Skip to content
Part 17 of 25 in the Series Bakar Kaddara by Haiman Raees

Na Kashe Su

Hankalin Ilham in ya yi dubu ya gama tashi. Wani irin fitinannen gudu Shamsu yake yi da su kamar wanda zai bar duniyar. Babban abin da ya fi ba ta mamaki shi ne irin yadda shi ko a jikinshi, bai damu da ko a wane irin hali suke ba. Da alama ma ya manta cewa daga asibiti suka dawo.

Kwanan ta biyu kenan ba ta da lafiya, rashin kuɗi da matsin rayuwa ya sa basu samu damar zuwa asibitin ba sai yau. Shi kuma jaririnta da bai wuce wata shida ba a duniya, gudawa ce ta kama shi. Da alama haƙori ne zai fara fito mishi.

“Don girman Allah Abban Sadik ka rage gudun da kake yi.”

Ilham ta faɗi da ƙarfi saboda ya ji. Domin a irin gudun da yake yi, ba kowace irin magana bace za a yi ya ji. I’m ma ya ji ɗin, to bai nuna ma. Ci gaba kawai ya yi da ba wa babur ɗinsa wuta ba tare da ya tsagaita ba. Haka ta yi ta mishi magiya amma ya yi biris da ita.

Suna cikin tafiya kuwa, sai wani ɗan Akuya ya gitta ta kan hanyar a guje. Nan fa Shamsu ya yi yunƙurin kauce mishi. Ƙarfin gudun da yake yi ne ya hana shi damar yin hakan. Maimakon hakan ma, sai babur ɗin ta ƙwace daga hannunsa. Ai kuwa take ya yi cikin wani kwalbati da su. Ilham ba ta ankare ba sai ji ta yi kawai an yi sama da ita. Kai ka ce jifa aka yi da hoge. Kawai sai ta tsinci kanta tana mai tafiya a sararin samaniya, daga baya kuma ta faɗa jikin katangar wani masallaci da ke kusa da titin da suke tafiya a kai.Nan take kuwa kanta ya fashe, jini ya fara shatata.

Shi kuwa jaririn da ke bayanta tuni ya suma. Ko da ganin faruwar hakan, sai ta yi tsammanin ya mutu ne. Nan fa ta ruɗe, hankalinta ya tashi, ta rungume yaron tana wani irin kuka mai tsima zuciyar duk wani mai imani. Uwa kenan! Ita ko ta raunukan da ke jikinta ma ba ta yi, duk kuwa da cewa har yanzu sun kasance suna masu zubar da jini.

Shi kuwa Shamsu, babu ɗin da ta ƙwace sai ta yi cikin kwalbati da shi kuma ta danne shi. Ba ka jin komai sai ihunsa tare da kururuwar neman ɗauki. Da ƙyar jama’ar da ke wurin suka taimaka wajen zaro shi. Daga nan kuma babu abin da yake fitowa daga bakinsa face,

“Na kashe su! Na kashe su!! Na kashe su!!!”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Bakar Kaddara 16Bakar Kaddara 18 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×