Hikaya ta tattauna da haziƙar marubuciya Fareeda Abdallah game da rayuwa, rubutu da kuma irin ra’ayinta game da rubutu. Ga yadda tattaunawar ta kasance:
Tambaya: Da farko dai za mu so jin cikakken sunanki da kuma taƙaitaccen tarihin rayuwarki in ba za ki damu ba.
Amsa: Sunana Fareeda Abdallah. Haifaffiyar garin Kaduna. Na yi Firamare da Sakandare duk a garin Kaduna, yanzu haka ina aure a garin Kaduna.
Tambaya: A wacce shekara ki ka fara rubutu? Kuma me ya ja hankalinki har ki ka fara rubutun?
Amsa: Na fara rubutu a shekarar 2012. Yawan karanta littattafai na marubuta daban-daban shi ya ja hankalina na fara rubutu. Sannu a hankali ina matsayin makaranciya har na kai matakin da nake ga ni ni ma fa kamar ina da baiwar da zan iya isar da saƙo ga al’umma ta hanyar alƙalami.
Tambaya: Zuwa yanzun littattafai nawa ki ka rubuta? Kuma za mu so mu ji sunayensu.
Amsa: Na rubuta littattafai guda goma sha biyu.
- A Dalilin Ɗa Namiji
- Duniya Sabuwa
- Inuwar Mutuwata
- Bara A Kufai
- Bihakki
- Sanadiyya
- Tsakanina Da Mutuwa
- Tubalin Toka
- Rabon A Yi
- Lokaci
- Kasaitacciyar Mace
- Bayan Tiya
Tambaya: Wanne littafi ki ka fi so a duk cikin litattafan da ki ka rubuta, kuma me ya sa?
Amsa: Duk littattafan da na rubuta ina matuƙar son su. Amma a zahirin gaskiya na fi son littafin Rabon A Yi saboda a cikin labarin ne na taɓo wani ɓangare daga cikin halayena da wani ɓangare na tarihin rayuwata.
Tambaya: Shin kina da Maigida ko Uwargida a harkar rubutu?
Amsa: Akwai marubuta da yawa daga cikin manyan marubuta da ƙanana waɗanda nake kallon yanayin rubutunsu a matsayin madubin dubawa kafin tsara nawa rubutun.
Tambaya: Wanne littafi ne ki ka taɓa karantawa da ya fi burge ki?
Amsa: Gaskiya littattafan suna da yawa, kawai dai duk wani littafi da marubuciya ko marubucin ya zurfafa bincike gurin rubutawa, kuma aka hasko matsalolin da muke fama da su aka yi bayanin hanyoyin warware matsalar wannan littafi abin burgewa ne a gare ni.
Tambaya: Shin kin taɓa shiga wata gasa, idan eh ne amsar, shin ko kin taɓa yin nasara? Sannan wasu irin nasarori ki ka samu a rayuwa game da harkar rubutu?
Amsa: Eh! Na taɓa shiga gasar Hikayata ta BBC. Sau biyu labarina ya taɓa fitowa a fitattun labaran da suka tsallake matakin farko. Na kuma taɓa shiga gasar Gusau Institude labarina ya tsallake matakin farko sau ɗaya. Na samu nasarori da yawa sanadiyyar rubutu. Kaɗan daga ciki su ne, bayan alkhairan da nake samu daga wurin mabanbantan mutane, na haɗu da manyan mutanen da ban taɓa tsammanin zan haɗu da su ba a rayuwata, amma sanadiyyar rubutu yanzu alaƙa ta girmamawa da mutunci ce tsakanina da su. Alhamdulillah!
Tambaya: Idan za ki yi rubutu, shin ki kan tsara komai da komai ne kafin ki fara ko kuwa kai tsaye ki ke farawa?
Amsa: Ina tsara matakin farko na labarin, tsakiya, ƙarshe. Amma kuma idan tafiya tayi tafiya wasu abubuwan suna canjawa daga cikin wanda na tsara.
Tambaya: Ya ki ke yi idan wani tunani sabo ya zo miki game da wani rubutu na daban alhalin kina tsakiyar rubuta wani. Ki kan saki wancan ne ki yi wannan sabon ko kuma sai kin gama da wanda ki ka fara?
Amsa: Ina rubuta muhimman abubuwa ne daga cikin sabon tunanin da ya zo min. Sai in cigaba da asalin wanda nake yi, bayan na gama sai in ɗauko wancan sabon tunanin da yazo min in fara bincike a kanshi.
Tambaya: Ki kan ɗauki kamar tsawon wane lokaci kina bincike kafin ki fara rubutu, kuma daga nan yakan ɗauke ki tsawon wani lokaci kafin ki kammala rubutun littafin?
Amsa: Eh to tsawon lokacin da nake ɗauka wajen bincike ya danganta da irin jigon da nake so inyi rubutu a kai. Wani jigon bincikenshi mai sauƙi ne, wani kuma mai wahala ne. Da wannan dalilin ya sa bazan iya yanke takamaimai lokacin da nake ɗauka wajen bincike ba. Ina ɗaukan watanni biyu, uku, huɗu kafin in kammala rubutun littafi.
Tambaya: Wacce hanya ki ke bi wajen samun jigon labarinki?
Amsa: Rayuwarmu nake kalla a matsayin madubi, sannu a hankali sai in zaƙulo ɗaya daga cikin manya ko ƙananun matsalolin da suke addabarmu in yi rubutu akai.
Tambaya: Wacce hanya ki ke bi wajen fitar da halayen taurarinki tare da ba su sunan da ya dace da su?
