Skip to content
Part 1 of 67 in the Series Lokaci by Fareeda Abdallah

Da wani irin kasala a jikinsa ya ɗaga idanu a hankali ya sauke kan wayarsa da take ajiye a gefensa.

Ƙirjinsa ne ya buga daram! Lokaci ɗaya hankalinsa ya fara ɗugunzuma. Tun kafin ya ɗauki wayar ya ji a jikinsa ba lafiya ba, domin wanda yake kiransa a wayar ba kasafai yake kira ba sai in da wata gagarumar matsalar.

“Alhaji? Daman kana ciki? Ƙarar wayarka nake ta ji sai na zaci ko ka zaga banɗaki.”

Ta ƙarasa maganar haɗe da kai hannunta kan wayar.

“Laaa kaga, Khamis ne ma ya ke kira.”

Amsa kiran da yake gaf da tsinkewa tayi sannan ta kara mishi wayar a kunnensa.

“Hello, Hello, Hello Yaya. Kana ji na?”Kalmomin da aka fara faɗa kenan daga can ɓangaren, da wani irin murya mai bayyana mamallakinta yana cikin tashin hankali.

“Ina jin ka Khamis”

Alhaji Yusuf ya faɗa da sanyin murya, gabansa sai bugawa yake yi. Sai addu’a yake a cikin ransa Allah yasa a wannan karon ba wata mai zafi Khamis ɗin ya sake ɓaro musu ba.

“Yaya kana gida ne? Don girman Allah ka taimaka min. Na san a daidai irin wannan lokacin idan kana gari tabbas kana gida, kar ka ce min baka nan don girman Allah Yaya.”

Khamis ya ƙarasa da salon roƙo, da wani irin rauni da karaya sosai a muryarsa.

“Ina gida.”

Alhaji ya amsa a taƙaice.

“Yauwa Yaya, ka ganni a state CID, idan baka zo a wannan lokacin ba wallahi nema suke su tozarta ni su wulaƙantani. Don girman Allah ka taimaka min. Insha Allahu wannan shi ne na ƙarshe…”

“Fiye da sau goma sha biyar kana faɗin na ƙarshe Khamis. Me yake faruwa?”

Kafin Khamis ɗin ya amsa sai wayar ta katse. Wayarsa ya karɓa a hannunta. A hankali ya ɗaga idanunshi yayi mata wani irin kallo, da saurin gaske ta bar gurin.

Zuciyarta cike da zakwaɗin son jin gagarumin rigimar da Khamis ya sake janyowa a wannan karon.

Amma ba ta da yadda ta iya, a dole ta fice daga ɗakin. Ta san mijinta da sirri, musamman tsakaninsa da ɗan’uwansa.

Ko yanzu da ta ɗaga wayar har suka fara magana a gabanta Allah ne kawai yasa tana da rabon ji.

Miƙewa zaune yayi daga kishingiɗen da yake a farko. Yana niyyar danna kiran lambar Khamis sai wani kiran ya sake shigowa.

“Ka bari zan kira ka…”

“A’a Yaya, ba sai ka kira ba. Ka saurareni don Allah, ina da wadataccen katin da zai isa muyi magana.”

“Ina jin ka…”

“Yaya, wallahi ba wani babban laifi nayi ba. Don Allah don darajar fiyayyen halitta SAW ka zo yanzu. Wacce ta kawo ni gurinnan ba uwa a gindin murhu ba iyaye take da a gindin murhu.

Ƙoƙari take ta toshe min duk wasu hanyoyin da zan iya bi in kuɓuta. Ta rantse da girman Allah sai ta ɗaure ni har igiya tayi rara, ta ce za ta ɓatar da ni a daina jin labarina gaba ɗaya.”

Ya ƙarasa maganar yana jan wani irin shessheƙar numfashi kamar yana kuka.

Hankalin Yayan ne ya ƙara tashi, a zabure ya miƙe tsaye. Ya san Khamis da masifaffen taurin zuciya, duk abinda zai jefa shi cikin irin wannan firgicin ba ƙaramin abu bane.

