Skip to content

Bita akan rubutun gajeren labari 2

Kuna iya karanta darasin ranar farko kafin ku ci gaba da wannan.

RANA TA BIYU

Darasi na 1

Abubuwan lura a rubutun gajeren labari

A jiya mun bayyana siffar gajeren labari ta fuskar adadin kalmomi. Mun riga mun san cewar shi Rubutu baiwa ne. Ba kowa ke da baiwar rubutu ba. Duk da haka akwai hanyoyin da ake bi domin karawa rubutun armashi da inganci.

Mun fahimci cewar shi gajeren labari ya fiye tsarabobi, wajibi ne a bi matakan da aka shardanta musamman idan kana yin rubutun ne domin shiga gasa.

Yau za mu tattauna ne akan wasu ka’idoji da mai rubuta gajeran labari zai lura da su. Za mu kawo misali idan ta kama. Wadannan kaidoji ba sharadi ba ne, amma suna daga cikin manyan abubuwan da suke karawa gajeren labari armashi har ya zama ya karbu. Bari mu soma jero su kamar haka:

1. Amfani da zababbun kalmomi
2. Zaben waje da muhalli da lokaci
3. Bai wa manufa muhimmanci
4. Fayyace tauraro da irin burinsa
5. Maida hankali kan jigo
6. Takaitawa – Siffantawa, Yawan Taurari, Yawan
7. Bayyana aikatau

Za mu dauki kowanne mu yi bayani tare da misali a darussa masu zuwa.

Darasi na 2

1. Amfani da zababbun kalmomi

Rubutun gajeren labari na bukatar yin nazari bisa kalmomin da za a saka masu ma’ana. Duk kalmar da za ka saka sai ka yi tunanin irin tasirin ta a labarin da kuma yadda mutane za su gane abin da kake nufi da hanzari.

Ɓarna ce kwarai ka tsaya ƙaƙaro kalmomi masu sarkakiya matukar akwai masu sauki a kusa. Akwai wasu kalmomi da asalinsu ba Hausa ba ne, amma an mayar da su cikin Hausar har sun zama sabagiji, ya fi ka yi aiki da su maimakon bata lokaci wajen fassara.

Misali:

Talabijin Maimakon Rediyo mai hoto

Kurkuku/Yari/Fursun
Maimakon
Gidan bada horo/Gidan gyaran hali/Gidan maza

2. Zaben waje da muhalli

Ana so a dan takaitaccen bayani ka nunawa mai karatu wuri ko yanayi ko muhallin da labarinka yake. Ba a so ka tsawaita wajen kawo tarihin wajen ko siffanta yadda yake ko abin da ake aiwatarwa. Koda ya zama wajibi ka kawo abubuwan, sai ka rubuta su a takaice.

Bari mu yi misali da wani muhalli a dogo da gajeren labari domin fahimtar manufa.

Dogon labari

Faffadan wajen mai girman kimanin kafa dari biyu kusurwa huɗu. Kananan kujeru ne a jere kowanne an makala ‘yar takarda mai dauke da sunan wanda aka tanadarwa. Daga can gaba kuma, wasu manyan kujeru ne na alfarma cikin sahu biyu. Da alama na manyan mutane ne. Babba ma ashe da babbansa, cikin wadannan kujerun akwai wata a tsakiya wadda ta fi su girma da ado da kyau. An yi mata wani irin zane da ruwan zinariya sai daukar ido take, ga wasu irin matasai na gashin jimina an dora hagu da damanta. Kai da gani ba sai an fada maka ba, wannan ita ce kujerar da aka tanada ta musamman domin mai martaba Sarki, yana da matsayi biyu a wannan muhimmin taro. Na farko shi ne shugaban makarantar domin shi ne ya fara karfafawa iyayen yara gwiwa suka bude makarantar kuma da kansa ya jagoranci taron ta na farko. Na biyu kuma, a yau shi ne uban taro sai abin da yake so za a aiwatar.

Bari mu takaita wannan wajen zuwa gajeren labari

Gajeren labari

An cika babban dakin da kujeru, kuma kowacce kujera an rubuta sunan wanda zai zauna akai. Can gaba kuma manyan kujeru ne na alfarma domin manyan baki. Babbar kujera mafi kayatuwa ita aka ware musamman domin mai martaba sarki wanda yake uban taro kuma shugaban makaranta.

Kun ga mun bayyana wancan dogon labarin a takaice kuma an fahimta kamar yadda yake a dogon labarin

Darasi na 3

3. Bai wa manufa muhimmanci

Yana da kyau tun a sadarar farko mai karatu ya gane manufar rubutunka. Ana so ka zamana ka ambaci wani abu da zai sa a gane cewar labarin nan akan abu kaza yake magana. Anan ba ina nufin bude hanjin labarin ta yadda mai karatu zai yi hasashen karshensa ba watau ‘pre-emptive’.

