Skip to content
Part 18 of 24 in the Series Bakon Yanayi by Hadiza D. Auta

Babu zato idanuwansu suka hango musu dank’areriyar motar sai k’yallin sabunta take yi, jikin Munara har tsima yake yi yayin da ta isa wurin ta fara shafa motar tare da fad’in

“Wowwww!”

Ta k’are maganar tana bud’e motar jikinta har rawa yake yi ta shiga ta zauna, farin ciki bayyane a kan fuskarta saboda yadda kyawun motar ya tafi da ita.

Mummy kanta motar ta burge ta sosai amma zuciyarta cike take fam da tunanin ta inda motar ta fito. Don ko fuskarta ba ta b’oye mamakin da take yi ba, har ta isa wurin motar sannan ta kai dubanta ga Munawwa ta ce,

“Ni fa kin sani a duhu Munawwara, daga ina wannan motar ta fito tare da wad’ancan tulin kayan da na gani?”

Munawwa a tsule take da fargaba, tare da tsoron abin da za ta fad’a, hannunta dafe da bakinta tana nazarin bayanin da za ta yi musu kai tsaye su fahimce ta. Hannunta duka biyu dafe da kumatunta idonta a kan motar ta ce,

“Wallahi ni ma Mummy abun ya bani mamaki sosai, wani fa ne daga had’uwarmu a chat; shi kenan ya ce zai zo gidanmu. Amma kafin ya zo sai gift d’insa ya riga zuwa, yanzu wannan kiran da kika ce Baba isah ya yi mini, shi ne fa ya aiko wani da sak’on ya kawo motar da kayan da ke cikin ledodin duka yace inji mutumin. Kuma ni wallahi Mummy ban ma san shi ba fa, kuma ban san a ina yake ba, amma kin ga wannan haukar da ya yi sai ka ce an saka shi dole.”

Mummy ta zaro ido hannunta a gaba, babu shiri ludayin miyar ya sub’uce a hanunta, sai k’arar faduwar shi suka ji. Munawwa ta duk’a ta d’auki ludayin yayin da Munara ta fito da hanzari tana k’are wa Munawwa kallo sama da k’asa tana girgiza kai sannan ta ce,

“had’uwar chat! Kuma ba ki san shi ba! Ko ganin shi ba ki tab’a yi ba, amma ya yi miki irin wannan kyautar? C hiab! To ai hankali ma ba zai tab’a d’aukar wannan zance ba, don ko a garin mahaukata ba a tab’a yin irin haka ba, balle mu ki zo ki raina mana wayo. WALLAHI da sake ‘yanmata, Mummy ki binciki ‘yar son ki da kyau, don kar ta je ta jawo mana bala’in da zai sa mu k’are rayuwarmu a prison, don wannan mota; ko Daddy bai kai matsayin da zai hau irnta ba ballantana har a ba ta ita matsayin kyauta, kyautar ma wai irin wannan ta rainin hankalin da na ji tana fad’a, saboda ta mayar da mu wasu jahilai.”

Tana k’are fad’ar maganganun ta yi wa Munawwa wani matsaiyacin kallon sama da k’asa ta buga wani k’aton tsaki, sannan ta bar wurin. Cikin gidan ta nufa tana ta sambatun cin mutunci da cin fuska ga Munawwara, tana zuwa wurin kayan dake ajiye cikin corridonsy ta saka k’afa ta shure ledar da ke gabanta, babu shiri ta ce,

“Wash! Allah wad’annan shegun kaya za su kassara ni.”

Mummy kam shiru kawai ta yi tana nazarin abin, sannan ta cire tagumin da ta yi ta ce,

“Mu shiga daga ciki kafin Daddyn naku ya dawo, amman kafin nan; ina son ki fad’a mini gaskiya Munawwara. Don ba na son abin da zai zo daga ba ya ya d’aga mana hankali muna zaman zamanmu lafiya.”

Tana maganar tana tafiya munawwa biye da ita a baya har suka kai inda kayan, Mummy ta duk’a ta d’auki leda d’aya, jin ba za ta iya d’aukarta ita kad’ai ba, saboda nauyinta ya sa ta ce da Munawwar ta rik’a su shiga da ita ciki. Nik’i-nik’i suka kama ledar suka kai d’akin Mummy, sannan suka dawo suka k’ara d’aukar d’aya suka kai.

