Skip to content
Part 8 of 17 in the Series Bakar Tafiya by Amina Abubakar Yandoma

Ihu Basma keyi tana naiman agajin su Jafar.

Lokaci guda ƙwalwarta ta fara tunano mata inda Ammar ya basu addu’a insun shiga bala’i.

“LA’ILAHA ILLAH ANTA SUBUHANAKA INNI KUNTU MINAZZALIMIN.”
Basma ta furta da ƙarfin gaske.

Tsunsun jiyayi kamar ya ta ɗauko garwashin wuta, bai bata lokaciba ya sakota ƙasa shida sauran ƴan uwanshi suka bace bat! Kamar basu ta6a wanzuwa a wurinba.

Duk da buguwar da Basma tayi sanadiyyar faɗowar da ta yi amma haka ta miƙe tana gudu tana ɗingishi.

Tun kafin dare yayi sosai suke gudu har saida duhun dare ya raba sannan suka zube suna maida numfashi.

“Wayyoh! Zani mutu, wayyo Umma na, na shiga ukku, shikenan mu haka zamu dawwama cikin bala’i muna mutuwa ɗaya bayan ɗaya, koda waɗan nan Aljanun basu kashemu ba yunwar cikin mu kaɗai ta isa tayi sanadin mutuwarmu, wayyo Ummana shikenan bazan ƙara ganinkiba.”Jamcy ta ƙarashe maganar tana harba ƙafafu a ƙasa kamar ƙaramar yarinya tana kuka.

Tk jiyayi kamar ya mangare Jamcy, amma soyayyar daya ke mata bazata bari ya iya yi mata komiba.

Dare ya raba sosai ga wani irin sanyi da ilahirin dajin ya ɗauka.

Matan su duka haɗe suke wuri ɗaya suna gyangyaɗi ga kyarmar sanyi sunayi.

Tk da Jafar wuri suka gyara da hannuwansu tareda kwantawa.

Wuri yayi tsit! Bakajin mitsin komi sai kuka tsuntsaye, bacci yayi nasarar sace su.

Cikin Bacci Basma taji kamar ana ja mata ƙafa, ƙara gyara kwanciyarta tayi.

Fizgar ƙafar akayi da ƙarfin gaske aka jawota daga inda take kwance.

Ƙara ta ƙala da tayi sanadiyyar farkawar su Jafar suka miƙe a firgice.

Wasu irin mulmula_mulmulan halittu masu kama da dodanni jikinsu duk gashi,ga wasu zara_zaran farata masu tsini, in ka kallesu sau ɗaya bakayi marmarin sake kallonsu ba saboda tsananin muninsu.

Kafin suyi ko ƙarin guduwa tuni dodannin sunyi nasarar kamesu sun sa awani keji, suka ɗauki kejin da hannu ɗaya suka ci gaba da tafiya.

Ihu kawai suke in banda Jafar da tuni bakinshi ya fara ambaton Allah da naiman agaji a wurinshi.

Tsawa ya daka masu wadda tayi sanadiyyar yin shirunsu.
“Bashakka ina ga mun kusa raba tafiyar nan daku, kuna ganin halinda muke ciki amma kun wage baki kuna wani kukan banza da bazai amfanemu da komiba, Shawara ɗayace muyi ƙokarin tseratar da rayuwarmu domin bashakka in muka bari dodannin nan suka ida isa damu lofa lalla mun zama nama cinyemu zasuyi.”

“Eh musan yadda zamuyi mu buɗe kejin nan mu kubutar da rayukanmu.”
Tk ya ƙarashe maganar yana ƙara riƙe hannun Jafar kamar za’a kwace mashi shi

“Amma abinda nike gani naga mun fara hango alamu kamar a kwai kogi nan gabanmu in muka buɗe saimu faɗa ruwan, abinda nasani dodanni basu san ruwa mu bari sai muna gaf da ida isa wurin sai muhaɗa ƙarfi mu buɗe ƙofar nan.”

Sun yi na’am da wannan shawarar ta Jafar, suna gani sun doshi gefen ruwan suka fara koƙarin tserewa.

Da ƙyar da ji6in goshi suka samu ƙofar ta ɗan buɗe yadda mutum zai iya fitowa daga cikin kejin.

Da ɗai ɗaya suka riƙa dirowa suna ficewa a guje, Mandiyace ƙarshen fitowa tana dirowa Dodan daya ɗauko kejin yaji kamar kejin ya rage nauyi.

Kejin daya gani a buɗe duk sun fice ya sanyashi wata irin kuwwa da sai da dajin yayi amsa Amo!.

Jin wannan ƙarar ya sanya sauran Dodannin rugowa domin sun fahimci naman da suka kamo ya sun tsere,agujsuka bi bayansu Jafar suna gudu suna daka wani irin tsalle tamkar ƙwaɗanni.

Gani irin azababben gudun da Dodannin keyi suna ƙoƙarin iskosu yasa su Jafar ƙara ƙaimi suna ƙoƙarin isa ga wannan kogi.

