Ka Yi Wa Kanka
An taɓa yin wani makaho a unguwar Na'ibawa da ke birnin Kano. Duk da kasancewarsa mabaraci, wannan makaho yana da wani irin abin mamaki. A duk lokacin da wani ya bashi sadaka ko kuma ya yi mishi wata kyauta, madadin ya yi godiya sai dai ya ce mishi 'ka yi wa kanka' kawai. Sunan wannan makaho na asali Haruna, amma saboda wannan ɗabi'a tasa ta aka daina kiransa da sunan shi na gaskiya sai dai 'ka yi wa kanka' kawai. Har ta kai ma dai in ba. . .
Lallai ya faɗi gaskiya.
Da ta ƙi ɗacin gaskiya, ai ta ci ɗacin rashi.
Allah ya ba mu ikon karɓar gaskiya ko mai ɗacinta.
Shukran Allah ya ƙara basira da ɗaukaka.
Amin. Jazakallah Khair.
Ya kuwa yi wa kansa. Allah ya tsare mu.
Amin. Jazakallah Khair