Bayan sun ajiye ledodin ne Mummy ta koma kitchen ta zuzzuba wa kowa abincinsa, sannan ta dawo d’akin ta zauna kan gadon, inda Munawwa take zaune har lokacin ta yi tagumi da hannunta biyu, saboda zuzzurfan tunanin da ta faɗa.

Mummy ta kalle ta da kyau, ganin yadda jikinta ya yi sanyi ta kira sunanta a hankali da wata muryar tausayi, cikin nutsuwa ta ce da ita,

“Munawwara!”

Munawwa ta d’ago kai ta kalle ta tare da cire tagumin da ta yi ta ce,

“N’aam Mummy.”

Mummy ta sake kiran ta ta ce,

“Munawwara ina son ki yi mini bayani tsakaninki da ALLAH me kika sani dangane da waɗannan kayan da wanda ya turo da su?”

Munawwa kam jikinta ya k’ara yin sanyi k’alau, cikin sassanyar murya ta ce,

“Mummy kin san ba zan miki karya ba koda a ce ina yin ta, wallahi iya abin da kika ji na fad’a shi d’in dai ne, sai dai k’arin tambihin da zan yi miki a kan wannan lamari.”

Daga nan ta fara yi mata bayanin duk abin da ta sani tun daga kan text’s d’in da yake turo mata har chat d’in da suka yi da shi, sannan ta k’ara yi mata bayanin abin da zuciyarta take zargi, waton mai motar da take gani a kan hanya wanda zuciyarta take ta kai komo a kan zaton shi ne Nuradden d’in.

Mummy ta sauke k’atuwar ajiyar zuciya tsawon d’an lokaci tana tunani sannan ta ce,

“Dank’ari! Lalle wannan al’amari dole ne a yi bincikensa da kyau, yanzu ai kina da number’sa ko?”

Munawwa ta gyad’a kai, Mummy ta ce,
“To kira shi yanzu ki sanar da shi kin ga sak’o kin gode amman Iyayenki sun ce ba za a karb’a ba, har sai ya fad’a miki wane ne shi? Kuma a ina ya san ki?”

Munawwa ta jawo wayarta da ke kan gadon ta danna masa kira, don wannan shi ne karon farko da ta tab’a kiran shi, saboda ko muryarsa ba ta tab’a ji da kunnenta ba. Amma har ta katse bai d’auka ba, sai a na biyu ne ya d’auka cikin murmushin jin dad’i ya ce,

“Ina kan hanya idan na sauka za mu yi magana!”

Kit ya kashe wayar, sannan ta kalli Mummy da yake a hand’s free ta saka kiram, Mummy ta ce,

“To mu jira shi anjiman kafin Daddynki ya dawo, don mu san me za mu fad’a masa idan mun tashi.”

Munawwa tace, “To Mummy”

Munara da ke lab’e tana sauraronsu ta yi tsil ta shigo ɗakin da ‘yar fara’arta, wacce iya kacinta a fuskar, kai-tsaye ta ta nufi kayan tana cewa,

“Bari mu zo mu bud’a kayan mu kam mu d’ebe k’eyar idanuwa.”

Ta fara bud’a kayan tana fiddo su d’aya bayan d’aya tana mere, sai cillar da su take yi a k’asa, kamar wacce ta d’auko kashi. Amma fa a zuciyarta sai yaba kayan take yi, don dogayen riguna ne irin Arabians gawn d’in nan, sun ci kyau har sun gaji, stone d’insu da aka yi musu ado da shi sai walwalniya suke yi. Sai after dress na ji da fad’i tare da talkama kala kala da turaruka, set d’in sark’ok’i kala-kala da agoguna tare da da awarwaro.

D’ayar ledar kuma; turame ne manya-manya da lesussuka, tare da shaddodi gizner gizner har wani kyalli suke yi. Bayan kamfaloli manyan masu wani irin maik’o kamar an shafa masu mai.

A cikin tantama Mummy ta d’auki wani set d’in sark’a ta duba bakinta har rawa yake yi wurin faɗin,

“Gwal!!!!”

Daga Munara har Munawwara da sauri suka yo kan sark’ar suna rige rigen karb’a su gani, cike da mamaki Munara ta ce,

“Wai shi wannan mutumin ko ba ya da hankali ne ni kam! Anya wai ba d’anfashi ba ne?”

