Skip to content
Part 1 of 17 in the Series Birnin Sahara by Haiman Raees

Matashiya 

A wata duniyar can ta daban, akwai ƙasashe, mutane, dabbobi, addinai, al’adu da sauran abubuwa masu kama da irin namu, kuma suna da zubi da tsari irin namu. Ko da yake al’amuran da ke faruwa a cikin wannan duniyar sun yi kamanceceniya da irin namu, wasu abubuwan sun sha banban da namu. Akwai labarai masu tarin yawa da suka faru a cikin wannan duniya masu tarin abubuwan al’ajabi da ban mamaki, wataƙila mai karatu ya yi tunanin ma a tashi duniyar suke faruwa saboda kamanceceniya, amma a zahiri al’amuran na faruwa ne a wata duniya can ta daban. Mai karatu, shigo cikin wannan duniya mai kama da tamu ka sha labari.

Babi Na Ɗaya 

A hankali na buɗe idanuwana yayin da wani irin ƙaƙƙarfan hasken rana yake ƙoƙarin tilasta ni sake rufe su. Wani azababben zafi na ji ya fara shiga jikina da na rasa ta sama yake fitowa ne ko ta ƙasa. Da ƙyar dai na samu na buɗe idanunwan nawa, ai kuwa sai na yi arba da sararin samaniya mai cike da giza-gizai a jere wuri-wuri. Wannan ne ya tabbatar min da cewa a kwance nake. Cikin ƙarfin hali na yi yunƙurin tashi daga kwanciyar da nake, amma sai abu ya faskara, domin kuwa ji na yi tamkar an ɗaura min dutse mai nauyin gaske a ƙirjina, ga wani irin ciwo da na ji jikina yana yi da ba shi da alaƙa da wani abu da na sani. Ko da yake ina cikin hayyacina, amma gaɓobina sai suka gaza amsar umurnin da zuciyata take basu na su miƙe tsaye. Domin ji nake kamar bazan iya motsa ko da yatsun ƙafata ba. Kafin in ankara tuni gumi ya fara keto min kamar wanda ya wuni yana aiki a gona. 

Ina nan dai a kwance, sai wasu tambayoyi suka fara yi min yawo a cikin ƙwaƙwalwata. Shin a ina nake? Me ya kawo ni nan kuma ya aka yi na wanzu a wannan wuri? Waɗannan su ne kaɗan daga cikin irin tambayoyin da suke raina waɗanda ba ni da amsoshin su a daidai wannan lokaci. Na runtse idanuwana tsawon kimanin daƙiƙu talatin ina mai karanta addu’o’i a sirrance sannan daga baya na sake buɗe idanuwan nawa a karo na biyu. Ai kuwa nan take wani abun mamaki ya faru, domin kuwa ji na yi duk wata gajiya ta kau daga jikina tamkar a mafarki. Na miƙe tsaye a hankali yayinda nake duban hagu da dama na. 

A wani babban fili na tsinci kaina mai cike da rairayi, wanda tuni har ya fara ɗaukar zafi. Filin a zagaye yake da wata irin makekiyar katanga mai matuƙar kauri da kuma tsawo, yayin da a gefe ɗaya kuma wasu ‘yan ƙananan tanti ne masu kama da bukkoki a jere reras iya ganinka. Ga kuma wata hanya nan mai kyau da aka yi da duwatsu wacce ta ratsa ta cikin waɗannan ƙananun tanti har zuwa wurin da nake tsaye. Ko da na kai dubana gaba gare ni, sai na yi arba da wasu irin manya-manyan mutane a tsaye. Mutane ne masu girman gaske tamkar shanu, ga su baƙaƙe kuma murɗaɗɗu, kai da ganinsu ka ga ƙarfafa. Kowanne daga cikinsu sanye yake da wata baƙar riga mai haɗe da wando shi ma baƙi. Dukkansu kowanne na sanye da baƙin rawani a kanshi, ga kuma zabgegiyar takobi maƙale a ƙugun kowannen su. A ƙalla waɗannan mutane za su kai kimanin dubu ko fiye ma da haka, saboda bana iya ganin ƙarshen su daga inda nake tsaye. Ga su nan sun jeru a layi sahu-sahu kamar masu jiran haddi. 

