Skip to content
Part 5 of 17 in the Series Birnin Sahara by Haiman Raees

A zahiri na tsorata da jin muryar wannan badakare, amma sai na dake don bai kamata in zama matsoraci ba, ni ne fa Haidar! Sai dai kuma bana so in yi abin da zai ɓatawa Sarauniya Nadiya rai. Saboda haka ya zama dole in yi wani abu.

Maimakon in firgice ko in ji tsoro in duƙa in yi gaisuwa a ruɗe, kawai sai na dake, na yi murmushi sannan na ɗan yi taku uku zuwa gaba inda za’a fi ganina da kyau na fuskanci mai maganar na fara magana cikin raha ina cewa, 

“Haba mana bijimi sai ka ce baka waye ba, ai a matsayina na baƙo kuma mutum mai sauƙin kai, kamata yayi in yi wa Sarauniya gaisuwar ban girma irin wacce ba’a taɓa yi mata irinta ba. Haba duba fa ka ga irin kwalliyar da ta yi wacce na san ko wata ma da taurari kishi suke yi da ita saboda an fi kallonta a bisa su, duba fa ka ga irin kyawunta wanda ya zarce tunani, ta yaya kake tunanin zata ji daɗi in an gaisheta da salo irin na mutanen da wanda an daina amfani da shi da daɗewa? Haba mana ka waye aboki.”

Na ƙarasa maganar ina dariya ciki-ciki. Babu wanda ya yi dariya ko murmushi daga cikin jama’ar fadar, maimakon haka ma da yawansu murtuke fuskokinsu suka yi, yayin da wasu kuma suka buɗe baki kawai suna kallona. Sai a lokacin ne na fahimci tsantsar shirmen da na yi, ta yaya zan zo ƙasar mutane kuma in kushe musu al’adar da suka daɗe suna yi? Ƙila ma tun zamanin iyaye da kakanni? Me ke damu na ne? Na dai danne kawai ban ƙara cewa komai ba.

Daga nan sai na nufi inda karagar Sarauniya Nadiya take kai tsaye, ko da ganin haka, sai wasu ɗirka-ɗirkan ƙarti suka nufo ni da nufin su dakatar da ni, amma sai Sarauniya Nadiya ta ɗaga musu hannu alamar su ƙyale ni. Yayin da na iso dab da karagar, sai na tsaya cak, sannan na durƙusa bisa gwiwata guda ɗaya kamar yadda na ga sun yi, na duƙar da kaina ƙasa, sannan na fara magana cikin tausasa murya ina mai cewa, 

“Gaisuwa ga Sarauniya Nadiya, Sarauniyar kyawawan matan duniya, jarumar gaske, cikakkiyar mace mai kamala da cikar zati, haƙiƙa na aikata babban kuskure da na yi miki magana cikin rashin ladabi, kuma na san cewa na cancanci kowane irin hukunci kika yanke min, sai dai ya shugabata ki sani cewa ni ba komai bane face matashi wanda bai san abin da yake yi ba, kuma na jahilci matsayi da ƙimar da kike da su. Don haka ne ma na ke neman afuwa a gare ki yake wannan kyakkyawar Sarauniya mai cikar halitta.”

Yayin da na zo nan a zance na, sai fadar ta ƙara yin tsit tamkar maƙabarta, aka rasa wanda zai iya cewa komai. Bayan wani ɗan lokaci, sai na ɗago kaina da nufin in kalli Sarauniya Nadiya. Ai kuwa abinda na gani ya bani mamaki matuƙa. Ba komai na gani a tattare da Sarauniya Nadiya ba face abubuwa guda biyu, na farko dai mamaki ne ya bayyana ƙarara a fuskar ta, farinciki da jin daɗi kuma suka bayyana a cikin idanuwanta. Kada ku tambaye ni ta yaya na gane hakan a cikin ɗan ƙanƙanin lokaci haka domin bani da amsar da zan baku face in ce muku hakanan dai kawai na gane. Ita kuwa Sarauniya Nadiya dama can ta ƙware a irin wannan al’amari, domin kuwa ita ɗin mace ce mai tarin abubuwan mamaki.

