Ta k'are maganar tare da murgud'a baki. Babu shiri ya fashe da dariya, irin wacce sai yabyi watanni ba tare da ya yi irinta ba. Saboda ya fi yawan murmushi mai sauti fiye da dariyar da za a ce ya yi har muryarsa ta tashi. Amma Munawwa ta saka shi yin irinta bai shirya ba, sai da ya yi dariyarsa son ransa kamar ta kashe wayar sannan ya ce,
"Am telling the truth, ki ba ta shawara idan har ta gyara halayenta za ta samu mijin kirki. Idan kuma ta ci gaba a haka to gaskiya akwai matsala. . .