Skip to content
Part 25 of 25 in the Series Bakar Kaddara by Haiman Raees

Ramin Mugunta 

“Habiba ki yi sauri fa. Za mu makara!”

“To Maigida.”

Ita dai Habiba ta rasa dalilin wannan sauri nasa. Tun jiya ya ce mata za su je wani wuri da sassafe. Kuma ya ce kada ta ci komai kafin su fita tunda ba daɗewa za su yi ba. Ya ce in sun dawo sai su karya gaba ɗaya a nutse. 

Habiba ta yarda da mijinta sosai. Hakan ya sa ba ta kawo tunanin komai a ranta ba. Ta kuma tashi da wurwuri ta shirya domin yin wannan tafiya da ba ta san ko ta zuwa ina ba ce. Kuma kamar yadda ya umarta, ba ta ci komai ba. Suna gab da fita ne ta ji kwaɗayi ya taso mata. Abinka da mai yaron ciki. Sai ta ɗauki yalo guda biyu ta ci ba tare da ya sani ba sannan suka fita. Dama tun jiya ta aika aka siyo mata da rana. Kwana biyu kuma shi kawai take sha’awa. 

Shi kuwa bai taɓa tunanin zai ce mata ta yi abu kaza ta ƙi yi ba. Sabo da ya santa da matuƙar biyayya. Duk abinda ya ce ta yi masa shi take yi. Wannan dalili ne ya sa shi sakin jiki tare da shiga yanayi na ɗumbin farincikin da bai taɓa shiga irinsa ba. Don ya san cewa lokaci ya yi da shi ma zai fita daga cikin ƙangin rayuwar da yake ciki. Shi da kanshi ya buɗe motar abokinsa da ya aro suka shiga suka kama hanya. 

Tun da ya hau kan hanyar basu wani yi magana sosai ba. Ita dai habiba tana ganin ikon Allah. Idan ya bi wannan layi, sai ta ga ya juya ya shiga wani. A haka dai har suka shigo wani layi mai faɗin gaske. A ƙofar wani katafaren gida suka sauka. Bayan sun ƙwanƙwasa ƙofar, sai mai gadi ya fito suka gaisa. Da alama ya san da zuwansu, sabo da haka ya buɗe musu suka shiga tare da barin motar a waje. 

Gidan yana da faɗi, ga fulawoyi nan birjik da sauran kayan alatu. Sai dai kuma ba su ga kowa ba har suka shiga babban falon gidan. A nan ne mijin Habiba ya danna wani madanni sau biyu sannan suka zauna. Ita dai ba ta ce komai ba. A zahiri inda za a tambaye ta za ta ce tsoro ne ya dabaibaye ta. Ba su jima da zama ba sai wasu ƙarti su uku sun fito ta wata ƙofa da ke jikin ginin ta gefen madannin da ya danna. 

Suna zuwa, ba tare da wani ɓata lokaci ba suka ce mishi, 

“Ita ce wannan?” 

“Eh ita ce.” ya basu amsa. 

“Ni ce wa?” Habiba ta tambaya a ɗan tsorace. Kafin ya ce wani abu tuni sun kamata sun yi gaba da ita. Ƙaraji take yi tare da kurma ihun neman taimako amma ko kallon inda take bai yi ba har suka shige da ita. Can bayan kimanin mintuna goma sha biyar sai gashi sun fito da ita. Wannan karon tare da wani mummunan mutum suka fito mai siffar bokaye. Jikinsa duk layu ne da wasu irin jajayen kaya da ya saka. 

A fusace ya dube shi ya ce, 

“Sai da muka ce maka ka tabbatar ba ta ci komai ba kafin ku zo. To ta ci wani abu, kuma tana da ɗan ƙaramin ciki. Don haka aikin ba zai yiwu a kanta ba. Amma kai tunda ba ka ci komai ba sai mu yi a kanka, don ba zai yiwu ba kuma a fara aikin a bari.”

Yana gama maganar waɗannan ƙartin suka yi gaba da shi yana ihu. Habiba kuwa da ke ta shesshekar kuka ta kasa cewa komai saboda tsananin firgita. Ji ta yi an turo mata wani abu kusa da ita, ta duba haka sai ta ga jaka ce babba cike da wani abu. Wannan bokan ya dube ta sannan ya ce, 

“Mu matsafa ne,mijinki ya kawo ki nan ne domin mu yi tsafi da ke mu ba shi kuɗi. Amma tsafin mu ba ya son mai ciki ko wadda ta ci wani abu da safe. Shi ya sa za mu ƙyale ki mu yi aikin da shi. Ga kuɗin nan sai ki kama gabanki. 

A firgice ta tashi ta wuce, ba ta ma iya ɗaukar jakar ba saboda tsananin tsoro. Waɗannan ƙarti ne suka kai ta har waje tare da kuɗin suka sa ta a motar sa suka bari a waje. Daga nan ba ta sake sanin inda take ba sai ganinta ta yi a cikin gidansu hannunta riƙe da jakar kuɗi. 

ALHAMDULILLAHI! 

Godiya ta tabbata ga Allah maɗaukakin sarki da ya bani ikon kammala wannan littafi mai suna Baƙar Ƙaddara. Masoyana masu karanta litattafaina ku ma ina muku godiya ta musamman. Ku ne ni, in babu ku, to tabbas nima babu ni. 

Na gode. 

Wasu daga cikin jerangiyar litattafai a ƙarƙashin Duniyar Labaran Haiman (DLH):

Birnin Sahara 

Fasaha Haimaniyya 

Malam Jatau 

Tambaya 

Baƙar Ƙaddara 

Dukkansu ana iya samun su a Bakandamiya Hikaya. 

Litattafai Masu Fitowa:

Kishiyar Kwali 

Dandi Ƙaho 

Karaya Uku  

Bidiri 

Tsibirin Al’ajabi 

Duniyar Labaran Haiman (DLH)

Labaran da babu kamar su.

#haimanraees 

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Bakar Kaddara 24

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×