Na yi matuƙar mamakin ganina a wannan wuri tare da ganin waɗannan mutane masu ban mamaki a gabana, domin abin da zan iya tunawa kawai shi ne, tsayuwa a gidan biredin da nake aiki yayinda muke ƙulla biredi a leda. Daga nan ban san abinda ya faru ba sai kawai ganina na yi a wannan wuri. Su dai waɗannan lafta-laftan mutane suna tsaye ne ƙam kamar gumaka, kuma babu wanda ya ko kalle ni ma balle ya yi min magana. Hakan ya sa ni ma ban ce da su uffan ba.

Ina nan a tsaye na rasa me zan yi, gashi rana ta take, ina ta gumi kamar wanda ya haɗiyi kunama. 

Ga rairayi sai gasa min ƙafa yake yi ina ta mutsu-mutsu, domin sai a lokacin na lura da babu takalmi a ƙafata. Da dai na ga haka, sai na ɗan yi taku ɗaya da nufin yin ‘yar tafiya a cikin wannan fili ko zan ga idon sani. Aikuwa nan take sai mutum biyu daga cikin waɗannan lafta-laftan mutanen suka zare takubbansu tare da auna ni da su. Cak! Na tsaya ba shiri sannan na koma da baya na tsaya a inda nake tun da fari. Bisa mamaki sai na ga suma sun koma kamar yadda suke da fari, kai ka ce basu taɓa motsi ba. Kowannen su kuma ya mayar da takobinsa cikin kube kamar babu wani abu da ya faru. 

‘Za’a yita kenan.’ 

Na ayyana a cikin raina. Muna cikin wannan hali ne na ji wata ‘yar ƙaramar ƙara na fitowa daga cikin aljihuna. Na yi maza na sa hannu a cikin aljihun shuɗin wandon jeans ɗin da ke jikina na zaro wayata ƙirar Infinity Space 7, wurin adadin yawan cajin wayar na kai dubana. Ai kuwa har ya yi ja, domin 15% ya rage. Kuma duka layukan biyu sun nuna min emergency, ma’ana dai ba sabis a wurin da nake. Na yi maza na sa wayar a battery saver sannan na mayar da ita cikin aljihuna. A dai dai wannan lokaci ne kuma wani tunani ya faɗo min, me zai hana in yi magana da waɗannan mutanen in ji ko a ina nake? Don haka, kai tsaye sai na sake yin taku ɗaya da nufin yi wa ɗaya daga cikin su magana. Ai kuwa cikin wani irin zafin nama waɗannan mutane biyun na farko suka sake zare takubannsu suna masu sake auna ni da su, ko da na koma inda nake tun da fari su ma sai na ga sun sake komawa kamar yadda suke da. Wannan abu fa sai ya bani dariya, don haka sai na fasa ce musu komai. Kawai sai na fara jan su da wasa, sai in yi taku ɗaya ko biyu zuwa gaba, sai in sake komawa da baya. Su kuma a duk lokacin da na yi gaba sai su zare takubannsu kamar za su far min, da zarar na koma kuma sai su maida takubannsu kamar babu abinda ya faru. Haka dai muka yi ta yi da su kamar wasu ƙananan yara. Ni kuwa me zan yi in ba dariya ba. 