“Khamis, ka nutsu! Ka faɗa min me yake faruwa? Ƴar gidan wa ka taɓo a wannan karon?”

“Ba ƴar gidan uban kowa bane Yaya. So take dai ta gwada min ta fini iya iskanci. Kazo, don Allah kazo, yanzu Yaya, don darajar iyayenmu…”

Ƙit wayar ta sake tsinkewa a karo na biyu.

Hankalinsa a tashe ya mayar da babbar rigarsa da take sagale jikin ƙofa. Ya ɗauki wayarsa, makullin mota, wallet ɗinsa ya fice daga ɗakin da sassarfa.

“Alhaji? Allah yasa dai lafiya? Za ka ina haka da tsakar ranar nan?”

Hajiya Zainab ta tambaye shi tana zaune akan kujera, ganin da tayi yana ƙoƙarin wucewa ba tare da ya tanka ta ba.

“Ba daɗewa zanyi ba. Yanzu zan dawo. Zan je gurin Khamis ne nan State CID…”

“Alhaji State CID ne za kaje kake magana kamar za ka nan kasuwar barci…”

Wani mugun kallo da ya aika mata yasa ta kasa ajiye numfashin maganarta dai dai. Duk wani ƙorafi da tayi niyyar yi masa ma a take ta haɗiye, da sauri ta gyara zancen da cewa.

“Allah ya baka haƙuri. A dawo lafiya.”

Da saurin gaske ya fice daga falon ba tare da ya tanka mata ba. Bayansa ta bi da kallo mai bayyana takaicin da ke danƙare a zuciyarta.

Tana sane taƙi yin addu’ar Allah ya taƙaita wahala ya kuɓutar da Khamis ɗin. Ai ita ba mahaukaciya bace, ta san haka kawai abin daɗi bazai kai mutum State CID ba. Amma tunda Khamis ɗin tantirin yaro ne da har gobe bai san Annabi ya faku ba sai yaje yai tayi.

“Ya Allah kasa ko Alhaji ya je kar su sake shi. Gara a kulle ɗan banza ko na shekara biyar ne ko za mu samu nutsuwa da sauƙin jefa kai a rikicin da bamu ji ba bamu gani ba.”

Ta ƙarasa maganar tana jan dogon tsaki. Zuciyarta cike da takaicin ƙanin mijin nata da munanan halayensa.

*****

Isarsa gurin yayi daidai da sake shigowar kiran Khamis cikin wayarsa.

“Gani na iso. Kuna ta wane ɓangare?”

Abinda yace kenan bayan ya ɗaga wayar.

Ba’a amsa ba daga can ɓangaren aka katse wayar. Minti ɗaya tsakani bayan ya gama daidaita fakin ɗin motarsa sai ga wani matashin jami’in tsaro ya ƙaraso gare shi.

“Kai ne Alhaji Yusuf?”

 tambaye shi da fuska a tamke.

“Eh! Ni ne”

Ya amsa jikinsa na ƙara sanyi. Tun daga irin wannan tarba ya sake tabbatar ma kansa lallai wannan karon ƙanin nasa ya ɗebo da ƙaton zafi. Sai fatan Allah ya kawo musu ɗauki.

“Ka biyo ni.”

Tafiyar mintuna biyu ya kai su inda Khamis yake, jami’an tsaro sun zagaye shi da fusatattun fuskokinsu. Khamis ɗin ya haɗa zufa yayi sharkaf, idanunsa sun kaɗa sunyi ja sosai saboda tashin hankali.

A gefe ɗaya kuma mutanen da suka yi ƙararshi ne a zazzaune kan kujera. Wata farar yarinya ce kyakkyawa ta gaban kwatance, sai wani farin dattijo wanda bisa ga dukkan alamu babanta ne saboda kamannin da ya bayyana a tsakaninsu.

Sai wasu matasa su uku, da alamun yayyin yarinyar ne ko kuma ƴan’uwanta na kusa. Sosai kamanninsu ke yanayi da nata.

