Kuna iya latsa nan don karanta darasin rana ta hudu.
RANA TA BIYAR
Darasi na 1
Misalan gajerun labarai
Yau ce rana ta karshe a wannan bita. Inda da yardar Allah za mu kawo misalan gajerun labarai domin gane yadda aka tsara su.
Kowanne labari muka kawo za a bayar da dama a yi nazarinsa kafin a kawo na gaba. Za mu kawo labari guda biyar daga marubuta daban – daban.
Labaran da za mu kawo, wasu cikakku ne wasu kuma tsakure.
Daga bisani kuma za mu ware lokaci domin yin tsokaci ga bitar baki daya.
Kila za mu wuce lokacin rufewa a yau.
Muna gayyatar ku.
LABARI NA 1
Hausa Mai Dole Na Danladi Haruna
Lokacin da aka ƙaddamar da Shari’ar Musulunci a jihar Kano, sai muke ta fargabar shiga jihar daukar fasinja domin gudun shan bulala yadda muka ji ana fada.
Na san Kano ana mata kirarin cewa ko da me ka zo an fi ka. Sai na shiga tunanin abin da zan yi da zai fi Kano da Kanawa musamman ta fuskar sana’ata ta tuki.
Daga bisani na sa aka rangada min wata kalma da na tabbata kowanne musulmi zai yi amanna da ita. Aka yi rubutun da manyan baki yadda ko daga nesa ka kalla za ka iya karantawa dalla – dalla. Na zunguri mota sai Kano cike da takama.
Duk inda na wuce sai na ga mutane suna kallon motar suna mamaki. Ni kuwa sai na ji dadi ya kama ni, domin a zatona na zo da wani sabon salon rubutu mai jan hankalin da babu wani direba da ya yi kamar sa. Na yi ta tuki har na isa tasha na sauke fasinja, sannan na samu waje na hakimce ina nazarin mutanen da suke taruwa suna kallon rubutun motar.
Can wani daga mutanen ya ɗaga murya ya ce, “wai shin motar nan ta wane ne?” Na yi zumbur na mike na je, wai a zatona za su yaba min ne a gaishe ne ko samari su yi mini kabbara albarkacin Shari’ar Musulunci da na yi wa ladabi a rubutun da na yi a jikin motata.
To amma maimakon haka, ban yi aune ba sai na ji saukar mari. Mutane suka dirar min da duka da naushi da zunguri. Tun ina karewa har na daina na mika wuya ga mutuwa. Allah da ikonsa ban san yadda aka yi ba na ji an daina dukana.
Na fahimce cewar wani dattijo ne ya tsawatar aka daina jibga ga. Mutane suka taitaye ni jina – jina aka jingine ana min firfita. Bayan wani lokaci aka shiga bibiyar musababbi. Samarin nan suka ce wai saɓo na aikata. Mummunan zunubi wanda ba wanda ya aikata kamar sa a duniyar musulunci.
Na dube su na ce, “tsakani da Allah wanne irin zunubi na aikata?”
Wani mai zafin kai ya yi farat ya ce, “kai kafirin ina ne? Dubi abin da ka rubuta a jikin motarka. Ka ce, BAWAN DA YA FI ALLAH kai ɗan sarkin kafiran ina ne za ka shigo mana gari? Watau ka yi karfin da ka fi Mahalicci? Tir da kai da takamar ka!”
Da na ji haka sai na yi salati ina sallalami na ce, “wallahi tallahi ba nufina haka ba. Ina nufin BA WANDA YA FI ALLAH ma’ana duk karfin mutum da isar sa bai yi kamar Allah ba.” Mutane suna jin haka sai suka shiga hayaniya tsakaninsu. Wasu na karyata ni wasu kuma suna gaskata ni.