Mummy ta yi mata wani mugun kallo sannan ta ce,

“Idan kin san bakinki ba zai dinga fad’ar alkhairi ba don ALLAH ki fita kawai, ke wai shi kenan ba ki da wata magana sai wacce za ki b’ata wa mutane rai?”

Ta k’are maganar tare da yi mata wani mugun kallo, Munara ta saki sark’ar dake hannunta daga tsayen ta fad’o k’asa ranta a b’ace ta ce,

“Ah! Lalle! A baya ma aka nunan wariya ballantana yanzu? To na yi nan, tun da ba a buk’atar gani na a nan, amma fa ba girin-girin ba dai ta yi mai, don kwad’ayi mabud’in wahala ne.”

Tana maganar tana tafiya har ta fice ta bugo d’akin da k’arfi, Mumny da Munawwa suka bita da kallon takaici, Munawwa ta yi saurin cewa,

“Don ALLAH Mummy kada ki b’ata ranki a kanta, don ALLAH ki ci gaba da yi mata addu’a kawai ko da za a samu sassaucin abin da take yi.”

Mummy ta sauke ajiyar zuciya ta ce

“Ni na rasa me ke damun Kwakwalwarta shin ita wai ba ta tunanin abin da take bai dace ba? Kullum jiya iyau, ni fa lamarin Munara ya fara ba ni tsoro fa!”

Munawwa ta yi ta kwantar wa da Mummy hankali har ta samu ta saki ranta ta daina faɗan, sannan ta mayar da kayan a ledarsu ta je ta zubo abinci ta zauna a falo tana ci, a gefe ɗaya kuma tana faman kiran Number’r Aliyunta. Ganin ta k’i shiga dole ta hak’ura, amman ba don ta so ba, don ta matsu ta ji muryarsa sannan ta san halin da yake ciki.

Har marece Mummy da Munawwa suna jiran tsammanin kiran Nuradden amman shiru, har lokacin da Daddy ya dawo tun daga corridor ya fara k’walla wa Munawwa kira, saboda ya ga motar, shi ma kansa sai da k’irjinsa ya buga. Don ya san motoci sosai ko a duba d’aya zai iya tantance prize d’inta, kasancewar shi mai huld’ar siye da siyarwa na motoci, saboda sana’arsa kenan, ya siye mota idan wani ya gani yana so sai ya siyar masa,sannan idan ya yi wa mota kud’i to ko a’ina ne da wuya su wuce haka saboda gogewar shi a kan harkar.

Shi ya sa idonsa suna k’yallawa suka hango ta hankalinsa ya tashi, dalilin da ya sa ya kasa hak’uri kenan har ya tambayi maigadi. Shi ma bai yi ƙwauron baki ba wurin yi masa bayanin cewa kyauta ce aka yi wa Munawwa. Shi ya sa yake ta k’walla mata kira tun kafin ya shigo hankali a tashe, Munawwa ta fito kitchen da gudu, domin girkin dare suke yi ita da Mummy. Jikinta yana rawa gabanta yana fad’uwa ta ce,

“Ga ni Daddy”

Daddy ransa a had’e ya ce da ita,

“Uban wa ya ba ki waccen tsadaddar motar?”

Jikinta yana rawa ta fara magana tana inda inda Mummy da ke fitowa daga kitchen d’in ta ce,

“Wani ne wanda yake sonta fa! Shi ne ya aiko mata da ita kyauta d’azu!”

Daddy jikinsa yana rawa yake fad’in,

“Shi d’an mahaukaciyar ina ne da zai ba ta kyautar motar da kud’inta za su kai two million?”

A tare Mummy da Munawwa suka dafe k’irji, sannan suka had’a baki wurin fad’in,

“Miliyan biyu?.”

Daddy bakinsa yana kumfa ya ce,

“Wallahi tun kafin ku jawo mini fitina ku mayar masa da kayansa tun wuri, don ni babu ruwana. Saboda ko ni duk hark’allata ban tab’a taka irinta ba, ballantana ita tashin yaushe? Don haka duk hanyar da kuka bi ya ba ta ita, to ku bi ta ku mayar masa da kayansa salun alun, don ni kam wallahi babu ruwana. Tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka.”