Misali. Dubi farkon bude wannan labarin:

“Ban san talaka sarki ba ne, sai da na shiga siyasa. A da na dauki talaka ba a bakin komai ba, sai ga ni ina yawo kwararo-kwararo ina durkusawa ina gaishe su. Duk inda na ji labarin biki ko suna ko mutuwa sai na yi maza ni da yarana mu riga kowa zuwa. Idan mun ga ana dariya mu ma mu fashe da dariya, idan kuka ake yi mu fi kowa kururuwa.”
– MM Karami

Daga karanta wannan sadara ta sama za mu fahimci cewar labari ake akan wani dan siyasa mai neman kuri’a. Mai karatu zai so jin karshen labarin yadda ta kaya.

Ana so kowanne sakin layi ya zama akan manufar labarin ne bai karkace zuwa wani abu ba kamar yadda ake yi a dogon labari.

4. Fayyace tauraro da irin burinsa

A gajeren labari, wajibi ne a nuna babban tauraro da irin abin da yake burin samu. Mun san cewa tauraron labari shi ne wanda yake da bukatar samun cimma wani buri amma wasu abubuwa suna kawo masa cikas. A gajeren labari ana so mai karatu ya fahimci irin burin tauraro cikin hanzari. Ga misalin wani gajeren labarin:

“ Tun ina ‘yar karama bana kaunar wannan aba wai ita tururuwa,idan daya ta cije ni to duk inda na ga danginta a ranar to sunanta gawa.

Abu har yakai ga girmana bana tausayin Tururuwa, su kuma iyayena basu damu dasu tsawatar dani hakan ba dan basa kaunar bacin raina.”

Mai labarin ya nuna yadda tauraruwa ke tsanar tururuwa da irin azabar da take gana musu.

Kenan ba a bukatar a gajeren labari a tsawaita wajen nuna burin tauraro kamar yadda ake yi a dogon labari.

5. Mai da hankali kan jigo

Manufar tauraro ita za ta bayyana jigon labarin. Ana so marubuci ya fito da jigon sosai yadda mai karatu zai gane. Ba kamar a dogon labari ba inda marubuci zai boye jigonsa cikin kananan jigogi, an fi so a bayyana a zahiri ko a aikace yadda kowa zai gane. Kana iya fito da manufarka ta hanyar da ka so watau, ko dai ta hanyar bayani ko aiki ko kuwa maganar tauraro. Haka kuma ana iya nuna jigon labarin tun daga takensa.

Bari mu buga misali a Sabon Post na wani gajeren da na ciro da Littafin Tekun Labarai.

Darasi na 4

Karanta wannan labari ka yi nazari kan jigonsa

SHARI’A SAB’ANIN HANKALI KUMA DAIDAI HANKALI

Wani buzu ya yi laftun kayan kanwa ya nufo k’asar hausa domin ya sayar. Duk kasuwar da ya je, yadda ya baza kanwar haka yake nad’ewa babu mai saya. Dalilin haka kuwa saboda furucin tallan da yake yi ya sa mutane k’auracewa kanwar. Abin da yake cewa kuwa shi ne, “a zo a yi magana a sha dukan kanwa.” Duk wanda ya ji haka sai ya kauce musamman da jama’a suka ga yana rataye da zabgegen takobi. Shi nufin wai a zo a taya a saye kanwar duka a sari.  

Ya yi ta yawo tsakanin manya da k’ananan garuruwa tun daga Sabon birni ya keta har ya isa wani k’auye da ke cikin k’asar Kano ana kiransa Tarau.  Ya baje hajarsa a kasuwa yana  mai addu’ar Allah ya kawo wanda zai saye kayan ya huta da d’awainiya.

Ya zauna tun safe har yamma babu wanda ya ce da shi ‘ci kanka’, har ya soma  shirin nad’e kaya sai ga wani mutumin Zazzau ya je wajensa ya ce, “Nawa za ka sayar min da laftun nan duka?”Ya ce, “fad’i da kanka mu ji.”

“na saya fam biyar.”

“Albarka.”
“Na k’ara fam biyu.”
“Albarka.”

Mai sayen kaya ya ce, “na saya fam goma, amma daga haka ba zan k’ara maka komai ba  sai babu.” Mai kaya da ya ji haka sai ya ce, “na sayar maka akan fam goma da babu.” Mai saye ya ce, “zan tafi da kaya rana wa ta yau zan kawo maka kud’in.”

Bayan kwana bakwai ya kawo masa kud’insa. Buzu ya k’irga ya ga sun cika fam goma cif. Sai ya ce, “kud’i sun cika, saura ka bani babu kamar yadda ka yi alk’awari.”

