A makalar da ta gabata na dabarun rubutun labari, mun duba musamman ma’anar jigo da yadda ake samar da jigo. A yau za mu duba yadda ake girka jigo ya koma labari.
Da yake mun yi maganar girki, yana da kyau mu yi misali da wani nau’in abincin na Bahaushe da yadda ake girka shi, saboda samun ƙarfin fahimtar yadda za a girka jigo.
(a) Sanwar jigo
Bari mu ɗauki miyar kuka, idan za ka kaɗa kuka ba iyaka garin kukar kake buƙata ba, bayan garin kukar kana buƙatar sauran kayan masarufi da za su tallafi ita kukar idan an kaɗa ta ba da ma’ana. Misali kamar mu ce gishiri, magi, yaji da su mai da sauransu.
To haka shi ma jigo yake, ya ƙunshi fuskoki guda biyu waɗanda da su ake fara ɗora sanwa, akwai:
- Babban Jigo
- Ƙaramin Jigo
Kamar yadda garin kuka ko garin kuɓewar da aka kaɗa a miya ya fi komai rinjaye, shi ma babban jigo shi ne muhimmin darasin da labarin yake koyarwa, wanda ana kallon labarin za a iya cewa shi ne darasin da aka koya ko kuma ake so a gujewa koya. Misalin hakan a cikin labarai shi ne kamar jigon “karuwanci” a cikin labarin ‘Yartsana na Ibrahim Sheme, “jarumta” a cikin labarin Ilya Ɗan Mai Ƙarfi na Ahmadu Ingawa, da sauran su.
Su kuma ƙananan jigon su ne kamar kayan masarufin da ake haɗawa da su wajen ƙara daɗin labarin, sau tari kuma labari ba ya taɓa girkuwa ya yi ɗanɗano idan babu su a ciki.
Misali: Idan marubuci ya ɗauki jigon “sata” a matsayin babban jigon labari, to akwai buƙatar ya ƙara wasu ƙananan jigon kamar,
- Son zuciya: Ya nuna cewa son zuciyar ɓarawon cikin labarin ne ya kai shi ga aikata satar.
- Talauci: Ko kuma ya nuna talauci da halin matsin rayuwa ne ya ci ƙarfin ɓarawon har ta kai shi ga satar, da sauran su.
Ana ɗora babban jigon labari ne kai tsaye a kan gudanarwar babban tauraro, idan jigon na karuwanci ne, to ya zamana babbar tauraruwar labarin ce karuwar. Kamar Zainab (Asabe) a labarin littafin ‘Yar Tsana. Su kuma ƙananun jigo yawanci ana ɗora su ne a kan ƙananun taurari.
(b) Samar da kamshi yayin dahuwar jigo
Bayan an ɗora sanwar abinci, abu na gaba da ake saka ran ji shi ne tashin ƙamshin abincin, yanayin yadda abinci yake ƙamshi idan ana girkawa yanayin yadda zai jawo hankalin duk wanda ya shaƙi ƙamshin ya ji yana kwaɗayin ɗanɗanawa. To game da girkin jigo ma akwai yadda ake yi wajen samar da wannan ƙamshi, a sanya wa manazarcinsa kwaɗayin ya karanta labarin, wanda kuma ana yi ne ta hanyoyi guda biyu:
- Bayanin Jigo
- Warwarar Jigo
Bayanin jigo
Idan aka ce bayanin jigo wata gaɓa ce da marubuci zai yi amfani da ita wajen yi wa mai karatu bushara ko nune a kan jigon da zai gina rubutun labarin nasa, a wasu lokutan ma marubuci kan yi dangwalili ma’ana ya lasa wa makaranci zaƙin zumar jigon da zai saƙa labarin nasa a kai, amma a dunƙule kuma a taƙaice ta yadda shi makarancin labarin ba zai iya gane abin da labarin ya ƙunsa ba gabaɗaya, amma kuma zai matsu sosai ya ji yadda za a warware masa cikumurɗar.
Domin fahimta sosai zan ba mu wani misali a cikin ‘yan taƙaitattun kalmomi, da wani labarina mai suna: Na Ji Na Gani.
Na Ji Na Gani
Tun bayan rasuwar Khadija rayuwa Salim ta sauya, bargon farinciki, walwala da jindaɗin da ta lulluɓa masa ya yaye na damuwa da ƙuncin rayuwa ya maye gurbinsa. Lokaci guda zuciyarsa ta cika da tsananin ƙiyayyar kusantar dukkan wata ‘ya mace, duniyar tunaninsa ta ta’azzara har ta kai ga ya samu babban tasgaro wajen gudanar da al’amuran rayuwar tasa.
