Ramin Mugunta
"Habiba ki yi sauri fa. Za mu makara!"
"To Maigida."
Ita dai Habiba ta rasa dalilin wannan sauri nasa. Tun jiya ya ce mata za su je wani wuri da sassafe. Kuma ya ce kada ta ci komai kafin su fita tunda ba daɗewa za su yi ba. Ya ce in sun dawo sai su karya gaba ɗaya a nutse.
Habiba ta yarda da mijinta sosai. Hakan ya sa ba ta kawo tunanin komai a ranta ba. Ta kuma tashi da wurwuri ta shirya domin yin wannan tafiya da ba ta san ko. . .