Skip to content

Ba yawan abu ne cigaba ba, nagartarsa shi ne abin dubawa – Bukar Mada

A wata tattaunawa da Bakandamiya ta yi da ɗaya daga cikin zaƙaƙurai kuma shahararrun marubuta na wannan zamani, wato Malam Bukar Mada a ranar Talata, 22nd-09-2020, marubucin ya bayyana irin gwagwarmaya da ya sha a harkar rubutu da kuma sauran bayanai da ya yi game da adabin Hausa da ma sauran abubuwa da suka shafi ruayuwa.

Ga dai yadda hirar ta kasance;

Tambaya: Da farko dai za mu so jin cikakken sunanka da kuma taƙaitaccen tarihin rayuwarka in ba za ka damu ba.

Amsa: Cikakken sunana shi ne, Abubakar Yusuf Mada. Bukar Mada laƙani ne kurum da nake amfani da shi a soshiyal midiya da kuma rubuce-rubucena. An haife ni ne a garin Mada da ke ƙaramar hukumar Mulki ta Gusau a jihar Zamfara, a shekarar 1982. Na fara karatun Islamiyya kafin na fara na zamani. Na yi karatun boko, tun daga matakin firamare har zuwa jami’a, in da na ƙware a fannin da ya shafi nazarin ‘yan halitta masu amfani da masu yaɗa cututtuka (Microbiology). Har yanzu ana cikin neman ilmin ne. Ina kuma koyarwa a Kwalejin Kimiyyar Lafiya (College of Health Sciences and Technology) da ke garin Tsafe, a jihar Zamfara. Ina da aure da ‘ya’ya.

Tambaya: A wacce shekara ka fara rubutu? Kuma me ya ja hankalinka har ka fara rubutun?

Amsa: Na taso da sha’awar karance-karance tun a firamare, wannan ya sa mini sha’awar zama marubuci wata rana. Kuma na fara jarraba rubutun tun a wancan lokacin, sai dai ni kaina a yanzu ba zan iya tuna wane labari ne na rubuta ba. Zan iya cewa na fara rubutu gadan-gadan ne a shekarar 2013 bayan wani kwas da Shehin Malamin Hausa, Farfesa Ibrahim Malumfashi ya yi mana, tare da wasu marubutan da yawa, a wata makarantar da ya buɗe a Fesibuk mai suna MAKARANTAR MALAM BAMBADIYA. A shekarar ne na shiga gasar gajerun labarai da makarantar ta shirya wa ɗalibanta, kuma Allah da ikonsa labarina ya zo na ɗaya. To, tun a lokacin na tsunduma harkar rubutu. Na shiga gasar rubututtuka iri-iri, kuma duk gasar da na shiga, labarina na fitowa cikin goma na farko da ake zaɓa.

Tambaya: Wanne irin ƙalubale ka fuskanta a harkar rubutu, kuma ta wacce hanya ka bi har ka tsallake?

Amsa: To, ni dai sabon marubuci ne, ba kamar yadda ku ka yi ta kururutawa ba, wai shahararren marubuci. Don haka har zuwa yanzu babu wani ƙalubale da na fuskanta, idan ma har akwai shi, to bai wuce na rashin wadataccen lokacin da zan yi rubutun ba.

Tambaya: Zuwa yanzun littattafai nawa ka rubuta? Kuma za mu so mu ji sunayensu.

Amsa: Yawancin rubutuna duk gajerun labarai ne. Gaskiya suna da yawa, sun kai hamsin ko sun fi, akwai waɗanda na ci gasa da su. Kaɗan daga cikinsu su ne:

  1. Ƙaddara Ta Riga Fata
  2. Sauyin Rayuwa
  3. Sawun Ɓarawo
  4. Ƙabilanci
  5. Goje Mai Dawa
  6. Malam Dudu
  7. Mahaƙurci Mawadaci
  8. Kowa Ya Ƙi Ji
  9. Fadar Barci
  10. Hikayar Ali Baba

Da saura da yawa.