Muna nan a cikin wannan hali, sai na fara jiyo ƙarar sawun wasu abubuwa kamar dawakai tare da bushe-bushe suna tunkaro mu ta wannan hanya da ta ratso ta tsakanin waɗannan tantuna. Na juya a hankali domin ganin ko menene ke tunkaro mu, ai kuwa sai na yi arba da wata tawaga ta waɗansu mutane da ba za su gaza mutum hamsin ba. Tafe suke akan wasu manyan dawakai, ga kuma wasu mutanen nan biye da su a ƙafa daga kowane gefe suna buga wasu irin ƙananun ganguna tare da busa wasu irin kayan kiɗa irin su farai da algaitu da dai sauransu. Ko da suka matso kusa da inda muke, sai na lura cewa dokin da ke kan gaba na ɗauke ne da wata mace wadda ta lulluɓe gaba ɗaya jikinta da wani irin farin kaya mai shara-shara. Kanta na sanye da wani irin kambun sarauta me ɗauke da hoton maciji, ta rufe fuskarta ruf da wani farin mayafi, idanuwanta kawai ake iya gani. Ko da wannan tawaga ta zo daidai inda waɗannan mutane suke sai ta tsaya. Ɗaya daga cikin mutanen da ke ƙasa ya kama wa wannan mata dokinta ta sakko. Sakkowarta ke da wuya sai masu buga gangar da masu busa sauran kayan bushe-bushen duk suka dakata. Cikin tafiyar ƙasaita wannan mace ta tunkaro inda nake tsaye. Wata irin tafiya take yi kamar maciya. Tafiya ce mai cike da ƙasaita da kuma haɗari a lokaci guda. Ko da ta zo dab da inda nake, sai na ga ta tsaya cak tana kallona. Ni kuwa da bana iya ganin komai a tattare da ita sai na ƙurawa idanuwanta ido ƙuri, domin su kaɗai nake iya gani. Wani irin yanayi na ji a jikina da ba kasafai na cika jin shi ba, yayin da zuciyata kuma ke riya min cewa na taɓa ganin waɗannan idanuwan, sai dai na kasa tuna ko a ina ne. A cikin nata idanuwan nake ganin sanayyarta a tattare da ni, amma na kasa tantance ko wacece ita. Abinda kawai zan iya fahimta shi ne, lallai da alama ita ɗin jinin sarauta ce, ta iya yiwuwa ma sarauniya ce. Don haka sai na sassauta murya sannan na ce da ita, “Gaisuwa a gareki ya ke wannan hamshaƙiyar mai mulki, cike da girmamawa tare da mutuntawa a gareki nake roƙon shin ko zan iya sanin a ina nake?”

Abinda ya sa na yi haka kuwa, wata dabara ce da na taɓa jin wani gwanin hikima ya taɓa faɗi cewa ‘Haɗuwarka ta farko da kowa a rayuwarka ita ke bayyana yadda alaƙarka da wannan mutumin zai kasance har bayan rayuwarka’ ni kuwa da ban san a inda nake ba ballantana in san yadda aka yi har na zo wurin, ban shirya samun matsala da kowa ba, shi yasa na yi tunanin yin aiki da wannan dabara, wataƙila in na burge ta mu rabu lafiya ba tare da an kai ruwa rana ba. 

Ita kuwa ko da ta ji wannan kalami daga bakina, sai alamun tsoro da mamaki suka bayyana ƙarara ta cikin idanuwanta. A hankali, kamar wacce aka zare wa laka a jiki ta kai hannu ta yaye mayafin da ya rufe fuskarta. Ko da na yi arba da fuskarta, sai nan take na ji duniyata gaba ɗaya ta sauya, wani abu ya taso tun daga ɗan yatsan ƙafata ya zo ƙirjina ya tsaya, yayin da maƙoshina kuma ya ƙafe kamar gonar shinkafa a tsakiyar rani. Wani ɓangare na zuciyata ya ji daɗin ganinta, domin ko ba komai yanzu na san cewa tana raye kuma cikin ƙoshin lafiya. Wani ɓangaren kuma na ƙoƙarin kawar da tsohon yanayin da zuciyata ke ji game da ita da ke ƙoƙarin sake kawo min ziyarar bazata gefe. Zuciyata na ji ta matse wuri guda, yayin da wasu bishiyoyin tunani suka fara kaɗawa a ƙwaƙwalwata sakamakon wata iskar ƙauna da ta fara busowa daga zuciyata zuwa ƙwaƙwalwata. Ba kowa bace face Nadiya. Nadiyar da ta tafi ta barni da begenta ba tare da sanin matsayin soyayyata a gareta ba, Nadiyar da ta tafi ba tare da ta sanar da ni adireshi ko lambarta ba, Nadiyar da ko sunan mahaifinta ta ƙi faɗa min saboda bata so in nemo inda take. Nadiyar da shekaru biyar kenan rabon da na sa ta a idanuwana, Nadiyar da kai tsaye ta bayyana min kada in sake in ce zan nemi inda take balle in bita. 