Khadija ita ce mace ta farko da ta fara farautar zuciyarsa a lokacin da bai shirya wa hakan ba, ta nuna masa ƙololuwar ƙauna irin wacce uwa take nuna wa ɗanta. A kowanne lokaci burinta ta gan shi cikin walwala da farinciki wanda hakan shi ya haifar ta dasa masa soyayyar ta a lambun zuciyarsa, har ma soyayyar ta yi yaɗo ta karaɗe ko ina a cikin lambun. Saboda tsabar shaƙuwar da ya yi da Khadija idan har ya wuni bai sanya ta cikin Idanuwansa ba babu makawa da zazzabi zai kwana cikin daren wannan rana.
Kamar faɗuwar rana haka a wani yammaci Khadija ta faɗi, sai dai saɓanin rana da idan ta faɗi yau za ta sake fitowa gobe, ita Khadija tun ranar da ta faɗi bata sake bayyanar masa ba. Ana cewa soyayyar farko kamar tabon halitta ne wanda ba ya fita, wataƙila shi ya sa Salim ya kasa mantawa da Khadija, har ma yake ji a ransa kamar ba zai taɓa ƙara son wata ‘ya mace ba a duniyarsa ballantana har ya yi aure kafin ya koma ga Allah.
Kwatsam kuma sai ga wata matashiyar budurwa Fatima wacce ta lashi kaifin takobin ceto rayuwarsa daga cikin tafkin kaɗaici da ya afka a dalilin rabuwar soyayya, tuni ta yi alƙawarin yin dashen soyayya a cikin ƙonanniyar ƙasar farfajiyar lambun makauniyar zuciyarsa wacce babu ko alamar danshi balle ruwan da tsiro zai yi sabon tofo….
Idan mun yi nazarin wannan rubutu da kyau, za mu ga a cikin rubutu ƙalilan an yi bayanin jigon labarin wato (yaƙin soyayyar da sabuwar budurwar za ta yi da makantacciyar zuciyar Salim irin ta waɗanda wani abu mara daɗi yake sakawa su ci alwashi).
Jodie Archer da Matthew L. Jockers sun ce jumlolin da fitattu kuma shahararrun marubuta irin su Sylvia Day, da Toni Morrison, da Jeffrey Eugenides da Virginia Woolf kan yi amafani da su wurin buɗe labaransu (mabuɗin labari), sukan dunkule rikicin da ke cikin littafi mai shafuka 300 a cikin jumla guda mai kalmomi 20 ko ma ƙasa da haka. Kenan dai suna amfani da hikima su bayyana jigon su a ciki taƙaitattun kalmomi don kama zuciyar mai karatu, ya ji yana so ya karanta labarin irin yadda mai jin yunwa zai matsu ya kai abinci mai ƙamshi zuwa bakinsa. Bayan wannan kuma sai,
Warwarar jigo
Shi kuma warwarar jigo ya ƙunshi yadda za a bi a warware saƙon da ke cikin bayanin jigo a fili kowa ya fahimce shi. Ko kuma ana iya cewa warwarar jigo shi ne bayani daki-daki da ake yi a cikin labari don saƙon ya fito fili, masu karatu su fahimce shi. In aka ce saƙo a nan ana nufin jigo.
Idan muka yi amfani da misalin labarin Na Ji Na Gani da muka kawo, a warwarar jigo ne marubucin zai riƙa warware zaren labarin daki-daki. Tun daga kan ta yadda Fatima za ta tunkari Salim da batun soyayya, shin za ta faɗa masa baki da baki ne? Ko kuwa ƙawarta ko wani za ta yi amfani da shi wajen sanar masa? Idan ta sanar masa wani ƙalubale za ta fuskanta? Ta yaya za ta magance ƙalubalen?
A haka za a yi ta warware labarin gaɓa bayan gaɓa har zuwa lokacin da za a dangana da ƙarshen labarin, inda za a nuna nasarar jawo hankalin Salim da Fatima zata yi bayan tarin gwagwarmaya da ƙalubale.
Ku karanta makala ta gaba da ta yi nazarin murhun girka jigo.
Kamar kullum, ƙofar gyara, sharhi, ƙarin haske ko tambaya a buɗe take.