A littafai kuma kammalalle, sai littafin Labarun Dare Dubu Da Ɗaya da muka sabunta fassararsa tare da Ɗanladi Haruna ƙarƙashin jagorancin Prof. Malumfashi. Littafin zai kai mujalladi goma, yanzu haka mujalladi na farko na kasuwa, na biyu zai shiga kasuwa daga yanzu zuwa kowane lokaci.
Akwai kuma wasu littafan da nake rubutawa, Burgami da kuma Ƙarkon Kifi da wasu da dama.

Tambaya: Wanne littafi ka fi so a duk cikin litattafan da ka rubuta, kuma me ya sa?

Amsa: Littafin Dare Dubu Da Ɗaya, saboda shi shi littafin sha-kubdum ne a ɓangaren adabi, babu irin labaran da babu a ciki, kamar: soyayya, jarunta, addini, tafiye-tafiye, bokanci, labarin aljanu da ifiritai, kai hatta labarin halittun da ke ƙarƙashin teku da labarin halittun da ke sararin Subuhana duk akwai. Shi ya sa na fi son wannan littafi fiye da kowane.

Tambaya: Wanne littafi ne ka taɓa karantawa da ya fi burge ka?

Amsa: Akwai su da yawa, amma na fi son karanta littafin MAGANA JARI CE.

Tambaya: Idan za ka yi rubutu, shin ka kan tsara komai da komai ne kafin ka fara ko kuwa kai tsaye ka ke farawa?

Amsa: Eh nakan tsara yadda farko da tsakiya da ƙarshen labarin zai kasance a cikin raina, daga nan sai na soma rubutu. Sai dai wani lokaci kuma wani abun kan faɗo wanda ban tsara da shi ba, kuma duka zan sanya a cikin labarin muddin dai zai ƙara wa labarin armashi.

Tambaya: Ya ka ke yi idan wani tunani sabo ya zo maka game da wani rubutu na daban alhalin kana tsakiyar rubuta wani. Ka kan saki wancan ne ka yi wannan sabon ko kuma sai ka gama da wanda ka fara?

Amsa: Duk na kan haɗa biyun ko ma fiye da haka. Domin sakin sabon tunani lokacin da ya zo zai iya sa mutum ya manta da shi.

Tambaya: Ka kan ɗauki kamar tsawon wane lokaci kana bincike kafin ka fara rubutu, kuma daga nan yakan ɗauke ka tsawon wane lokaci kafin ka kammala rubutun littafin?

Amsa: Gajeren labari yakan ɗauke ni daga kwana ɗaya, kwanaki uku har zuwa sati guda ko ma fiye da haka, ya danganta da yawan kalmomin labarin da nake so na rubuta da kuma irin kwalliya ta karin magana da salon magana da nake so na sanya a cikin labarin. Akwai wani irin labari da ake cewa Flash Fiction da Turanci, wanda kalmominsa ba su wuce ɗari biyar (500) ba, irin wannan a cikin sa’a ɗaya ko biyu nake rubuta shi. Littafi kuma daga wata ɗaya har zuwa shekara ɗaya ko ma fiye da hakan yake ɗaukata.

Tambaya: Wanne littafi ne ya fi ba ka wahala daga cikin dukkan litattafan da ka taɓa rubutawa?

Amsa: Babu wanda ya ba ni wahalar rubutawa, idan ma akwai wahalar ba ta wuce ta zaunawa a rubuta ba.

Tambaya: Wani lokaci kan marubuci kan cushe har ya kasa rubuta komai. Shin ka taɓa shiga irin wannan yanayin? Kuma ta wace hanya ka bi wurin magance hakan?