A firgice yake ƙwarai, bai saba shiga rikici irin wannan ba, a kullum ƙanin nasa ke ɗauko masa. Shi ko rigima da mutane baya yi saboda tsananin haƙurinsa da kawar da kai.

Addu’o’i yake ta ja mabanbanta har ya ƙarasa inda su Khamis suke, a hankali yayi sallama ga duk ɓanrorin biyu.

“Da gaske kai ɗan’uwan wannan yaron ne?”

Ɗaya daga cikin jami’an tsaron ya tambaye shi, ba tare da sun amsa sallamarsa ba.

“Eh! Ni Yayansa ne.”

Ya amsa cikin nutsuwa da haiba.

“Wace shaida za ka bamu da za mu tabbatar kai ɗan’uwansa ne ba wani ƙaton iska ya sake gayyato mana ba?”

A hankali ya ɗaga idanu ya sauke kan jami’in da ya jefe shi da wannan maganar. Ya girgiza kai kawai, ko wace irin magana aka faɗa masa Khamis ne yaja mishi.

Lalubo hotunansu yayi a wayarsa ya miƙa musu suka gani.

“Amma gaskiya Alhaji baka yi sa’ar ƙani ba. Officer ba shi gurin zama.”

Jami’in ya sake faɗa cikin rashin damuwa da kalaman da ke fita a bakinsa.

Da raunataccen fuska ya aika ma da Khamis kallon

‘Kana gani ko? Ɗan kuka mai ja ma uwarsa jifa.’

A kasalance ya zauna a kujerar da suka bashi, yayi shiru yana saurarensu.

“Kai!!! Don ubanka maimaita abinda ya haɗa ka da wancan yarinyar yanzunnan a gaban yayanka, idan ka ɓoye kalma ɗaya wallahi anan gurin za mu rufe ka da dukan mutuwa.”

A tsorace Khamis ya ɗaga idanu ya kalli jami’in da yayi mishi wannan maganar. Idanunsa ciccike da hawaye ya mayar da kallon kan Yayansa.

“Yaya, ita wancan yarinyar”

Ya ɗaga yatsarsa manuniya ya nuna yarinyar nan da take zaune da Babanta da ƴan’uwanta. Aka yi sa’a suka haɗa idanu ta kuwa galla mishi harara da manyan ƙwayoyin idanunta.

Saurin kawar da kansa yayi ya duƙar da kanshi ƙasa ya cigaba da cewa

“Sunanta Firdausi. Budurwata ce…”

“Allah ya kiyaye in zama budurwarka”

Yarinyar ta katse shi da sauri da yanayi mai bayyana tsananin rashin kunya da fitsara.

“Baby Feedy kiyi shiru, ƙyale shi ya gama maganganunsa.”

Ɗaya daga cikin ƴan’uwanta ya faɗi haka yana ɗan shafo gefen fuskarta.

“Yaya, budurwata ce ita har a yanzu. Kawai dai mun ɗan sami saɓani ne kan abinda bai taka kara ya karya ba ni kuma na janye mata, da tayi tayi in dawo naƙi shi ne ta kawo…”

“Amma dai Khamis Allah ya tsine maka albarka. Tunda nake a rayuwata ban taɓa ganin tantirin maƙaryaci, mayaudari, mazambaci, maci amana irin ka ba. Amma a juri zuwa rafi, watarana tulu zai fashe.

Ko da yake tun yanzu ma ai ruwa ya ƙare ma ɗan kada. A wannan karon na rantse da girman Allah sai na kawo ƙarshen iskanci da yaudararka.”

Tsam ta miƙe tsaye daga gurin zamanta ta nufo inda suke, tana tafe tana wani karkaɗe-karkaɗen jiki da fari da idanu.

Daf da Alhaji Yusuf ta tsaya.

“Yayan Khamis, ni bari in faɗa maka gaskiyar abinda ya haɗa ni da wannan ɗan iskan ƙanin naka. Tunda na ga ganinka yasa yayi la’asar, da alamun ba ka bashi goyon baya a irin iskanci da lalatar da yake tsulawa a garinnan, kai a ƙasarnan ma gaba ɗaya.”

