Tsautsayi
Hausawa kan ce, 'Biki wan shagali'
Suna kuma ƙanin biki ne.
Kamar yadda aka saba, a mafi yawancin sassan ƙasar Zazzau da maƙwaftanta, a duk ranar da ake yin suna, wato ranar da jariri ko jaririyar da aka haifa ya cika kwanaki bakwai. A kan yi fate ne da tuwo domin mahalarta taro. Sai dai yanzu da yake zamani ya canza, akan haɗa da shinkafa domin sirkawa.
Yau na dai haka abin yake. Yau ce ranar da ake suna a gidan Malam Sallau da ke ƙauyen Kyamfa. Wannan kuwa ita ce. . .