Skip to content

Alamomin daidaita rubutu 12 da yadda ake amfani da su

Alamomin daidaita rubutu wani fanni ne na rubutu, ko kuma a ce na ilimi mai zaman kansa. Wannan fanni ya shafi wasu ƙa’idoji ne da tilas ne a yi amfani da su a cikin rubuce-rubuce, matuƙar dai ana so a yi rubutun bisa tsari da nagarta. Amfani da alamomin daidaita rubutu yadda ya dace yana sauƙaƙa fahimtar abinda aka rubuta ga masu karatu. Ƙin yin amfani da su, ko amfani da su ta hanyar da bai dace ba kuwa na sa karatun marubuci ya gundiri masu karatu kuma su kasa fahimtar saƙon da ke ciki.

Wannan ya sa a cikin wannan muƙala zan bayyana waɗannan alamomi da kuma yadda ake amfani da su a cikin rubutu.

1. AYA (Full Stop .): Aya alama ce da ke zuwa a ƙarshen jumla. Alamar aya kuwa shi ne ( . ) sannan kuma ana amfani da su wajen raba haruffan da aka taƙaita su a cikin suna. Alamar aya na nuna kammaluwar magana ce a cikin jumla, ko kuma dakatawa na ɗan wani lokaci.

Misali:

  • Hausawa jajirtattun mutane ne.
  • Abdulhadi A. Abubakar

Idan kun lura da kyau za ku ga cewa an yi amfani da alamar aya a ƙarshen jumlar farko domin nuna alamar dakatawa, a jumla ta biyu kuma domin nuna rarrabuwar taƙaita haruffa a rubutun suna.

2. WAƘAFI (comma ,): Shi ma dai alama ce ta dakatawa, amma shi dalatarwarsa ba ta kai tsawon na aya ba. Amafnin waƙafi shi ne a ba wa mai karatu damar hutawa kafin ya ci gaba da karatu. Sannan kuma, duk inda aka saka waƙafi, to da ƙaramin baƙi za a tashi da rubutu ba da babban baƙi ba.

Misali:

  • Da ace ni ne kai, da ba haka zan yi ba.
  • Ko da suka isa bakin kasuwar, sai suka yada zango a nan.

3. WAƘAFI MAI RUWA (semi colon ;): Wannan ma alama ce ta dakatawa, sai dai ita dakatarwarta ta fi ta waƙafi tsawo, amma ba ta kai ta aya kuma tsawo ba. Ana amfani da wannan alama ne a cikin jimla mai tsawo don ta rarrabe abubuwan da suke da alaƙa da juna.

Misali:

  • Ana dubawa sai ga mage tsuru-tsuru; da gari ya waye aka kai ta gidan mai ita.

Ana kuma iya amfani da alamar wajen rubuta kalmomi kamar haka,

  • Jibgege; Sharɓeɓe. d.s

4. AYA RUWA BIYU (colon :): Alama ce da ake sakawa a gaban batu, wato topic kenan da Turanci, wani lokaci kuma akan kira su da tagwan aya. Wannan alama tana nuni ne da za a fayyace wa mai wani abu a gaba dalla-dalla.

Misali:

  • Asibiti: Wurin da ake kula da marasa lafiya.
  • Wushirya: Tazarar da ke tsakanin haƙoran mutum na gaba da ke sama.

5. ALAMAR MOTSIN RAI (exclamation mark !): Alama ce da ake sakawa a gaban duk wata kalmar da ke nuna mamaki, firgici, murna, annushuwa ko tashin hankali.

Misali:

  • Wayyo!
  • Wohoho!
  • Ahayye!
  • Tirƙashi!

6. BAKA BIYU (brackets ()): Ana amfani da wannan alama ne domin yin sharhi ko fayyace wata kalma da ta gabace ta. Ta hanyar yin amfani da alamar baka biyu, marubuci na iya bayyana ma’anar wata kalma da ya rubuta a baya domin mai karatu ya fahimci abinda yake nufi sosai.

Misali:

  • Ƙwalla (hawaye)
  • Aisha ta ci na jaki (duka).
  • Gobe za mu je birnin gwamna (Kaduna)

7. KARAN ƊORI (hyphen -): Ana amfani da wannan kalma ne wajen haɗa harɗaɗɗun suna.

Misali:

  • Gama-gari
  • Ruɗa-kuyangi
  • Ci-bari-kallo
  • Ba-ji-ba-gani

8. ALAMAR ZARCE (dash …): Alama ce da ake sakawa a gaban yankin maganar da ba a kammala ba, dalili, so ake mai karatu ya ƙarasa da kansa.

Misali:

  • Duk wanda ya ce kai na da nama…
  • Wanda duk bai ji bari ba…
  • Da wasa da yaro…

9. ALAMAR ƘAULI (quotation marks): Alama ce da ke nuna cewa alamar da ke tsakaninsu maganar wani ce ba ta marubuci ba. Ana yin amfani da ita ne saboda mai karatu ya fahimci maganar da kyau, kuma duk abin da ke tsakaninsu haka yake babu ragi, babu ƙari. Ana rubuta su ne bayan waƙafi, sannan da babban baƙi ake rubuta duk kalmar farko da ta zo a cikinsu.

Misali:

  • Ya yi gyaran murya, sannan ya ce, “Na yi murna da zuwan ku.”
  • Bari ku ji abinda ta ce, “Mijinta dukanta yake yi kullum.”

10. ALAMAR TAMBAYA (question mark ?): Wannan alama ita kuma takan zo ne yayin duk da aka yi tambaya. Da babban baƙi ake tashi bayan an yi amfani da ita.

Misali:

  • Waye a nan?
  • Yaushe ka zo?
  • Ashe sun tafi?

11. KARAN TSAYE (stroke /): Alama ce da ake amfani da ita wajen raba kalmomi ko lambobi da ke da kusanci a tsakaninsu.

Misali:

  • 09/09/2023
  • Sama/ƙasa
  • Malami/malama
  • Yau/gobe

12. BAƘIN HAMZA (apostrophe ‘): Ana amfani da baƙin hamza ne a tsakiyar kalma domin fitar da ma’anarta.

Misali:

  • ma’aikata ba maaikata ba
  • ɗan’uwa ba ɗanuwa ba
  • la’akari ba laakari ba

2 thoughts on “Alamomin daidaita rubutu 12 da yadda ake amfani da su”

  1. Avatar

    Madallah da wannan ilimi cikin harshen mu, kuma a saukake. Jazakallah khair.

    Sai dai ya na da kyau a fahimtar da mai karatu, yadda ake rarraba kalmomi. Kamar a rubutun sama, an hada “tsakanin su” kamar haka “tsakaninsu”. Akwai makamanta wannan kuskuren a rubutun sama. Da fatan za’a gyara, a kuma gyarawa mai karatu dan gaba.

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page