Ɗaya daga cikin jami’an tsaron ne ya katse ta da cewa,

“Ranki ya daɗe, ai da ma kin hutar da kanki. Ki koma gurin zamanki kawai. Bari mu kunna record na maganganunsa Yayan nasa ya ji…”

“A’a! Yallaɓai inda ba ƙasa ai nan ake gardamar kokawa. Kuma waƙa a bakin mai ita ta fi daɗi. Bari in warware gaskiyar zare da abawa, inda nayi mishi ƙarya don ubanshi ya katse ni idan ya isa.”

Ta sake mayar da hankalinta kan Alhaji Yusuf wanda tun ɗazu hankalinsa na kanta, kwarjinin da yayi mata yasa ta ɗan rusunar da muryarta tace,

“Kayi haƙuri Yayan Khamis. Na san za ka ji babu daɗi kan irin kalaman da nake faɗa akan ƙaninka. To wallahi ya cancanci fiye da haka, da na iya maguzawan ashariya da su zanyi amfani gurin siffanta shi.

Ka ganni nan? Shekaru biyu da suka wuce nutsattsiyar yarinya ce ƴar islamiya. Budurwa mai tsananin kamun kai da kunya.

Duk yadda kaga na zama ayau ba wani bane yaja min gora face wannan tantirin ɗan’uwan naka.

Yadda abin ya faru kuwa shi ne, wata rana na dawo daga gidan Yayata a unguwar dosa Allah ya haɗa ni da shi a bakin titi.

A lokacin yamma tayi sosai, kuma ana cunkoso wajen hawa mota. Ina raɓe can gefe ɗaya hankalina a tashe.

Tun kafin in taho Mamana tayi ta jaddada min kar in kuskura inyi yamma wajen dawowa. Gidanmu can kadaure yake, ga hadari na ta haɗuwa kaɗan-kaɗan.

Kuma wani ikon Allah duk napep ɗin da na tare da niyyar in ɗauki shata da sunji inda zan je sai suce ba can suka nufa ba.

Da wannan dalilin yasa ko da Khamis ya faka motarsa kusa da ni yayi min tayin rage hanya ban ce a’a ba.

Ko da na faɗa mishi inda zan je nayi mamaki da ya kai ni har ƙofar gida. Cikin farin ciki muka rabu bayan munyi musayar suna da lambobin waya.

Tun daga wannan lokacin wata irin zazzafan shaƙuwa ta shiga tsakanina da shi. Ba ma awa guda cif bai kira ni a waya munyi hira ba, ga shi kuma gwani ne ƙwarai gurin iya tsara maganganu masu nuna matuƙar damuwa da kulawa da mutum.

A wancan lokacin bai fito fili ya bayyana soyayyarsa a gare ni ba. Nima duk yadda yake kwance male-male a zuciyata ban taɓa nuna mishi ina son shi ba.

Har sai da muka kai matakin da ya fara nuna ƙarara yana kishi na. Idan yazo ƙofar gidanmu ya ganni da saurayi ya dinga ƙunci kenan yana kushe saurayin da ya tarar. Idan ya kira ni ya ji busy kuma na tabbatar mishi da saurayi nake waya wallahi a wasu lokutan har kuka yake min.

Lamarin sai ya dinga ɗaure min kai yana bani mamaki. Shi bai ce yana so na ba, amma sam ba ya so yaga ina kula wasu samarin. A dole na kawo idanu na zuba masa ina so in ga iya gudun ruwansa.

Muna cikin wannan halin kwatsam sai Abbana ya ce ya bani sati ɗaya, in tsayar da mutum ɗaya cikin samarina. Zai bincika idan yana da halaye masu kyau ya aurar da ni, tunda a lokacin na gama Diploma, ina zaman gida ne kawai.

Hankalina a tashe na kira Khamis na sanar da shi abinda yake faruwa. Saboda a lokacin duk samarin nawa masu niyyar aure ya gama zuge ni na rabu da su.

