Skip to content

Burina shi ne na zama babbar marubuciya da duniya za ta yi alfahari da irin rubutunta – Rukayya Ibrahim Lawal

A ci gaba da tattaunawa da Bakandamiya ta ke yi da fitattun marubuta na wannan zamani, a wannan karon mun samu tattaunawa kai tsaye da gwarzuwar marubuciya Ruƙayya Ibrahim Lawal. Marubuciyar ta bayyana irin gwagwarmayar da ta sha game da harkar rubutu da ma sauran abubuwa masu muhimmanci da suka shafi rayuwarta.

Ga dai yadda hirar ta kasance:

Tambaya: Malama Ruƙayya, za mu so mu ji tarihin rayuwarki a taƙaice, in ba za ki damu ba.

Amsa: Da farko dai sunana Ruƙayya Ibrahim Lawal, wacce a duniyar marubuta aka fi sani da Ummu Inteesar. An haife ni a shekarar 1997, na yi Primary School ɗina a Family Support Model Primary School Sokoto, daga 2003 zuwa 2009, daga nan na shiga Nana Girl Secondary School Sokoto na yi JSS ɗina inda na fice daga makarantar zuwa Abdul Rashid Adisa Raji Speacial School, a can na yi candy na a shekarar 2015. A lokacin ban samu damar komawa makaranta ba sai a 2017, inda na shiga Ummaru Ali Shinkafi Polytechnic Sokoto, ban shekara ba na fice saboda wasu dalili. Nan ma ban kuma shiga wata makarantar ba sai a shekarar 2019 na shiga Shehu Shagari College of Education Sokoto, inda na karanta ECCE (wato Early Childhood Care and Education) yanzu haka na kammala har na karɓi sakamakona.

Haka ma na yi karatun addini a Islamiyyar Sahabi Abubakar Siddik da ke cikin garin Sokoto. A can na yi saukar Alƙur’ani ta farko a shekarar 2012, na sake yin sauka ta biyu a Islamiyyar dare mai suna Tahafizul Ƙur’an Wattarbiyatul Islamiyya a 2013. Bayan sauka na karanta littattafai da dama na addini, wanda kuma har yanzu ana kan neman ilimi. Wannan shi ne taƙaitaccen tarihina.

Tambaya: Ma Sha Allah! To, a wacce shekara ki ka fara rubutu? Kuma me ya ja hankalinki har ki ka fara rubutun?

Amsa: Gaskiya abin da ya ja ra’ayina shi ne yadda matsaloli suke faruwa a society namu, a lokacin baya akwai wani abun da ke faruwa wanda yake ci mini tuwo a ƙwarya, na rasa hanyar magance shi, sai na nemi wata marubuciya na ba ta labarin domin ta rubuta shi tare da kawo mafita, ta yi iya bakin ƙoƙarinta amma saƙon bai isa yadda nake so ba, ganin hakan ya sa na fara tunanin me zai hana ni na rubuta, tunda a baya ina da ra’ayi a kan rubuce-rubucen.

Dangane da fara rubutu kuma, na fara sakin littafina ne a November 2019, Soyayyar Meerah shi ne na farko da na fara saki, duk da ba shi ne littafin farko da na rubuta ba. Sai dai sauran suna rubuce ne a exercise book ɗina.

Tambaya: Zuwa yanzun littattafai nawa ki ka rubuta? Za mu so mu ji sunayensu da kuma bakandamiyarki daga cikinsu.

Amsa: Littafaina da suka watsu a media yanzu guda tara ne, ban da wasu gajerun labarai, sai wani na haɗaka da muka fara ni da wata ƙawata.

Sunayen labaran gasu kamar haka;

  1. Soyayyar Meerah
  2. ‘Yar Gantali
  3. Rikicin Masoya
  4. A Sanadin Kama
  5. Halittar Allah Ce
  6. Wata Unguwa
  7. Gidan Duhu
  8. Sharri Kare Ne

Sai wanda zai fita nan ba da jimawa ba in Sha Allah.

‘Yar Gantali shi ne bakandamiyata domin shi ya kawo ni duniyar rubutu.