Na roki dattijon nan ya rokar min alfarma aka yi shiru. Na ce, “na fahimci rashin bin ka’idojin rubutu ne ya jawo min haka, inda na hade kalmar da bai kamata na hade ba. Hakan kuma ya bada ma’ana ta daban. Ina rokon a yi min alfarma na goge rubutun nan na sake wani.” Kafin na rufe baki tuni wasu matasan sun hau kan fentin nan sun kankare sarai har da jirkita kamannin motata.
Haka na fita daga tasha ba fasinja, jikina ya yi rudu – rudu. Sai da na kwana uku ina jinya sannan na warware.
Daga lokacin na kuduri aniyar komawa makaranta inda na dage sosai wajen nazarin rubutun Hausa tare da dukkan ka’idojin ta.
LABARI NA 2
Haihuwa Nufin Allah Na Sadiya Garba
Kimanin shekaru bakwai da yin aurena amma ko batan wata ban taba yi ba ballantana a sa rai da haihuwa. Ga shi sai kumbura na ke kamar huhulahu, tun mutane na tsammanin ciki ne ke sa ni kiba har aka gaji aka daina, aka koma gulmar wai juya ce ni. Abin mamakin shine duk sa’annina da aka yi mana aure lokaci daya sun hayayyafa. A lokacin bikinmu, mu takwas aka sa a lallai gaba daya, a gidanmu ni da kanwata ne, sai bayan layinmu wasu kawayenmu su biyu sannan mijina da dan uwansa suka yi aure ga kuma wasu uku da aka hada mu gaba daya. Duk ragowar bakwan sun haihu har da facalata wadda ta fi kowa yawan ‘ya’ya. A lokacin ‘ya’yanta hudu; biyu maza biyu mata. Kanwata kuwa ‘ya’yanta uku, an sha jefa min maganganu masu daci da yarfe, an sha zuga mijina kan ya kara aure, wasu ma cikin danginsa sun daina shiga huldarsa saboda wai na shanye shi na hana shi kara aure ni kuma babu haihuwa sai ci kamar gafiya. Ni da mijina auren soyayya muka yi wadda ta shafe shekaru uku muna kasafin yadda rayuwar mu zata kasance, yadda za mu kula da gida da tarbiyyar yara sai ga shi shekaru shida ba amo ba labari. Wannan abu na matukar kona min raina.
Mijina yana matukar kula da ni, kusan sai na ce shi kadai ne cikin danginsa wanda bai guje ni ba kuma ya ke karfafa min gwiwa a duk lokacin da na samu kaina cikin damuwa. Mafi yawan lokuta idan abin ya dame ni sai na shige daki na yi ta rusa kuka har na gaji tukunna na share hawayena. Wani lokaci idan muna tattaunawa game da matsalar ya kan nuna cewar ba laifina ba ne laifinsa ne.
“Ki daina damuwa Amina, haihuwa ta Allah ce, ya kan bayar da ita ga dukkan wanda ya so a lokacin da ya so.” Ya yi ajiyar zuciya ya ce, “na tabbata kafin mu bar duniyar nan sai mun ga k’wanmu.” Na yi ajiyar zuciya na ce, “Mubarak ban ki ta taka ba, amma saboda tsangwamar da danginka ke min da dora min laifin da ban ji ba ban gani ba, ina rokon ka karo aure. Kila a jikin matar da zaka auro rabonka yake ba a jikina ba….”
“A’a Amina” ya katse min hanzari. “Wallahi ban taba yanke kaunar za mu haihu tare da ke ba. Ni ina jin cewa ma matsalar daga wurina take. Da zai yiwu…”
“Babu wani abu mai yiwuwa sai da yardar Allah. Mu je mu ga likita ya ba mu shawarar da ta dace. Idan ma wani abu ne sai a gano.” A wannan daren muka kwana muna kuka muna tausasar juna. Washegari tunda sassafe muka rankaya wajen likita, wani kwararre wajen sani cuce – cucen mata. Ya yi mana wasu gwaje – gwaje kuma ya dora mu kan yadda za mu iya cimma burinmu.