Amsa: Eh akan samu haka, tunani ya tsaya cak. Nakan ajiye rubutun gefe, sai na ci gaba da wani can daban wanda tunaninsa bai tsaya man ba, duk lokacin da tunanin wancan ya dawo sai na ci gaba da shi.

Tambaya: Yanzu lokaci ya canza, haka zalika al’amura da dama na mutane su ma sun canza wanda na wasu yake zuwa a karkace, har ta kai ga yanzu rubutun littafin batsa abun so ne ga wasu mutanen. Shin wane kira za ka yi wa irin waɗannan marubuta?

Amsa: Su ji tsoron Allah a dukkan rubutun da za su yi. Magana ma da mutum ke yi, akwai mala’ikun da ke rubutata su ajiye, to balle wanda ya rubuta da alƙalaminsa, iyaka su yi copy and paste a cikin littafinsa. Kuma ko bayan mutum ya mutu duk wani rubutu da ya bari a duniya, har kuma rubutun nan ya yi sanadin saɓawa Allah, to kuwa marubucin na da nasa kamasho da zai isko shi har cikin ƙabari. Haka kuma duk wanda ya yi rubutun da aka karanta aka yi amfani da shi ta hanyar da ya dace da addini, to yana da nasa kaso. Don haka marubuta su ji tsoron Allah, su san abin da za su rubuta.

Tambaya: Ka samu nasarori da dama duba da irin littafan da ka ke yi irin waɗanda mutane ba sa gajiya da karantawa ne, kuma suna daga cikin waɗanda suka yi suna, kusan duk mai karatun litattafai na Hausa ya san su. Shin waɗanne irin nasarori ne ka samu wajen rubutunka?

Amsa: Gaskiya ne, na samu nasarori da dama ta hanyar rubutu. Na haɗu da manyan mutanen da ban yi zaton zan haɗu da su ba. Na samu kyautuka da dama daga gasa daban-daban da na yi nasara. Mutane da dama sun san sunana kodayake ba su taɓa gani na ba. Kusan kullum sai na samu kiran waya daga mutane na jihohi daban-daban, suna kira ne kurum domin mu gaisa. Alhamdulillah, rubutu ya yi mini komai.

Tambaya: A naka ra’ayin, tsakanin rubutun online da bugun littafi na hannu wanne ya fi ma’ana da tsari?

Amsa: Rubutun littafi ya fi tsari da ma’ana, saboda shi sai an ba wa wasu sun duba sun yi editing kafin a sake shi a kasuwa. Amma na online ya fi yawan makaranta, amma kwamacala ta fi yawa a ciki.

Tambaya: Wasu mutanen suna tunanin cewa babu abin da rubutu yake jawowa sai ɓata tarbiyya. Shin wacce shawara yakamata a dinga ba irin waɗan nan mutanen?

Amsa: Eh to, da ma wasu ke ɓata wasu. Wataƙila irin waɗannan mutanen suna la’akari ne da irin littafan da ake rubutawa yanzu, waɗanda mafi yawancinsu babu komai a ciki sai soyayya da batsa, ko ni ba zan goyi bayan a karanta su ba. Amma akwai littafai da dama waɗanda ke koyar da abubuwa da yawa musamman tarbiya da zamantakewar yau da kullum, irin waɗannan suna da matuƙar amfani wajen saita rayuwar al’umma.

Tambaya: Shin ya ka ke ganin tafiyar Adabin Hausa? Ma’ana, irin ci gaban da aka samu game da shi a yanzu?