Ya wuce fuuu tare da gyara zaman babbar rigarsa ya yi sama, fara hawa step ya yi sannan ya waigo yana cewa,

“Tukunna ma dai d’an gidan Uban waye a garin nan? Da har zai iya irin wannan kyautar almubazzancin?”

Bakin Munawwa yana rawa ta ce,

“A can gaban layinmu nike ganin yana ajiye motarsa, daidai wurin mai shagon nan..”

Da sauri Daddy ya ce,

“Miye sunan shi? Kuma d’an waye a garin nan? Sana’ar me yake yi?”

Mummy ta yi saurin fad’in,

“Ke Munawwara ki kira shi a waya ki ce da shi mahaifinku yana son ganin shi, idan ya zo sai ya yi masa bayani da kansa kamar zai fi ganewa.”

Munawwa ta ce “To”

Jikinta har rawa yake yi tabar wurin, Munara ta bi ta da harara sannan ta k’araso cikin falon ta zauna, idonta a kan Daddy ta ce,

“To ma wa ya sani wai ko d’an damfara ne Daddy! Miliyan biyu fa! Cabd’ijam! Hmmm wai kodai d’an Mafiya ne ma ba a sani ba Daddy? Shi ya sa yake so ya siye ta da kud’i ya je ya yi tsafi da ita domin ya samu wasu kud’in.”

Daddy ya juya, sannan ya ci gaba da maganarsa ya ce, “Ko dai mene ne, bala’in da suka janyo ya tsaya iya kansu.”

mummy ta bishi da kallo har ya shige sashensa sannan ta dawo da kallonta ga Munara, suna had’a ido ta tashi sumui sumui ta shige d’akinsu ta rufo ƙofa tana babbaka dariya.

Munawwa kam tana shiga d’akin Mummy ta d’auki wayarta ta fara kiran Nuradden d’in, ta yi kira ya kai biyar tana ringing bai d’auka ba, sai ga shi ma ya turo mata da text yana cewa,

“Am busy plss! I will call you letter.”

Ba shiri ta jefar da wayar a kan gado tana cewa,

“Oh my god! Shi kam wannan mutumin busy dai busy dai?”

Mummy ta shigo d’akin a rikice ta ce,

“Kin kira shin?”

Munawwa cikin damuwa ta ce,

“Na kira shi ya ce wai na jira zai kira ni anjima.”

Mummy ta kai zaune babu shiri sannan ta ce,

“ALLAH ya fisshe mu cikin wannan jidali da ya jajibo muna zaman zamanmu. “

Munawwa ta ce “Amiñ”

*****

Basarake kam duk wannan kira da take yi masa suna kan hanyar shiga garin Abuja, shi ya sa yake son sai ya je gida ya huta sannan ya kira ta.

Wani tangamemen K’aton gida motar ta nufa, wanda ko gate d’in shigowa biyu ne, na farkon akwai masu tsaron da suka kai 20, sai gate na biyu inda shi kuma yake da mutanen da za su kai goma, duka suna sanye da wasu uniform iri d’aya, wanɗanda ba za a iya tantance su waye hadiman gidan, su waye masu gadi,?.

Idan aka shiga gate na biyu; gidan ya kasu part-part har ƙwara biyar, abin mamaki kowane part idan ka kalla za ka d’auka cewa gida ne sukutum, domin kuwa Basarake koda ya shiga part d’in farko ne na gano hakan, saboda k’ato ne na gaske mai sama da k’asa d’auke da d’akuna birjik, tun daga bakin babban falo ya fara kiran sunan kakale ‘yar tsohuwa har ya kai tsakiyar k’aton falon, wanda ya sha kayan alatu iri dabam-dabam wanda tsayawa fadin su bata lokaci ne.

Kakale da Ummi suka fito kowane nsu daga nashi b’angare, inda Kakale take ta dogara wata ‘yar k’aramar sanda mai shegen kyau tana k’ok’arin k’arasowa wurin shi, shi ma da sauri ya isa wurinta yana zuwa ya rungume ta yana farin ciki, Ummi tayi tsaye tana kallon shi fuskarta cike da fara’ar ganin tilon d’anta, Kakale kam saboda Murnar ganin shi har da su kukan farin ciki.

Basarake ya dinga rarrashinta da daddad’an magana har ya samu ta yi shiru, sannan ya samu damar gaisawa da Ummi. A cikin farin cikin ganin juna suka…

<< Bakon Yanayi 17Bakon Yanayi 19 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.