Sai da muka shafe shekara biyu muna zarya wjeny likita amma shiru kamar Malam ya ci shirwa. A tsakanin wannan lokacin babu irin cin fuskar da ban gani ba, daga kawayena har zuwa dangina da dangin miji da sauransu. Babu inda na fi ganin tashin hankali da cin fuska kai tsaye fiye da wanda nake samu daga wajen facalata. Haka kawai muna zaune muna tattaunawa sai ta soma jefa min ‘yan maganganu, tun ba na nakaltar habaici har na soma gane cewar da ni take.
– Daga Littafin Gobarau
LABARI NA 3
Kwallo Ko Annoba? Na Bukar Mada
A karo kusan na biyar, Ashiru, dan kimanin shekara sha biyu, ya kai wa fuskarsa mari domin buge sauron da yake ta faman yi masa jiniya a kunne, wannan karon ma bai yi nasara ba, sai dai sauron ya kara yi masa wata gudar ya yi gaba. Ya yi zugudum yana ta tunani. Ban da sauro ma, tsananin duhun dakin da zafi, sandiyyar rashin wutar lantarki, ba za su bar shi ya runtsa ba. Kodayake ba shi da agogo, amma yana iya kiyasta cewa karfe sha biyu na dare ya yi, tunda tun karfe goma sha daya da ‘yan mintuna aka kammala kwallon kafar.
Ashiru ya sake juya kwanciya daga kan gadonsa, ya dubi duhu-duhun kanensa da ke kwance can gefe, bisa tabarma, yana ta sharbar barci. Ya kuta, sannan ya ce a cikin ransa, ‘ina ma a ce na lalubo dutse lokacin da muke fadan nan, da na fasa wa dan banza kai.” Sai kuma wata zuciyar ta ce masa, “kai sakarai! Idan ka fasa masa kai ya mutu fa? Saboda kwallo za ka kashe abokinka? Ka manta Malam Iro ya ce duk mutumin da ya kashe dan uwansa da gangan, ranar lahira wuta za a sa shi?”
Har yanzu wurin da Salele ya buge shi a gefen idonsa, kafin a raba su fadan, yana yi masa ciwo da zogi. Sannan sai wata zuciya ta ce masa, ‘wannan ita ce ribar da ka fara samu ta wajen kallon kwallo.’ Da ma Malam Iro ya sha fada musu a makaranta, babu wata riba a kallon kwallo, ta gida ko ta Turawa, wadanda ba su ma san wainar da suke toyawa ba. Allah bai halicci mutum da aljani domin wasa ba, sai don su bauta masa.’
Sai kuma ya ji wata zuciyar kamar tana yi masa dariya, tana cewa da shi, “dubi yadda ka bi littattafanka na makaranta ka rubuce da sunan Rooney, har wadansu rigunanka ma ka rubuta masu Rooney, yau ga shi saboda an zagi Rooney, za ka kwana da kumburarren ido, amma dai Salele ya more maka. Wai me ma Rooney ya taba yi maka ne? Ya ma san da akwai wani Ashiru a duniya? An ce wata shekara ma, da ‘yan Manchasta suka zo kasar nan wurin wasan kwallo, shi Rooney da kake so rufe hancinsa ya rika yi da kyalle, don kada ya shaki cuta daga wurin bakaken mutane. To don me kai kake son mutumin da yake kyamar ka?’
A hankali kuma sai tunanin Ashiru ya koma kan kwallon da aka buga cikin wannan dare. An buga kwallon ne tsakanin kungiyar kwallon kafar da yake so, watau Manchasta da kungiyar kwallon kafa ta Asanal. Wasan ya tashi Asanal na da ci biyu, Manchasta kuma na da ci daya. Kodayake dan wasan da yake so ne, watau Rooney, ya ci wa Manchesta kwallo, babban abin da ya fi ba shi haushi shi ne, Asanal ta ture Manchesta bisa tebur, ita ta haye da maki biyu, kuma a Jan Bulo aka yi wasan. Wannan shi ake kira ga mari ga tsinka jaka.