Sunyi nasarar isowa.

Tk ya fara isowa wani irin birki ya ja ya tsaya ganin irin zurfin da ke akwai kafin ka isa zuwa ciikin kogin, Jamcy na isowa batare da ta luraba ta banka Tk sukayi ƙasa, suma sauran baya suka mara masu.

Dodannin na isowa basu iske kowa ba, ganin haka ya sanya suka fasheda wani irin kuka daya sanya wurin amsa kuwwa.

Abinda ya basu mamaki kuma ya tsorata su shine ganin ƙasan ruwan haske fayau tamkar ba dareba.

Iyakar ƙarfinsu suke iyo amma abinda suka lura shine duk ƙokarin da suke suna nan tsaye a wurin da suka faɗo, wannan al’amari ya matuƙar ɗaga masu hankali.

Ga iskar da suka shaƙo ta kusa karewa.

Lokaci ɗaya ruwan ya fara wani irin motsi tamkar wani abu ya fao cikinshi.

Duk ƙoƙarin da suke amma a banza, sai da Jafar ya fara karanto addu’a cikin zuciyarshi sannan suka ga kamar an saki jijiyoyin jikinsu sun fara wuce wurin.

Tamkar an wulloshi haka suka tsinci Nura gabarsu kamanninshi su sauya yakoma Horror idanunshi babu ƙwayar baƙi sunyi fari tas!.

Kafin suyi wsni yunƙuri ya warci Mandiya yayi ƙasan ruwan da ita…

“Allahumma ajirnifiy musibati wa’aklifini khairan minha.”

Biba ta ƙarashe Addu’ar yayin da taga ƙofar na rufewa.

Tsaye suke ido ya raina fata, kowa ka kalla zaka hango tsananin firgici atattare dashi.

Ko ƙwaƙwƙwaran motsi bakaji kogon yayi tsit!

Jin motsi bayansu yadawo dasu daga duniyar tunanin da suka lula.

Kulu da Nas su suka farayin gaba sai Biba Rabson da Salma suka take masu baya.

Tunda suka fara tafiya basu haɗu da komi ba sai yana da ta dabaibaye ilahirin kogon sai sun sanya hannu sun ɗebeta sannan suke samu su wuce.

Abinda suka lura kogon wata irin doguwar hanya gareshi tunda suka fara bi har yanzu basu zo ƙarshenta ba.

Wani irin daddaɗan ƙamshin abinci hanci nansu suka fara shaƙo masu.

“Wow! Nas kaji abinda hancina ya jiyo mani?”

“Nima shinike jiyowa masoyiya.”

Sauri suka riƙayi tamkar zasu tashi sama, turus! Suka ja wani birki yawunsu na tsinkewa.

Abinci ne aƙasa cikin filattai jere reras!, shinkafa damiya hada naman kaji zuƙu_zuƙu.

Rabson wani yawu ya haɗiye ƙut! Tare da lasar la66anshi.

“Kada kuci abincin nan, wani tarko ne aka haɗa mana, kuyi tunani.”

Biba ta ƙarashe maganar tana riƙo hannun Kulu dake ƙoƙarin bin Nas daya kusa isa ga abincin.

“Malama sakar mani hannu, ke in bakici muki ƙyalemu muje muci iya cin mu.”

Ta fizge hannuta tayi gaba.

Salma gallama Rabson harara tayi.

“To jikan ƴan lasau, kaje kaci naga tun ɗazu sai lasar baki kake kamar sabon kamu.”

“Hhh! Haba my Salmaty na hanaki yawan magana fa, kinga yadda kike komawa bakinki har hawa yake kamar tsohuwa zata kira tukur.”

Ya ƙarashe maganar yana cigaba da dariyarshi.

“Bani da lokacinka marar aikinyi kawai mtsw!.”

“Niko nike da aikinyi, in zauna inta kallon bakinki yadda yayi suntum ɗin nan in kina magana tamkar yadda kikasan bakin aku haka kike komawa.”

Iya ƙuluwa Salma ta gama ƙulewa da rainin wayon Rabson, a fusace tayo kanshi tamkar zata kai mashi bugu.

Ihu Kulu ta fasa wanda ya jawo hankalinsu Biba.

Abincin da suka fara ɗiba ne ya koma tsutsotsi Nas da ya kai abincin cikinshi tuni ya baje ƙasa ko motsi bai yi.

Ihu take tana girgiza Nas Amma babu alamar zai tashi.

Biba ta matso tahau tofa mashi addu’o’i a hankali ya fara buɗe idanunshi, wata mahaukaciyar ƙasa da sukaji tasanya shi ida miƙewa tsaye.

Tsutsotsin ne suke haɗewa wuri ɗaya suna zama ƙatuwar tsutsa mai hannuwa bila adadin.

Salma da Rabson wuri ɗaya suka haɗe tana ihun kiran sunan dadyn ta shikuma yana kiran Wayyo Kaka wayyo bunsurunleee….

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Bakar Tafiya 7Bakar Tafiya 9 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×