Mai sayen kaya ya yi dariya ya ce, “dama babu na ce zan baka, kuma babu tana nufin babu komai kenan.” Buzu ya b’ata rai ya ce, “ka bar yi mini maganar banza, na sayar maka da kayana bisa sharad’in za ka k’ara min da babu. Idan ko ba haka ba ka dawo min da kayana ga kud’inka nan.” 

Wasa wasa dai magana ta zafafa, suka rik’a musayar maganganu suna d’aga murya kamar za su yi fad’a. Mutane suka taru suna k’ok’arin sasanta su. Da abin ya faskara sai aka d’unguma da su wurin sarkin kasuwa. Sarkin kasuwa ya rasa yadda zai b’ullowa shari’ar musamman da buzu ke ta hak’ik’icewar sai an ba shi hak’k’insa. Sai cewa yake, “don kurum kun ga ni bak’o ne za ku zalunce ni?”

Da ya ga cewar ba zai iya sulhunta su ba sai ya kwashe su zuwa wurin Hakimi mai kula da yankin k’asar Tarau ana yi masa lakabi da Sarki. Lokacin kuwa fada ta cika da makad’a da mawak’a da masu algaita suna  zarya suna zuga Sarki.

Da Sarki ya ji wannan zance, sai ya yi shiru yana tunani, ya dubi mai kaya ya ce, “shin ya ba ka kud’in da kuka yi ciniki?” Ya ce, “na’am ya ba ni, amma a cinikin ya ce, zai k’ara min da babu kuma a haka muka k’ulla yarjejeniya.”

Sarki ya fusata ya ce, “kai wanne irin mutum ne? Wa ka ga an ba shi babu kamar yadda kake wassafawa?” Mai kaya ya ce, “Allah ya baka sa’a kan mak’iya, ni fa wayayye ne d’an wayayyu. Kuma na fi shekara talatin ina saye da sayarwa. Don haka a ba ni hak’k’ina kamar yadda shari’a take bisa adalci.”

Sarki ya rasa yadda zai b’ullowa al’amarin. Ya yi shiru yana tunanin yadda sai yi da hak’ik’icewar da buzu ke yi. Gaisuwar da wani makad’I ya yi gare shi ne ya dawo da shi daga duniyar tunani.  

Shi wannan makad’in ganga mai suna Abul K’asimu, yana cikin cashewa da kalangu aka zo da wannan shari’ar. Don haka sai ya bar abin da yake yi ya shiga cikin ‘yan kallo.

Da ya ga al’amarin ya cukurkud’e sai ya tafi ta gangarsa a kafad’a ya durk’usa gaban Sarki ya ce da murya k’asa k’asa yadda babu wanda ya ji shi sai Sarki, “Allah ya ja kwananka, a ba ni izni na yi wannan hukuncin, domin na lura da’awarsu ba ta biyo cikin littatafan shari’a ba, sai irin namu littatafan na ‘yan duniya.”

Sarki ya ce, “na ba ka izni, amma idan ka kasa yin hukuncin adalci, za ka d’and’ana kud’arka.”


Makad’i Abul K’asimu ya zauna kujera ya ce, “a kawo min daro cike da ruwa.” Aka kawo masa. Ya dubi wanda ya sayi kaya ya ce, “a cinikinku ka yi masa alk’awarin za ka ba shi babu. Haka ne?” Ya ce, “haka ne.” Ya waiwaya ga mai kaya ya ce, “Shin ya baka kud’inka amma bai baka babu ba?” Ya ce, “na’am, kuma mun yi yarjejeniya ne kan fam goma kuma ya amince zai k’ara min da babu. Daga baya sai ya hana ni. Wannan wanne irin zalunci ne haka?” Ya ce, “tunda haka ne mu za mu karb’ar maka hak’k’inka  yanzun nan kamar yadda kuka yi alk’awari.” Ya dubi mai sayen kaya ya ce,  “Dank’e hannayenka da kyau.” Mai sayen kaya ya dank’e hannaye.

Ya ce, “sake dank’ewa dai.” Ya dank’e. Ya ce, “dandank’e da kyau sosai.” Yayin da ya tabbatar ya dank’e hannunsa sosai, sai ya ce, “to tsunduma hannayenka duka suna dank’e cikin wannan ruwan.” Mai sayen kaya ya aikata kamar yadda aka umarce shi. Bayan wani lokaci mai shari’a ya ce, “to fito da hannayenka.” Ya fito da su alhali suna dank’e. Ya ce, “to mik’a duk abin da ka dank’o ga abokin cinikinka.” Ya mik’awa bak’auye hannunsa a dank’e har suka yi musabaha sannan ya bu’de.