Amsa: To, Adabin Hausa, musamman rubutataccen Adabi da muke magana a kai yanzu, zan iya cewa an samu ci gaba amma na mai haƙar rijiya. Ci gaban kuwa shi ne, kullum garin Allah ya waye akan samu sabbin marubuta, akan kuma samu sabbin littafan da ke shiga kasuwa. Sai dai ba yawan abu ne ci gaba ba, nagartarsa shi ne abin dubawa. Ance da haihuwar yuyuyu gara ɗa guda ƙwaƙƙwara. Mafi yawancin marubuta yanzu ba su san ma me su ke rubutawa ba, da yawa ba su kiyaye ƙa’idojin rubutu balle Nahawun Hausa, maimakon a yi abin da ɗalibai za su yi nazari a makarantu, sai a yi abin da zai ƙara rikirkita su. Sannan littafan da ake rubutawa duka masu gajeren zango ne, idan littafi ya fito wannan shekara, da an shekara biyu ko uku, sai a neme shi a rasa, ya ɓata bat, wani lokaci har a wajen marubucin ba za a samu kwafi ba. Shi kuwa littafi tamkar wata ma’ajiya ce ta al’adun zamanin da aka rubuta shi, wanda idan aka ɗauka aka karanta, za a ga hoton yadda wannan al’umma ta tafiyar da tsarin rayuwarta.

Tambaya: Wacce Karin Magana ka fi so? Kuma me ya sa?

Amsa: Suna da yawa, amma kuma ina son wannan: bari in yi, ba ta yi sai an yi. Karin maganar na nuna cewa idan mutum ya yi nufin yin wani abu to ya zage damtse ya yi abun, zai ga nasara in sha Allah. Amma idan mutum ya tsaya inda-inda ko shawarwari, to babu abin da zai yi har lokacin abin ya zo ya wuce.

Tambaya: Shin kana da wani maigida da yake nuna maka harkokin rubutu?

Amsa: Eh, a’a. Na zama marubuci ne ta dalilin wata makaranta da Farfesa Ibrahim Malumfashi ya buɗe a Facebook mai suna MAKARANTAR MALAM BAMBADIYA. Manufar buɗe makarantar kuwa shi ne domin samar da sabbin marubuta da kuma ƙara wa tsofaffin marubuta ilmi. To ina cikin sabbin marubutan da makarantar ta ƙyanƙyashe. Idan har ina da maigida a rubutu, zan iya cewa Prof. Malumfashi ne mai gidana kuma Malamina.

Tambaya: Shin ko akwai wani labarin da ka ke rubutawa a yanzu haka da masoyanka za su yi tsumayin fitowarsa?

Amsa: Eh, akwai su da yawa.

Tambaya: Wacce irin shawara za ka iya ba wa sabbin marubuta masu tasowa?

Amsa: Ni ma ai ƙaramin marubuci ne. Shawarar da zan ba ire-iren mu shi ne, mu tsaya mu rubuta abin da zai amfani al’ummar mu, ya kuma amfane mu ko bayan ranmu. Sa’annan duk rubutun da za mu yi mu riƙa yin bincike a kan abin da ba mu sani ba kafin mu rubuta shi, ban da rubuta ƙarya ko shaci-faɗi a cikin labari. Kodayaushe marubuci ya kasance shi ke juya akalar mai karatu, ba wai mai karatu
ya kasance shi ke juya marubuci ba.

Tambaya: Daga ƙarshe, me za ka iya cewa game da Bakandamiya Hikaya?

Amsa: Wannan wani babban yunƙuri ne ko babbar gudummuwa da wasu masu kishin Hausa suka fito da ita domin bunƙasa harshen Hausa da adabin Hausa a duniya. Kuma wannan abu zai taimaka, ko ma yana taimaka wa marubuta sabbi irinmu, har ma da tsoffin, wajen tallata littafansu a ko’ina cikin duniya. Kuma wuri ne da tsoffin marubuta ke ba sabbin marubuta darussa da shawarwari domin inganta rubunsu. Madalla da samun wannan shafi na Bakandamiya wanda muke fata nan gaba ya zama tamkar Fesibuk ɗin Hausawa.

Tsara tambayoyi da gabatarwa: Maryam Haruna tare da Hauwa’u Muhammad.

Tacewa da sabuntawa: Jamilu Abdulrahman (Haiman Raees)
19-08-2023

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page