Nan take sai ya ji wata zuciyar na ce masa, “Ashiru wawa! Ashiru sauna! Ashiru duk ya san sunayen ‘yan kwallon Manchasta, da yadda ake hawa tebur, da yadda ake sauka bisa tebur, da yadda ake zuwa raligeshin, amma bai san abubuwa takwas ba, wadanda dole duk wani abu mai rai yake yin su. Kuma bai san sunayen Annabawa biyar ba, wadanda suka fi sauran Annabawa daraja.”
– Daga Littafin ‘Yan Yau.
LABARI NA 4
Na Gama Dariya Na Maimuna Idris Sani Beli
Ina sauka daga Keke Napep na daga kai na sake duban sama karo na sau babu adadi saboda tsumayin bayyanar dare biyu da masana kimiyyar sararin samaniya suka hasashi zai bayyana karfe hudu na yammacin wannan rana. Na balle jaka na biya mai Keken kudinsa sannan na juya na fara cira kafa jiri na dibana, ina debo kai na na cigaba da tafiya tare da kallon sararin samaniya wadda ta hada rai, ina kuma kiyasta cewa, nan da mintuna arba’in ranar za ta kisfe bisa hasashen masanan .
Na sauke kaina kasa na cigaba da jan kafa da sunan sauri. Gabobin jikina dai na kokarin dole sai an ga kuzarinsu amma ina da yakinin karya suke da yaudarar kai domin Uwarsu wato zuciyata ita murtuke take, na tabbatar a cikinta dare goma ake ba wai biyu ba.
Ina shiga layin gidana zuciyar tawa ta kara kuntacewa sannan ta cigaba da bugawa fat! fat! fat! fiye da yadda bugunta ya farkar da ni daddatan baccin da na ke a daren jiya, ciwon kai da kekeshewar idon suka taru suka nuna mana iyakar mu ni da bacci har ma da Maigidana da ya kwana tsaye kaina. Wannan ne ya tilasta min buga sammako na tafi asibiti da sanyin safiya. Na je asibitin likita ya ishe ni da wa’azin kwantar da hankali da na hana kai damuwa, na saurari wa’azin nasa a matsayin sarewar da ta fi shantu zaki sannan na karkade zani na bar masa Ofishinsa, lokaci ne dai ya bata wa kansa dan ban ga yadda za a yi irina a hana ta damuwa ba.
Na dage na runtse ido ruf! na cigaba da tafiya ina laluben hanya har na isa kofar gidana, hikimar rufe idon shi ne kar wata daga cikin makotana ta leko ta matsa min in gaishe ta dole, alhalin na gama cin alwashin ba ni ba makota.
A bude na sami gidan wannan ne ya ba ni shaidar Maigidana ya dawo, na afka kai cikin gida. Haba! ina shiga falo na ci karo da kwanukan da mu ka karya kumallo da yarana biyu da maigidan suna nan inda na bar su sai na ji raina ya kara mugun baci kamar na hadiyi zuciyata na mutu, amma dai na daure na rike ta a rarraunan kirjina na kwashe ta mu ka afka dakin baccin da nake da tabbacin maigidana na ciki. Na same shi kwance rub da ciki a kan gado ya tasa sana’arsa ta catin a facebook ko 2go.
Ko sallama ban yi ba na hau kwance masa cikina cikin zafin rai,
“Yanzu Abban Amir ko dadi ne ya fitar da ni da da sanyin safiya daga gidan nan ya kyautu da ka dawo ka kwanta aikin da babu lada? Ko ba ka shiga Kitchen ka dafa mana abinda za mu rage yunwa ba ai ka dau tsintsiya ka rage nauyin gidan”
Ya dago a firgice ya dube ni lokaci guda kuma yana kokarin kife wayarsa, amma kafin hakan tuni na ga abinda ya ke son boye min wato hotunan `yammata tsirara haihuwar iyayensu Abban Amir ya tasa gaba yana kallo, ga kuma rana a sama na shirin kisfewa ba ya ko tsoron cewa za ta iya zuko shi ta hadiye in ta fusata da fushin makaginta.