Sai dai abinda ya fi tayar min da hankali a daidai wannan lokaci shi ne, me yasa kuma take mamaki bayan ita ta roƙe ni da in kwantar da kaina matuƙar ina so ta cece ni? Ina cikin wannan tunani ne kwatsam sai naji an yi gyaran murya. Hakan ne yasa na fahimci cewa ashe fa tun ɗazu na saki baki ne sakaka ina ta kallonta.

Ko da na fahimci haka sai na yi sauri na sake duƙar da kaina ƙasa tare da bada haƙuri. Bayan wani ɗan lokaci sai Sarauniya Nadiya ta sake yin gyaran Murya sannan ta fara magana cikin wata irin siga wacce babu tausayi kuma babu tursasawa a cikinta tana mai cewa, 

“An karɓi tubanka ya kai wannan baƙo, sai dai kada hakan yasa ka fara jin daɗi ko ka saki jiki, domin kuwa laifin da ka aikata ya wuce inda kake tunani. Amma da fari, zan so in ji ta yadda aka yi har ka samu damar shigowa wannan birni namu.”

A yayin da Sarauniya Nadiya ta zo nan a zancenta, sai na rasa me ma ya kamata in ji ne? Farin ciki ko baƙin ciki? Hakanan dai na yi ta maza na sake ɗago kaina ina mai kallonta ido cikin ido sannan na ce, 

“Ya ke wannan Sarauniya mai karamci, ni kaina ban san yadda aka yi na zo nan ba, ni dai abin da zan iya tunawa kawai shi ne kasancewata a gidan biredin da nake aiki yayinda nake ƙullawa a leda, kwatsam sai na ji kamar an ɗaga ni sama, daga nan ban sake sanin inda kaina yake ba sai farkawa na yi na ganni a wannan fili da ki ka ganni tun da fari.”

Ina rufe baki kuwa sai wannan boka ya yi caraf ya fara magana da cewa, 

“Kai yaro, kada ka raina mana hankali, ko gashin gemuna na san ya haife ka ballantana ni kaina, kai a tunaninka za mu yarda da wannan tatsuniyar taka ne? Shin me zai hana kawai ka faɗa mana gaskiyar cewa kai ɗan leƙen asiri ne da aka aiko ka domin ka kwashi sirrinmu ka miƙa shi ga maƙiyanmu domin su zo su ga bayan mu?”

Jin wannan magana ba ƙaramin ɓata min rai yayi ba, domin idan akwai abinda na fi tsana a duniya, to bai wuce ka zarge ni akan abinda ban yi ba. Amma saboda bana son in ɓata wa Sarauniya Nadiya rai, sai na yi banza da shi kawai ban ce masa komai ba, sannan na ci gaba da magana ina mai cewa,

‘Wannan shi ne iya abinda zan iya tunawa ya ke wannan sarauniya mai duniya.”

Yayin da Sarauniya Nadiya ta ji wannan batu nawa, sai ta yi shiru na tsawon wani lokaci ba tare da ta ce komai ba. Can sai ta ce, 

“Ya kai wannan baƙo, ka sani cewa abu ne mai wahala a samu mutum ɗaya da zai iya yarda da zancenka a duk faɗin birnin Sahara, saboda yau sama da shekaru ɗari biyu da arba’in kenan da kafuwar wannan birni, amma ba’a taɓa samun mahaluƙin da ya shigo cikinsa daga waje ba sai kai, ta yaya kake tunanin za mu iya yarda da kai?”

Ko da Sarauniya Nadiya ta zo nan a zancenta, sai na ji kamar an ɗaura min ƙaton dutse a kaina. Haƙiƙa in dai har sama da shekaru ɗari biyu da arba’in babu wanda ya taɓa shigowa cikin birnin Sahara, to tabbas Sarauniya Nadiya da mutanenta suna da duk wata hujja ta tuhumata a matsayin ɗan leƙen asiri, to amma ni na san cewa bani da laifi, tunda ko yanka ni za a yi ban san ta yadda aka yi na shigo birnin nan ba. A dai-dai wannan lokaci ne kwatsam sai wani tunani yazo min, don haka banyi wata-wata ba wurin yin amfani da shi.

“Ya ke wannan kyakkyawar Sarauniya mai haiba, idan har a tsawon wannan lokaci babu wanda ya taɓa shigowa cikin wannan birni, shin kuna da tabbacin in ku kun fita wani ba zai biyo ku a baya ba shi ma ya shigo? Ina nufin am… Tun da dai ba za a rasa ƙofa ba, kenan ai kowa na iya shigowa, menene banbancin nan da sauran garuruwa?” 