Na bita da ido kawai ina mai kasa yarda da cewa ita ce yau a gabana bayan duk waɗannan shekarun. Ita ma alamun mamamkin ne shimfiɗe a kyakkyawar fuskarta wacce har yanzu ke sa zuciyata yin tsalle a duk sa’adda na kalle ta. A hankali Nadiya ta ƙaraso inda nake tsaye, sai da ta matso dab da ni sosai sannan fuskarta ta faɗaɗa da ƙayataccen murmushinta wanda ko baka shirya ba kai ma sai ya saka murmushi, domin ban san lokacin da na fara murmushi ba kamar yaron da ya ga alewa. Amma ko da na tuna irin wulaƙancin da ta yi min a ranar ƙarshe da muka rabu da ita sai nan da nan na murtuke fuska tare da kawar da kaina gefe.

Bayan ta ɗauki wani ɗan lokaci tana wannan murmushi sai ta buɗi baki a cikin sassanyar muryarta ta ce da ni, ”Barka da zuwa Birnin Sahara Haidar! Ko da yake ban san ta yaya aka yi har ka iya shigowa cikin wannan birni namu ba, ka sani cewa ka cancanci a jinjina maka bisa wannan kasada da kuma namijin ƙoƙari da ka yi.”

Yayinda na ji wannan kalami nata, sai na yi ajiyar zuciya tare da ɗan sakin fuska sakamakon jin su, domin na fahimci cewa akwai yiwuwar zan iya samun damar barin wajen lafiya. Amma duk da wannan tunani da nayi, hakan bai hanani tambayarta abinda ke damuna ba. 

“Nadiya shin kece da gaske? Ina ne nan?” 

Na tambaye ta yayinda na daidaita yanayin fuskata saboda kada ta fahimci wani abu dangane da abinda ke damuna.

”Tabbas ni ce da gaske, kuma nan Birnin Sahara kenan, sannan inda muke yanzu shi ne filin da ake baiwa jarumaina horon yaƙi”. Ta bani amsa ba tare da wata wahala ko nuna damuwa ba.

”Jarumanki fa kika ce? Kina nufin duk waɗannan samudawan a ƙarƙashinki suke?” Na kuma tambayarta cike da mamaki.

Maimakon ta bani amsa, sai kawai na ji ta fashe da dariya, ta ci gaba da dariyarta har sai da ta gaji sannan ta ce da ni,

”Tabbas waɗannan jarumai suna ƙarƙashina ne kuma ko rabin su ma baka gani ba, sannan su sun kasance masu biyayya tare da girmamawa a gareni, domin na kasance sarauniya a gare su.” Ta sake zubo min wasu bayanan kai tsaye.

”Af! toh! Wai dama ke sarauniya ce ban sani ba?” Na tambaya ina mai riƙe ƙugu tare da girgiza kai, ko da yake na yi mamakin jin cewa ita Sarauniya ce, sai na dake kawai na ƙi nunawa. Sai ma na sake tambayarta da cewa, 

“To amma me yasa baki taɓa faɗamin ba?” 

”Ka! Wani garjejen ƙato ya daka min tsawa yana mai nuna ni da wani ƙaton mashi wanda saboda kaifin tsininsa har walƙiya yake yi a cikin hasken rana. Na ɗan ja da baya sakamakon ganin wannan al’amari, amma bisa mamaki na sai naga Nadiya ta yi mishi alama da ya ƙyale ni, nan take ya koma inda yake ya tsaya. Daga nan kuma sai ta ci gaba da cewa, 

”Haidar, ina so ka fahimci cewa da da yanzu ba ɗaya bane, yanzu ni sarauniya ce mai ƙarfin iko, kuma gashi ka shigo birnina ba tare da gayyata ko izini ba, don haka ka kyautata kalamanka a gareni, in kuwa ba haka ba to zaka fuskanci hukunci mai tsanani irin wanda baka taɓa fuskantar kamarsa ba, ina fata ka gane?”