Amsa: Ina kallon mutanen da ke kewaye da ni ne da irin kyawawa da munanan halayensu, sai in fitar da halayen taurarin labarina sannan in zaɓa musu sunayen da ya dace da su.
Tambaya: Shin ko kin taɓa amfani da wani ɓangare na tarihin rayuwarki a cikin rubutunki?
Amsa: Eh! Na taɓa yi.
Tambaya: Wanne littafi ne ya fi ba ki wahala daga cikin dukkan litattafan da ki ka taɓa rubutawa?
Amsa: Littafina na A Dalilin Ɗa Namiji
Tambaya: Wanne irin ƙalubale ki ka fuskanta a harkar rubutu, kuma ta wacce hanya ki ka bi har ki ka tsallake ƙalubalen?
Amsa: Gaskiya Alhamdulillah! Har zuwa yanzu kasancewata ƙarama a cikin marubuta babu wani gagarumin ƙalubale da na taɓa fuskanta wanda har ya zame mini ƙaƙa-nikayi.
Tambaya: A duk cikin taurarin labaran da ki ka rubuta wanne ki ka fi so, kuma me ya sa?
Amsa: Na fi son Fareeda ta cikin labarin Rabon A Yi. Ina son ta sabida wasu daga cikin halayena na kalla na samar da halayenta.
Tambaya: Akan samu wani lokaci da kan marubuci ke cushewa har ya kasa rubuta komai. Shin kin taɓa shiga irin wannan yanayin? Kuma ta wace hanya ki ka bi wurin magance hakan?
Amsa: Eh! Na taɓa shiga. Rubutun nake ajiyewa gaba ɗaya in koma makaranciya. Sannu a hankali idan na karanta littattafai da dama masu ma’ana da marasa ma’ana sai ƙwaƙwalwata ta buɗe.
Tambaya: Mene ne abin da ki ka fi so game da rubutu?
Amsa: Ina son rubutu saboda sassauƙar hanya ce ta isar da saƙo ga al’ummarmu cikin ƙanƙanin lokaci.
Tambaya: Me ki kan yi a duk lokacin da ki ke da sarari?
Amsa: Tunanin abinda zan yi rubutu akai.
Tambaya: Wace karin magana ki ka fi so? Kuma me ya sa?
Amsa: Ina son karin maganar Babu maraya sai rago. Saboda a aikace nake amfana da karin maganar.
Tambaya: A naki ra’ayin, tsakanin rubutun online da bugun littafi na hannu wanne ya fi? Kuma me ya sa?
Amsa: Ko wanne yana da amfani da kuma muhimmancinsa. Amma a halin yanzu gaskiya rubutu online ya fi rubutun takarda. Saboda kaso takwas cikin goma na makaranta sun fi samun sararin karatu online.
Tambaya: Wanne tasiri marubuta suke da shi a cikin al’umma?
Amsa: Marubuta suna da tasiri mai matuƙar yawa a cikin al’umma. Domin kaifin alƙalami ya fi na takobi. alƙalamin marubuta na iya canja abinda ba zai yiwu ba ya koma wanda zai yiwu. Shi yasa a kullum ake ƙara tunasar da marubuta su ji tsoron Allah su tsarkake alƙalumansu, ba don komai ba sai don saboda yadda saƙonsu mai kyau ko mare kyau ke saurin isa ga al’umma.
Tambaya: Shin ko akwai wani labarin da ki ke rubutawa a yanzu haka da masoyanki za su yi tsumayin fitowarsa?
Amsa: Eh! Akwai labarai guda biyu. Ƙasaitacciyar Mace da kuma Bayan Tiya akwai wata caca.
Tambaya: Wane ne tauraronki a cikin marubuta?
Amsa: Duk wani marubuci da yake wasa ƙwaƙwalwarsa gurin yin rubutu mai cike da ma’ana taurarona ne.
Tambaya: Tsakanin Fim da littafi wannene ya fi saurin isar da saƙo?
Amsa: Littafi.
Tambaya: Wacce irin shawara za ki iya ba wa sabbin marubuta masu tasowa?
Amsa: Su ji tsoron Allah su tsarkake alƙalaminsu. Kar rububin neman fans ya sa su dinga rubutun batsa ko munanan rubutun da zai taka rawa gurin ƙara taɓarɓarewar al’umma. Su dinga yin bincike kafin rubutu. Sannan su dinga ƙoƙarin ba da rubutunsu ga manyan marubuta suna duba musu kafin sakin ko wane feji na labari ga masu karatu. Domin wanda ya riga ka kwana dole ya riga ka tashi.
Tambaya: Mene ne burinki a harkar rubutu?
Amsa: Burina in zama ɗaya daga cikin marubutan da ake kwatance da su wurin yin rubutu mai cike da ma’ana da faɗakarwa.
Tambaya: Me za ki iya cewa game da Hikaya?
Amsa: Hikaya manhaja ce mai muhimmanci da ya zo da tsare-tsare masu kyau don tallafawa marubuta. A iya sanina, nan kusa dai ban ga wata manhaja da ke tafiya kafaɗa da kafaɗa da marubuta ba kamar Hikaya. Ako wane shirye-shirye da tsare-tsare na bakandamiya za ka samu marubuta a ciki. Kuma wani abin burgewa shi ne sun san darajar rubutu da marubuta. Babu abinda zan ce da Bakandamiya sai fatan alkhairi, da addu’ar Ubangiji Allah ya ƙara musu ɗaukaka.
An yi wannan hira da Fareeda Abdallah ne a ranar 22 ga watan Maris, 2024.
Tsara tambayoyi da gabatarwa: Jamilu Abdulrahman (Haiman Raees)