Na tambayeta a lokacin da zuciyata take riya min ‘yauwa na kama su.’ 

Ko da Sarauniya Nadiya ta ji wannan tambaya tawa, sai ta yi wani tattausan murmushi wanda yasa har fararen haƙoranta masu matuƙar kyau suka bayyana, sannan ta ce da ni, 

“Tabbas akwai banbanci mai girma a tsakanin Birnin Sahara da sauran birane, domin kuwa babu mahaluƙin da ke iya gani ko shigowa cikin wannan birni face sai ya kasance ahalin wannan birni, dangane da shiga ko fita kuwa, ahalin masarautar ce kawai ake barinsu suna fita izuwa wasu ƙasashen domin su koyo sabbin ilmomi a fannoni da dama su dawo su koyar da mutanen gari. Don haka babu damar shigowar wani cikin wannan birni.”

Ko da na ji wannan batu, sai nan take na ji gwiwata ta yi sanyi, domin kuwa bani da wani uzuri da zan iya ba wa mutanen nan har su amince da ni. Don haka, kawai sai na yanke shawarar rungumar ƙaddara tare da miƙawa Allah komai. Kawai sai na kalli sarauniya Nadiya na ce da ita, 

“Shin yanzu babu wata hanya da za’a iya bi domin a gano gaskiyar maganata?

Ko da gama faɗin hakan, sai mutanen fadar suka fara yi min dariya, wasu ma har da tuntsirowa daga kan kujerun su. Bayan sun ɗau tsawon lokaci suna wannan dariya, sai Sarauniya Nadiya ta ɗaga hannu sama alamar a yi shiru, bayan kowa ya yi shiru sai ta dube ni cikin alamun damuwa tana mai cewa, 

“Ya kai wannan baƙo, ka sani cewa muna da wata doka mai tsawon tarihi da muka kafa a wannan birni, wannan doka kuwa ita ce, duk mutumin da ya shigo ƙasar nan da nufin cutar da ko da ƙadangaren da ke cikinta ne, to nan take zamu yanka shi, duk kuwa wanda ya shigo bisa ɓatan kai ko tsautsayi, to zamu ajiye shi a ƙarƙashin kulawar wani ɗan ƙasar har na tsawon wata guda kafin mu yanke hukuncin yadda zamu yi da sh, sai dai kuma ba a nan gizo ke saƙar ba, dole ne ga duk wanda zamu aje a cikin wannan birni namu na tsawon waɗannan kwanaki ya zama ya ƙware a cikin ɗayan abubuwa uku, Jarumta, Ilimi ko kuma wata Fasaha, idan kuwa har bai yi nasara a ɗayan waɗannan abubuwa ba, to kai tsaye mu a wajen mu ba shi da amfani, duk kuwa wanda ba shi da amfani a gare mu, to bamu ga amfanin da zai iya yiwa sauran mutanen duniya ba, don haka nan take shima za a kashe shi. Bisa rashin sa’a sai gashi kun zama mutane na farko da kuka fara shigowa wannan ƙasa tamu don haka ka ji abinda zaka fuskanta matuƙar kana so burinka na kuɓuta ya cika.”

Ko da na ji wannan batu sai na yi shiru ina tunanin abin da ya kamata in yi, ni dai ban jin kaina, to amma Sadiya fa? Duk da cewa babu soyayyar ta a zuciyata, babu wani mukusanci nawa da ya wuce ta, haka itama bata da wani makusanci da ya wuce ni, lallai ya zama dole a gare ni in san hanyar da zan kuɓutar da mu daga wannan hali da muke ciki, in kuma abin ya ƙi yiwuwa, to ko ba komai dai ita ta kuɓuta. Don haka kawai sai na dubi Sarauniya Nadiya na ce, 

“Na amince da wannan sharaɗi, amma ina neman alfarma guda ɗaya, ina so idan har na yi nasara a jarabawar da za a yi min, to ya zama nasarar tamu ce ni da Sadiya, ita ba sai an jarabata ba.”

Yayin da Sarauniya Nadiya ta ji wannan kalami nawa, sai ta cika da mamaki, ashe su mutanen wannan birni a mafi yawancin lokuta kowa ta kansa kawai yake yi. 

“Tabbas kana da ban mamaki.” 