Maimakon in duƙa in fara ahi kamar yadda wasu fadawan kan yi, kawai sai na sake riƙe ƙugu a karo na biyu na ce da ita, 

“To na ji Sarauniyar su, yanzu mene dalilin kawo ni nan?” Na tambaye ta cikin alamun jin kai da taƙama, kai ka rantse cewa ni ne sarkin. 

Nadiya ta ajiye wani gajiyayyen numfashi sannan ta ci gaba da cewa, 

“Na fuskanci har yanzu baka fahimci inda lamarin ya dosa ba, kuma na ga kamar kana tantamar girman sarautata don haka ina mai baka shawara da ka ajiye zafin kanka kayi biyayya domin nan fa birnina kake in kuma ba haka ba zan nuna maka cewa da da yanzu ba ɗaya bane, saboda kai ne mai laifin a nan ba ni ba, don haka ni zan yi tambayar, kai kuma za ka bada amsoshin su, in kuwa ka yi min ƙarya to za ka gamu da fushina.” 

Nadiya ce ta yi wannan furuci a yayinda fuskarta ta canja zuwa ga alamu na fushi.

Ko da jin haka, sai nima na bushe da dariya irin ta ƙeta, bayan na yi wacce ta ishe ni, sai na Kalli Nadiya ido cikin ido na ce da ita, “Amma lallai na lura cewa ƙwaƙwalwar ki ta fara samun matsala, yanzu in banda tsabar rashin adalci, ta yaya za a ce ki sato mutum daga garinsu ki kawo shi wannan rairayin kuma ki ce kina buƙatar ya yi miki biyayya? Kuma ki rasa wanda ma za ki yi wa hakan sai ni? Shin kin manta cewa ni ruwa ne bana son takura? Ko don kin ga ina son ki a da? Lallai ya kamata ki sake tunani, domin abinda kike tunani ba fa zai yiwu ba kawai ki faɗa min dalilin ki na kawo ni nan sannan ki hanzarta maida ni gida yanzun nan!”

Waɗannan kalamai nawa ba ƙaramin ƙonawa Sarauniya Nadiya rai suka ba, domin tunda na fara dariya naga ta turɓune fuska, ai kuwa ina gama wannan jawabi nawa sai Sarauniya Nadiya ta kalli waɗannan Lafta-laftan samuwadan a fusace ta ce da su, 

“Ku kama shi ku kaishi kurkuku!”

Nan take kuwa suka nufo ni a fusace da nufin su yimin kamun kazar kuku su kulle kamar yadda sarauniyarsu ta umurta.

Birnin Sahara 2 >>

51 thoughts on “Birnin Sahara 1”

  1. Bilkisu garba aliyu

    Gaskiya wannan labari yy dadi Kuma zai anfanarda mutane matukar mutun ya fahimci kan labarin Kuma muna addua Allah ya Kara ma marubuci lafiya,basira ,dakuma Nisan kwana

  2. Masha allah gaskiya nayi matukar farinciki sosai kumana fa idanta dana karanta wannan labarin kuma gaskiya akwai abubuwan amfani sosai musamman ga dalibai masu koyon salon zance dakuma hikima da azanci gurin magana sannan akwai darussa masu yawa da lbrn yakunsa allah yasakada alkhairi yakara basira malam

  3. Masha allah gaskiya wannan labari yayikyau sosai kuma yayi dadi allah yakara basira acikinsa akwai abubuwan amfani dayawa musamman ga dalibai masu koyon iya maganada azanci dakuma hikimomi na salon magana sannan yanada darussa sosai mungode malam

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×