Alk’ali makad’i ya dubi bak’auye ya ce, “shin ya ba ka wani abu da kuka gaisa?” Ya ce, “eh na ji danshin ruwa a hannunsa amma babu komai.” Alk’ali ya ce, “wannan ita ce babun da kake buk’ata, don haka d’auki babunka ka kama gabanka.” Ya juya zai tafi kenan sai Sarki ya ce da shi, “shin ka gamsu da wannan hukuncin?” Ya ce, “na gamsu, tun da an bani hak’k’ina.” 

Jama’ar da ke wurin gaba d’aya suka fashe da dariya har da Sarki. Ya sa aka yi wa makad’i kyautar kud’I da tufafi ya sallame shi. Don haka masu iya magana ke cewa, shari’a ta sab’awa hankali, amma wasu kuma suna cewa shari’a ta yi daidai da hankali. Duk ma’anar da ka d’auka, haka shari’ar take.

Wannan labari ya nuna mana jigonsa tun daga takensa, kuma aka sake jadadda haka a karshen labarin.

Darasi na 5

6. Takaitawa – Siffantawa, Yawan Taurari, Yawan Zance

Duk sharadan nan da na ambata suna karkata ne ga takaitawa. Daya daga manyan abubuwan da ake so a takaita su ne siffanta kamannin tauraro.

A dogon labari ana so kowanne tauraron da zai taka rawa a labarin ya zamana an san kamanninsa da irin dabiunsa. Amma a gajeren labari idan aka nuna tauraro da irin abin da ya sa gaba kadai ya wadatar. Kana iya ambata kamannin tauraro ta yin nuni da halayyarsa ko sunansa. Misali a ce sunan tauraro, Malam Kazallaha. Daga jin sunan za a fahimci mutum ne mai karambani. Ko kuwa a ce, Alhaji Mai Dariya, mai karatu zai gane cewa tauraron yana da fara’a ne. Haka kuma kana iya kawo siffar tauraronka a takaice yadda mai karatu zai gane irin yanayin da tauraron ke ciki.

Bari mu dauko misali daga wani gajeren labari;

Motocin na tsayawa sai wani mutum gajere tutturna, mai siffar ‘yan dambe sauko tare da yaransa su biyu. Maigari da mukarrabansa suka yi musu maraba. Bayan tattaunawar kankanin lokaci, Maigari ya yi wa mutanensa fatan alheri tare da shaida musu irin aikin da za su yi a birni da kuma alkawarin da kamfani ya yi musu.
“Ku sani aikin nan mun jima muna neman muku, sai yanzu ya samu alhali kuma an soma samun ruwan sama, to haka Allah ya tsara. Muna fatan ku dawo mana da arzikin da zai magance matsalar da kauyenmu ke ciki sakamakon karancin ruwan sama da aka yi bara.” Yana gama bayanin sai sai aka soma kiran suna. Duk wanda ya ji sunansa sai ya shiga mota ya zauna.

7. Bayyana aikatau

Bayyana aiki ba tare da magana ba yana rike makaranci. A gajeren labari yana da matukar amfani a nuna yadda aiki ke gudana ba tare da tsoma bakin tauraro ba.

Bari mu yi misali da wani gajeren labari:

Ba mu yi nisa sosai ba motar ta fara tangadi saboda rashin kyan hanya. Ga kwazazzabai ga kura duk ta cika mana ido. muka rinka hantsilawa daga wannan gefe zuwa wancan. Kowa daga cikinmu ya shiga  kokarin samun madafa, wasu naga har sunyi tsalle sun dira waje. Nima nayi yunkurin haka, amma da naga wani yaro ya dira ya kwanta shiru na saddakar babbar kasada ce.

Cikin sa’a na kama wani guntun katako dake jikin bodin gam.  Naga wata mata ta zama kamar wani kuli – kuli, idan motar ta jirga gefe guda ita ma sai ta fada nan. Wata hantsilowa da motar tayi kamar zata kifa, matar ta samu sa’ar kamo kafafu na ta rike, yayin da ni kuma nake reto kamar jemage. Naji karfina ya dada raguwa, hannuna ya kama rawa saboda fisga ta da ake ta baya musamman idan motar ta jirkita bari daya. Hannuna daya ya kufce daga inda na makalkale.

A cikin haka wani daga cikin daurin kayan dake sama ya kwance, ya fado min a hannun da nake rike da bodin motar. Nayi kasa tim na fadi, kayan suka zubo kaina, suka danne ni. Nan da nan naji numfashina na barazanar daukewa. Har na soma ganin wasu taurari na zagaya ni. Ban san yadda aka yi ba naji motar ta tsaya cik, naji wasu na magana suna dariya….

Ku ci gaba da karatun darasin rana ta uku.

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page