– Daga Littafin Hannu Da Yawa
LABARI NA 5
Huhun Ma’ahu Na Danladi Haruna
A shekarar da zan yi ritaya bai fi wata bakwai ba, na samu shiga cikin tawagar mai girma Gwamna muka rika kai ziyara makarantu muna shiga aji muna duba yara.
Kun san makarantunmu na sakandare al’amarin kullum dada tabarbarewa yake musamman yadda ake ta faduwar jarrabawar karshe. Don haka, mai girma Gwamna ya yi alkawarin kai ziyarar ba-zata a wasu daga makarantun domin gane wa idonsa matsalolin da suke ciki.
Duk inda muka je mukan shiga aji mu yi musu tambayoyi. Gwamna ne yake farawa, sai Kwamishinan Ilmi ya yi tasa tambayar sai Babban Darakta ya yi, sa’annan sai ni, sai wani Sufabeza. Yaron da aka samu da kwazo akan yi masa kyauta sannan ya gaisa hannu da hannu da Gwamna da mu masu rufa masa baya.
A lokacin wannan ziyarar ba-zata, mukan soma shiga babban aji, sai tsaka – tsaki, daga nan kuma sai karamin ajin farko. Tambayoyin da muke saukaka ne daga al’amuran yau da kullum da lissafi da Ingilishi da tarihi da addini. Ba mu taba samun ajin da yaro daya ya amsa fiye da rabin tambayoyin shi kadai ba sai a ziyararmu ta ranar karshe a wani ajin karshe. Ashe shi din ma huhun ma’ahu ne, ta gina ba ta shiga ba ne.
Bayan gaisuwar yara da gabatarwar shugaban makaranta, mai girma Gwamna ya yi bayanin zaburarwa da kuma kudurin gwamnatinsa na inganta ilmi. Daga nan aka bude filin tambayoyi ga yara.
Gwamna ya soma tambaya da Ingilishi, “wacce shekara aka haifi Mungo Park?” Aka yi tsit. Wannan tambayar ta gagari kundila a irin wannan ajin, domin duk makarantun da muka zaga babu inda aka amsa ta. Sufabeza ne ya soma yin ta, da Gwamna ya lura an kasa ba da amsar sai ya karbe yake maimaita ta a duk inda muka je. Ba mu yi tsammanin za a samu mai amsawa ba, aka yi shiru cikin ajin. Can wani yaro da ke kuryar baya ya daga hannu, aka ba shi dama, ya ce “an haifi Mungo Park ranar sha daya ga Satumba a shekarar 1771.” Gwamna ya gyada kai cikin gamsuwa da jin dadin amsar.
“Ku tafa masa!” Gwamna ya ba da umurni.”A sake tafa masa!” Aka sake sakin wani tafin. Nan take Gwamna ya matsa kusa da yaron suka gaisa ga kyamarori na dauka.
Kwamishina ya yi tasa tambayar a kan abin da ya shafi addini, bayan jele-jele yaron nan ya yi mata kwaf daya. Daga nan Babban Darakta ya watso tasa tambayar aka amsa. Sai kuma tawa tambayar wadda na yi a kan lissafi. Da dama sun daga hannu an ba su dama. To amma amsar ba ta gamsar ba. Wannan yaron ya sunkuyar da kansa, muka kaddara cewa lissafi yake da abin rubutu.
Tambayar cewa take yi a takaice, alewa ce aka kawo guda ashirin da daya, ake so a raba wa mutum uku, amma rabon na farko ya ribanya rabo na biyu, haka nan rabo na biyu ya ribanya rabo na uku. Nawa nawa kenan rabon zai tashi? Tambaya ce mai sauki domin duk abin da ka dauka lambar farko sai ka ribanya ta sau biyu, ta biyun ma ka sake ribanya ta.