Hira da Rukayya Ibrahim Lawal
Ruƙayya Ibrahim Lawal kenan yayin da take karɓar shaidar girmamawa daga hannun Mai Girma Gwamna Dikko Raɗɗa na Jihar Katsina a wurin bikin Gasar Ɗangiwa Literary da aka gudanar a 2022

Tambaya: Shin kina da Maigida ko Uwargida a harkar rubutu?

Amsa: Idan har ubangida shi ne wanda ya koya wa mutum rubutu to ni kam gaskiya ba ni da shi, sai dai daga baya na samu masu duba mini rubutuna bayan na kammala, waɗannan mutanen kuwa su ne:
Yaya Ibrahim Muhammad Indabawa da kuma Yaya Yusuf Gumel, Jibrin Adamu Jibrin Rano, da Muttaƙa A Hassan.

Tambaya: Wanne littafi ne ki ka taɓa karantawa da ya fi burge ki?

Amsa: littafin gwanina Abubakar Auyo mai suna Jarrabi.

Tambaya: Shin kin taɓa shiga wata gasa, idan eh ne amsar, shin ko kin taɓa yin nasara? Sannan wasu irin nasarori ki ka samu a rayuwa game da harkar rubutu?

Amsa: Ina shiga gasanni sosai. Alhamdulillahi! Nasarori an samu ana kuma kan samu. A shekarar 2020 na ci wata gasa da wata ƙungiyar marubuta ta saka, na yi ta 3. Sai a 2021 kuma na samu Satifket na shiga zagayen biyun ƙarshe a gasar Majalisar Marubuta, a wannan shekarar labarina ya fito a cikin 25 mafiya zarra a gasar BBC. A 2022 kuma na samu satifket na girmamawa a gasar Aliyu Muhammad Research Library Gusau Institute, da kuma a gasar Ɗan Giwa Literary. A wannan shekarar kuma labarina ya fito a cikin uku da za a karrama a gasar Gusau Institute da za a gudanar a watan Disamba In Sha Allah.

Tambaya: Ma Sha Allah. To, idan za ki yi rubutu, shin ki kan tsara komai da komai ne kafin ki fara ko kuwa kai tsaye ki ke farawa?

Amsa: Wasu lokutan ina fitar da sekelaton na labari, na kan yi blocking kuma nakan fitar da profile character, wasu lokutan kuma kai tsaye na ke fara labari idan komai na labarin yana kaina. A taƙaice dai ba yadda ba na yi, don har a tsakiya na kan faro labari kafin in yi farko da ƙarshe.

Tambaya: Ya ki ke yi idan wani tunani sabo ya zo miki game da wani rubutu na daban alhalin kina tsakiyar rubuta wani. Ki kan saki wancan ne ki yi wannan sabon ko kuma sai kin gama da wanda ki ka fara?

Amsa: Na kan samu littafi na rubuta sabuwar idea ne, kuma na kan iya haɗa rubutun labari biyu a lokaci ɗaya musamman a lokutan baya.

Tambaya: Ki kan ɗauki kamar tsawon wane lokaci kina bincike kafin ki fara rubutu, kuma daga nan yakan ɗauke ki tsawon wani lokaci kafin ki kammala rubutun littafin?

Amsa: Bincike shi ne abu mafi cinye mini lokaci a rubutu, na kan yi jira iya jira har zuwa lokacin da binciken nawa zai kammala, wala’alla na fara labarin ko ban fara ba ba na ciyarwar sai na tabbatar da komai ya yi mini yadda nake so. Na kan ɗauki Wata ɗaya har zuwa biyu ma, wani har shekara ya danganta da yadda idea na labarin ke zuwa mini.

Tambaya: Wacce hanya ki ke bi wajen samun jigon labarinki?

Amsa: Ina samun jigona ne daga tunani, wani lokacin kuma idan ana hira na ji wani abin da ya kamata na rubuta sai na ɗauke shi a matsayin jigo, wasu lokutan na kan samu jigo a cikin bacci, ko kallon hoton wani abu, ko yayin da nake tafiya a hanya. Hanyoyin dai da yawa.

Tambaya: Wacce hanya ki ke bi wajen fitar da halayen taurarinki tare da ba su sunan da ya dace da su?