Sosai ya rarrashe ni a waya, ya zo har gida ya ƙara rarrashina da kalaman kwantar da hankali. Muka rabu da shi kan cewa in bashi lokaci zai je yayi shawara, duk yadda ake ciki zai neme ni.

Kwana ɗaya, biyu, uku, tun da ya bar gidanmu bai ƙara dawowa ba, kuma ko a waya bai sake kira na ba. Hankalina ya ƙara ɗugunzuma, tun da na haɗu da shi bai taɓa ɗaukar awa ashirin da huɗu cif ba tare da ya zo gidanmu ko ya kira ni a waya ba.

Ga kwanaki bakwai da Abba ya bani yana ƙara kusantowa. Afujajan na kira shi a waya, amma wani abin mamaki da ban tsoro sai da nayi mishi misscall takwas bai ɗaga ba. Abinda bai taɓa faruwa tsakanina da shi ba.

Lamo na kwanta kan gado kamar mare lafiya, idanuna sai tsiyayar hawaye suke yi, na tasa waya a gaba kamar shi ne Khamis ɗin da yayi alƙawarin sama min mafita.

Kwatsam sai ga kiranshi ya shigo, kamar wacce ake shirin ƙwace mata waya haka nayi ma wayar wata wawuyar raruma na ɗauka na kara a kunnena. Jikina na rawa, baki na kyar ma, cikin kuka na ce,

Khamis haka za kayi min?

Ki fito ga ni a ƙofar gida.

Ya faɗa kai tsaye tare da kashe wayarsa.

Hijabi kawai na zumbula kan rigar barcin jikina, na rarumi waya na fice a gaggauce.

Ina wayarki? Abinda ya fara tambayata kenan.

Kai tsaye na miƙa mishi wayar ba tare da wata damuwa ba, saboda ba wannan ne karo na farko da ya fara karɓar wayata yayi abinda yake so da ita ba.

Baƙuwar lambar waya ya saka min, ya miƙo min wayar haɗe da cewa… Kin ga wannan lambar wayar? Lambar wani babban malamin sunnah ne da ya shahara gurin yin istikhara da bayar da taimako ga waɗanda ya tabbatar suna cikin ƙaƙa ni kayi irinki. A garin kano yake, kar ki damu da nisan da yayi, daman ba dole sai kin je ba.

Ki kira shi, a waya kawai za ki faɗa mishi halin da kike ciki. Zai miki istikhara da addu’o’i Allah ya gaggauta kawo miki miji na gari.

Idan kuma akwai wasu magunguna da zai baki ta acc kawai za ki tura masa kuɗaɗen maganin shi kuma zai turo a kawo miki maganin har ƙofar gida. Magungunansa akwai ɗan tsada kaɗan, amma fa ina tabbatar miki cikin ƙanƙanin lokaci za ki ga biyan buƙata.

Ya kanne min ido ɗaya fuskarsa cike taf da murmushi. Kuka ya ƙare ko Feedy amaryar gobe?

Da sauri na rufe fuska ina murmushin jin kunya da jin daɗi. Lokaci ɗaya nake jin yadda a hankali matsananciyar damuwar da na fito da ita danƙare da zuciyata take kwaranyewa farin ciki da kwanciyar hankali na maye gurbinta.

Na yarda da Khamis, na san damuwata tasa ce. A zuciyata na daɗe da yaddar ma kaina bazai taɓa bari na a cikin matsananciyar ƙunci da fargaba ba.

Da fara’a sosai a fuskata na ce, kuka ya ƙare Besty. Na gode ƙwarai, da zafi-zafi ake bugun ƙarfe, bari in kira shi tun yanzu.

Da saurin gaske ya dakatar da ni ta hanyar cewa, daɗina da ke gajen haƙuri. Me kike ci na baka na zuba? Ki bari muyi sallama, idan kin shiga gida a nutse sai ki kira shi kuyi magana.

Lokaci 2 >>

4 thoughts on “Lokaci 1”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.