Can yaron nan ya daga hannu aka ba shi dama. Ya mike, a wannan lokaci duk hankali ya koma kansa, hatta ‘yan jarida ma sun juya na’urorinsu kansa.”Amsar ita ce, na farko zai samu uku, na biyu zai samu shida na uku kuma zai samu goma sha biyu.”
“Ku tafa masa!” Na fada cike da jin dadi. Bayan an gama tafi na dubi yaron na ce, “dana yaya sunanka?” Ya amsa “sunana Amir Shehu Isa.”
“Da kyau,” na fada fuskata cike da annashuwa. “Malam Amir, fito ka nuna wa yara ‘yan uwanka yadda ka samo amsar nan.” Duk tambayar da ta shafi lissafi mukan yi haka a makarantun da muka zagaya. Ya yi dan jim, sannan ya fito ya dauki alli ya tsaya gaban allo. Kimanin minti biyu an yi shiru an zuba masa ido, ga ‘yan baka sun sa masa na mujiya ta hanyar na’urorinsu.
Can an yi tsit sai wayarsa ta shiga kara, kida na fitowa daga ciki. Wannan ya keta doka, karamin dan ajin farko na sakandare bai kyautu ya rike waya ba, balle ya bar ta a kunne lokacin karatu, ballantana irin wannan lokacin da manyan mutane ke wajen.
Mun lura hannun Amir rawa yake yi cikin yanayin rudewa. Sufabeza ya cusa hannunsa cikin aljihun yaron ya fito da wayar tana ta fitar da kidan zamani. Ya kashe, ya rike a hannunsa.
Yaron na tsaye ya kasa zana komai, wayar ta sake rudewa da kida. Wannan karon sai da Gwamna ya nuna damuwa a fuskarsa, duk da haka ya yi wa Sufabeza alamar ya amsa a ji dalilin kiran. Ko a yi wa mai kiran tsawa. Sufabeza ya kunna da babbar lasifika. Tun kafin ya yi magana aka soma magana daga wancan bangaren. “Kar ka manta fa, amsar na daya uku na biyu shida, na uku sha biyu, ka ji ko?”
“Wa yake magana?” Cikin hanzari yaron ya juyo a firgice duk ya hada gumi. Ya shiga kyarma yana cewa, “wal…wal…wallahi ba amsa yake ba ni ba.” Ajin ya yi gurnani gaba daya. Idan babu rami me ya kawo maganar rami? Mara gaskiya ko cikin ruwa jibi yake. Ashe wayarsa yake bugawa wani yake ba shi amsar tambayar da muka yi musu tun dazu.
Yanzu wannan ba alama ce ta rashin amfanin waya ba? Kun ji satar amsa ta musamman wadda a baya mu ba mu taba jin irinta ba!
– Daga Littafin ‘Yan Yau
Kammalawa
Mun godewa Allah Maɗaukakin Sarki da ya kawo mu karshen wannan bita. Da fatan an samu wani abu da aka amfana da shi wajen inganta rubutu musamman gajeren labari.
Ina fata a samu wani daga mahalarta bitar nan ya samu nasara a gasar da BBC ko Aminiya suke gudanarwa a halin yanzu.
Ina godiya ga mahukuntan wannan kamfani na Bakandamiya bisa kokarinsu na hidumtawa harshen Hausa. Babu shakka wannan namijin kokari abin yabawa ne. Da fatan Allah ya taimake su bisa niyyar su ta alheri.
Ina godiya ga jagoran wannan Zaure na Marubuta da ya nemi na zo na bada tawa gudunmawar.
Allah ya taimake mu baki daya.
Da fatan za a cigaba da himma wajen tsara labarai masu armashi tare da lura da sharudda da matakan da ya kamata.
Wadanda suka halarci wannan bita, hukumar Bakandamiya za ta basu satifiket, zan tattara sunayen duka na danka musu.
Idan akwai mai neman karin bayani ko tambaya ko wani abu, yana iya tuntuba ta. Zan ci gaba da lekowa gidan nan akai akai
Na gode
Wassalam
Danladi Z. Haruna