Amsa: Kamar yadda na faɗa maka nakan fitar da profile character kafin na fara rubutu. Sannan kowane tauraro a labari sunansa da ɗabi’arsa da shekarunsa suna a rubuce, ka ga ba zancen mantawa kenan.

Tambaya: Shin ko kin taɓa amfani da wani ɓangare na tarihin rayuwarki a cikin rubutunki?

Amsa: Tabbas na taɓa yin wannan.

Tambaya: Wanne littafi ne ya fi ba ki wahala lokacin rubuta shi?

Amsa: Wata Duniya shi na fi shan wahalar rubutawa saboda na ɗauko wani jigo na musamman da ba na jin an taɓa yin rubutun Hausa novel a kai. Ga kuma zurfaffen bincike, don kusan kowacce gaba ta labarin bincike ne ya gina ta.
Littafin da ya fi mini sauƙin rubutawa shi ne Rashin Gata, domin shi gajeren labari ne da na rubuta a zama ɗaya.

Tambaya: Wanne irin ƙalubale ki ka fuskanta a harkar rubutu, kuma ta wacce hanya ki ka bi har ki ka tsallake ƙalubalen?

Amsa: To dama a rayuwa ba za a rasa ƙalubale ba, in ko da akwai ƙalubalen da na fuskanta bai wuce yadda wasu ‘yan’uwa da kuma abokan mu’amala suke sukar harkar rubutun da nake yi ba.

Tambaya: A duk cikin taurarin labaran da ki ka rubuta wanne ki ka fi so, kuma me ya sa?

Amsa: Duka taurarin labaraina masu halayen kirki ina son su, amma na fi son yaro Abdurrazaƙ (jarumin cikin Halittar Allah Ce) yadda ya sha wahala da kuma jajircewar da ya yi a baya su ne suka saka nake tausayi da ƙaunarsa.

Hira da Rukayya Ibrahim Lawal
Ruƙayya Ibrahim Lawal

Tambaya: Akan samu wani lokaci da kan marubuci ke cushewa har ya kasa rubuta komai. Shin kin taɓa shiga irin wannan yanayin? Kuma ta wace hanya ki ka bi wurin magance hakan?

Amsa: Na sha shiga irin wannan yanayin ma. Ina magance hakan ta hanyar karance-karance da kallace-kallace ko kuma na ɗauki tsawon lokaci ina bacci, to daga na tashi sai ka ga abin ya kau.

Tambaya: Mene ne abin da ki ka fi so game da rubutu?

Amsa: In ga labarina ya samu karɓuwa.

Tambaya: Me ki kan yi a duk lokacin da ki ke da sarari?

Amsa: Rubutun dai ne.

Tambaya: Wace karin magana ki ka fi so? Kuma me ya sa?

Amsa: Zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana muzuru ana shaho sai ya yi. Saboda hakan na da tasiri a rayuwata.

Tambaya: A naki ra’ayin, tsakanin rubutun online da bugun littafi na hannu wanne ya fi? Kuma me ya sa?

Amsa: Kowanne daga cikinsu yana da fa’idarsa, sai dai wallafawar ta fi saboda ko yaya ne ba za ka nemi labarin ka rasa ba matuƙar da kwafe a hannunka saɓanin na online da watarana a matsayinka na marubucinsa ka kan iya rasa shi gaba-ɗaya.

Tambaya: Wanne tasiri marubuta suke da shi a cikin al’umma?

Amsa: A gaskiya marubuta mutane ne masu matuƙar tasiri a cikin al’umma, domin kuwa suna aike wa mutane saƙonsu da gyararraki ta hanyar yin amfani da kaifin basirarsu suke warware matsalolin da ke addabar wasu mutanen. Don haka marubuta suna da matuƙar tasiri. Tabbas saƙon da suke aikawa yana isa cikin gaggawa kuwa, domin da yawan mutane sun gyara rayuwarsu a dalilin wasu rubutuka da suka karanta.
Ni kaina akwai waɗanda suka faɗa mini sun ɗauki darussa da dama a dalilin rubutuna, kai zan iya cewa wannan abun ma ya zama gama-gari yanzu, don ga shi nan muna gani, ko a haka na bar ka nasan kin fahimci saƙon ya fita.