Sarauniya Diana ta faɗa fuskarta cike da mamaki, sannan ta ci gaba da cewa, 

“Abinda ka roƙa ba zai yiwu ba, sai dai na yi maka alƙawarin idan har ka yi nasara a jarabawar da za a yi maka, to zan baka damar sake shiga wata jarabawar a madadinta, in kuwa ba ka yi nasara ba to shi kenan duk za ku halaka.” 

Wannan magana da Sarauniya Nadiya ta yi ba ƙaramin faranta min rai ta yi ba, nan take na duƙa bisa guiwa ɗaya kamar yadda na ga suna yi na yi mata godiya, sannan na miƙe cikin izza na ce, 

“Na shirya domin fuskantar wannan jarabawa.” 

Nan take mutanen fadar suka fara bubbuga ƙafafun su a ƙasa, ƙarar bugun sawayen nasu na cika ko’ina kafin daga baya suka dakata don kansu. Ita kuwa Sarauniya Nadiya sai ta umurci wasu jibga-jibgan dakaru da su kawo mata wani abu da ban san

Mene ne ba. Dakarun basu daɗe ba sai ga shi sun dawo niƙi-niƙi ɗauke da wani teburin baƙin ƙarfe, a kan wannan teburi kuwa, wani kasko ne shi ma na baƙin ƙarfe, dakarun nan suka zo suka ajiye wannan teburi a gaban Sarauniya Nadiya.

Daga nan sai Sarauniya Nadiya ta yiwa Boka Wajagi izinin gabatowa gareta, sai a wannan lokaci ne na ji sunan shi. Ai kuwa sai da na yi ‘yar dariya ina maimaita sunan a raina ‘Wajagi.’ Wato duk wannan abu da ke faruwa fa kada ku manta babu ko ɗaya daga cikin mutanen fadar da ya ce ƙala, sai dai kawai lokaci bayan lokaci wasunsu kan nuna alamun jin daɗi ko rashinsa a fuskokinsu. Yayin da Boka Wajagi ya gabata a gaban Sarauniya Nadiya, sai ya maida dubansa zuwa ga wannan teburin baƙin ƙarfe yana mai karanto wasu ɗalasiman tsafi waɗanda shi kaɗai yasan abin da suke nufi. Bai jima da fara karanto waɗannan ɗalasiman tsafi ba sai ga wata shuɗiyar wutar ta bayyana a cikin wannan kasko da ke kan teburin, daga nan kuma sai bokan ya fara karanto wasu sabbin ɗalasiman tsafin da ƙarfi tare da ambaton wasu sunaye marasa kan gado kamar yaro na gwalan-gwalan.

Bai daɗe a wannan hali ba sai ga wasu kyawawan duwatsu farare ƙal sun bayyana a cikin wannan kasko ba tare da wannan wuta ta yi musu komai ba. Bayan ya gama wannan surkulle nasa sai ya dube ni ya ce, 

“Zaɓi ɗaya daga cikin waɗannan duwatsu, domin ƙaddararka tana jikin su ne.”

“Ashe?”

Na faɗa a fili ina mai riƙe baki cikin alamun mamaki sannan na ci gaba da cewa,

“Amma dai kana da matsala, idan har so ka ke yi na zaɓa me zai hana ka fito da su waje tukunna? Ko da yake, kada ka damu wataƙila kaima ba za ka iya bane ko? To ai shikenan, na fahimta.”

Ran Boka Wajagi na san in ya yi dubu ya ɓaci domin fuskar shi har wani karkarwa ta ke yi saboda tsabar fushi, sai dai kafin ya yi wata magana tuni na matsa gaban wannan teburi ya zamana ina fuskantar wannan kaskon baƙin ƙarfe mai ci da wuta. Ba zan ɓoye muku ba a firgice nake, domin wuta ba abar wasa bace, kawai juriya ce saboda komai na iya faruwa, don haka dole in bi al’amuran a yadda suke. Don haka kawai sai na yi Bismillah sannan na tura hannuna na dama cikin wannan kaskon baƙin ƙarfe mai ci da wuta. Bisa mamaki sai na ji wannan wuta ko kaɗan bata da zafi, maimakon zafin ma wani irin sanyi ne take fitarwa tamkar na’urar sanyaya ɗaki.

