gansu da robar zoɓon sai ta ruɗe, ta hau tambayar inda suka samo robar, su kuwa suka faɗa mata malam makaho ne ya basu zoɓo kyauta. Nan da nan a firgice ta ɗauke su suka nufi asibiti. Kafin su ƙarasa rai ya yi halinsa.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.4 / 5. Rating: 9

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Bakar Kaddara 2Bakar Kaddara 4 >>

4 thoughts on “Bakar Kaddara 3”

  1. Lallai ya faɗi gaskiya.
    Da ta ƙi ɗacin gaskiya, ai ta ci ɗacin rashi.

    Allah ya ba mu ikon karɓar gaskiya ko mai ɗacinta.

    Shukran Allah ya ƙara basira da ɗaukaka.

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×