Tambaya: Shin ko akwai wani labarin da ki ke rubutawa a yanzu haka da masoyanki za su yi tsumayin fitowarsa?

Amsa: Akwai guda biyu.

Tambaya: Wane ne tauraronki a cikin marubuta?

Amsa: Taurarona a maza shi ne Abdul’aziz Sani Madakin Gini, a mata kuwa akwai Halima K. Mashi, Jamila Umar Tanko, Abubakar Auyo. Idan kuma aka dawo online akwai A’isha Ali Garkuwa, Jibrin Adamu Jibrin Rano, Balkisu Garkuwa. waɗannan su ne madubina a rubutu.

Tambaya: Wacce shawara za ki bawa ‘yan’uwanki marubuta?

Amsa: Shawarar da zan ba su ita ce, su tsarkake alƙalummansu sannan su yi rubutu mai ma’ana da fa’ida, wanda ko bayan ransu mutane za su yi alfahari da su. Kuma su dinga lalubo muhimman jigo na abubuwan da suke addabar al’umma a wannan zamani, kuma su guji wulaƙanci domin wulaƙanta ɗan’dam ba shi da amfani, ba wai don kana ganin ka zama wani a yanzu ba sai ka tsiri wulaƙanci, wannan abu ne da zai iya rusa ɗaukakar da ka samu.

Tambaya: Mene ne burinki a harkar rubutu?

Amsa: To, burina shi ne na zama babbar marubuciya wacce duniya za ta yi alfahari da irin rubutukana, kuma rubutuna ya tasirantu a zuciyar mutane ta yadda za su gyara tasu rayuwar.

Tambaya: Tsakanin Fim da littafi wannene ya fi saurin isar da saƙo?

Amsa: Fim ya fi saurin isar da saƙo. Abin da ya sa shi ne, ina ganin cewa kamar a fim ɗin saƙunan da nake son turawa za su fi saurin isa tare da tasirantuwa a zuciyar masu kallo.

Tambaya: Wacce shawara za ki iya ba wa sabuwar marubuciya?

Amsa: Shawarata a gare ta ita ce, ta nutsu ta mayar da hankali sosai wurin samo jigo mai kyau da ma’ana domin shi rubutu abu ne da bai kamata a faɗa masa haka kawai ba ba tare da sanin yadda yake ba. Ta kuma shiga bincike da nazari akan harshen Hausa da ƙa’idojin rubutu domin ta samar da labari mai ma’ana da daɗin karatu, sannan ta yi bincike a kan zahiriyar rayuwa. Matuƙar ta yi hakan to rubutunta zai samu karɓuwa nan da nan.

Tambaya: Wacce shawara za ki ba wa marubuta masu ɗauko labari su kasa ƙarasawa?

Amsa: Shawarata a gare su shi ne, su fara tsara komai kafin fara rubutu, yawanci rashin tsarawar ke saka labari ya ficewa mutum a rai. Sannan zan ba mu shawara, Mu sa juriya mu cire tsoro ko fargaba, mu nace tare da jajircewa kuma mu kaifafa tunaninmu tare da yin bincike a kan abin da za mu yi rubutu a kai.

Tambaya: Daga ƙarshe, me za ki iya cewa game da Bakandamiya Hikaya?

Amsa: Abin da zan iya cewa game da bakandamiya hikaya, shafi ne mai kyau don adana littafai da karanta su, kuma yana da kyau marubuta suna amfani da shi don ɓoye labaransu gudun rasawa.

An yi hira da Ruƙayya Ibrahim Lawal ne a ranar Talata, 08 ga watan Satumba 2020; 9am – 6pm kai tsaye a taskar Bakandamiya. An kuma tace tare da sabunta hirar a ranar 12 ga watan Satumba 2023.

Tsara tambayoyi da gabatarwa: Maryam Haruna tare da Hauwa’u Muhammad

Tacewa da sabuntawa: Jamilu Abdulrahman (Haiman Raees)
12-09-2023

3 thoughts on “Burina shi ne na zama babbar marubuciya da duniya za ta yi alfahari da irin rubutunta – Rukayya Ibrahim Lawal”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page