Yayinda na taɓa ɗaya daga cikin waɗannan duwatsun sai na ji kamar yana motsi kuma kamar yana numfashi, don haka sai na kauda hannuna daga gare shi, haka na yi ta taɓa waɗannan duwatsu har na rasa wanda zan zaɓa, can sai wata zuciya ta ce min in ɗauki wannan mai motsin in yaso a yi wadda za a yi yi ɓera ya ɓaras da garin kyanwa.

Yayin da na fito da wannan dutse daga cikin wannan kasko sai na ji ya daina motsin da yake yi, har da na yi tunanin maida shi sai Boka Wajagi ya dakatar da ni ta hanyar fisge dutsen daga hannu na, bayan ya yi wa dutsen kallon ƙurilla, sai ya fashe da wata irin mahaukaciyar dariya, sannan ya ɗaga ɗan ƙaramin dutsen sama yana mai ci gaba da ƙyaƙyata dariyarsa. Ai kuwa ɗaga wannan dutse ke da wuya sai ga tambarin takubba biyu da garkuwa sun bayyana a saman fadar suna ƙyalli, nan take mutanen fadar suka bushe da sowa suna murna kamar an yi musu wani babban albishir. Bayan sun ɗauki wasu ƴan daƙiƙu suna wannan aiki na dariya, sai Sarauniya Nadiya ta ɗaga hannunta sama alamar a yi shiru, nan take kuwa fadar ta yi tsit! Kamar an ɗauke wutar lantarki a wajen taron biki. Daga nan sai Sarauniya Nadiya ta miƙe daga kan karagar mulkinta, bayan ta ɗan yi zarya na waɗansu ‘ƴan daƙiƙu, sai ta fuskance ni tana mai cewa, 

“Ya kai wannan baƙo, dutsen da ka zaɓa yana ɗauke ne da ƙaddarar yaƙi, don haka za a haɗa ka faɗa da ɗaya daga cikin mutanen wannan birni domin a tantance matsayin jarumtarka, amma ka sani cewa wannan faɗa da za ka yi yana da doka guda ɗaya tal! Ka kashe ko a kashe ka!

A zahirin gaskiya wannan jawabi nata ba ƙaramin tsoratani ya yi ba, domin ji na yi kamar in arce daga fadar, sai dai a yayinda take furta waɗannan kalamai, idanuwanta kuma wani labarin suke bani na daban. Labarin dai ya tafi ne kamar haka: ‘Kai dai Haidar matsala ne, ka san irin bala’in da ka jawowa kanka kuwa? Yanzu gashi babu yadda na iya dole in bari kayi wannan faɗa in ba haka ba kuwa jama’a ta za su yi min bore.’ 

Kada ku tambayeni yadda aka yi na fahimci duk waɗannan abubuwa a cikin wannan ɗan lokaci haka, sanin da na yi wa Nadiya ba ƙarami bane, kuma wannan yanayi da na ga ta shiga ciki ba ƙaramin nishaɗi ya saka ni ba, don haka ban san lokacin da na buɗe baki na fara dariya ba tare da cewa, 

“Haha ai sam kada ki damu Sarauniya komai zai yi daidai, babu wani abin firgici a cikin wannan al’amari haha!” 

Sai bayan da na gama wannan soki-burutsu ne tukunna na fahimci cewa kowa da ke fadar fa ni yake kallo cikin alamun rashin fahimtar inda batuna ya dosa, kafin kowa ya ce komai sai na yi gyaran murya tare da gyara tsayuwata na ce, 

‘An gama yake wannan Sarauniya mai mulkin duniya, tabbas na amince kuma zan kiyaye wannan doka.”

Na tabbata Sarauniya Nadiya itama hankalinta a tashe yake, amma jawabina ya ɗan kwantar mata da hankali. Daga nan sai ta bai wa Sarkin Yaƙi Dargazu izinin gabatowa gareta. Da fari na yi zaton cewa da shi za ta haɗa ni faɗa, don haka sai na fara tunanin cewa anya ma kuwa Nadiya so take in fita daga wurin nan lafiya? Musamman duba da yadda ya nufo inda Sarauniya Nadiya take yana wani irin murmushin mugunta. Na dai danne ban ce komai ba kawai ina jiran ganin abinda zai faru.

<< Birnin Sahara 4Birnin Sahara 6 >>

21 thoughts on “Birnin Sahara 5”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.