Assalamu alaikum masu bibiyarmu a wannan fili mai albarka na tattaunawa da marubuta, muna yi muku barka da sake kasancewa da mu. Kamar yadda muka saba, a wannan karon mun ɗauko muku fasihiyar marubuciyar nan ta Fikra Writers’ Association, wato Rufaida Umar. Ku kasance da mu don jin yadda tattaunawar ta kasance.
Tambaya: Muna son jin takaitaccen tarihin rayuwar baƙuwarmu.
Amsa: Assalamu alaikum warahmatullah wabarakatuhu. Sunana Rufaida Umar Ibrahim. Bayan haka, cikakken sunana da na faɗi a sama, ni haifaffiyar garin Kano ce. Ina da aure kuma ina da yarana biyu. Ina zaune a Kano yanzu haka. Na yi karatu daga Nursery har Secondary a makarantar Yandutse College a nan cikin Kano. Na yi karatun NCE inda na karanci Bio/Isc a F.C.E Kano.

Tambaya: Me ya ja hankalinki har ki ka fara rubutun?
Amsa: Gaskiya yawan karance-karance ne ya soma sanya min son yin rubutu.
Tambaya: Zuwa yanzun littattafai nawa ki ka rubuta? Kuma za mu so mu ji sunayensu.
Amsa: Ba zan iya cewa ga adadin rubutuna ba. Wasu gajeru ne, wasu masu tsawo.
- Mahaifiya
- Bazan Barki Ba
- Mata Iyayenmu
- Rayuwar Hamida
- Ƙazamar Gida
- Mijin Mace Daya
- Daraja Daya
- Ɗan Adam
- ‘Yar Bariki
- Amadu
- Taurari
- Rayuwa Ce
- Ruɗin Shaiɗan
- Firgici
- Ƙarfen Ƙafa
- Dukan Ruwa
- Fitar Tsiro
- Rumfar Kara
- Muƙaddari
Tambaya: Wanne littafi ki ka fi so a duk cikin litattafan da ki ka rubuta, kuma me ya sa?
Amsa: Ɗan Adam, saboda labari ne da ya fiddo da halayya daban- daban na rayuwar ɗan’adam.
Tambaya: Wanne littafi ne ki ka taɓa karantawa da ya fi burge ki?
Amsa: Tuna Baya, na Sumayya Abdulkadir Takori.
Tambaya: Idan za ki yi rubutu, shin ki kan tsara komai da komai ne kafin ki fara ko kuwa kai tsaye ki ke farawa?
Amsa: A’a, bayan na san jigon da zan yi rubutu a kai, nakan fara rubutuna ne kawai. Ba na tsayawa tsarawa, koda na gwada yi, sai na ji ba zan iya ba.
Tambaya: Ya ki ke yi idan wani tunani sabo ya zo miki game da wani rubutu na daban alhalin kina tsakiyar rubuta wani. Ki kan saki wancan ne ki yi wannan sabon ko kuma sai kin gama da wanda ki ka fara?
Amsa: Gaskiya ba na saki, kuma nakan bar shi har sai na kammala wanda nake yi tukunna.
Tambaya: Ki kan ɗauki kamar tsawon wane lokaci kina bincike kafin ki fara rubutu, kuma daga nan yakan ɗauke ki tsawon wani lokaci kafin ki kammala rubutun littafin?
Amsa: To sanadin dai cigaba da aka samu na kafofin sadarwa, bincike yanzu bai fiye yin wahala ga marubuta ba. Mutum zai shiga Google, zai nemi sani daga mutane da dama, tattara bayanan ko da kana cikin rubutu ne ma kana iya yi. Kasancewar ina yin dogon rubutu, nakan ɗauki wata biyu ma ban kammala ba.
Tambaya: Wacce hanya ki ke bi wajen samun jigon labarinki?
Amsa: Babu wata hanya da nake bi, sai dai wani lokacin mutum kan ci karo da abu da ya faru zahiri a gabansa sai ya ji ya na ƙaunar ya faɗakar da al’umma a kai.
Tambaya: Wacce hanya ki ke bi wajen fitar da halayen taurarinki tare da ba su sunan da ya dace da su?
Amsa: Eh to, babu wata hanya doguwa da nake bi gaskiya da ya wuce tunani.
Tambaya: Shin ko kin taɓa amfani da wani ɓangare na tarihin rayuwarki a cikin rubutunki?
Amsa: A’a ban taɓa ba.
Tambaya: Wanne littafi ne ya fi ba ki wahala daga cikin dukkan litattafan da ki ka taɓa rubutawa?
Amsa: Ƙarfen Ƙafa.

Tambaya: Wanne irin ƙalubale kika fuskunta a harkar rubutu?
Amsa: Na fuskanci ƙalubale da dama, musamman masu ɗaukar labarina su sanya sunansu. Wasu har ba da iznina ba su ɗauka su sanya a YouTube channel ɗinsu. Hakanan da na soma labarin kudi, nan ma na fuskanci ƙalubale, sai ka tara waɗanda suka biya ka keɓance za ka turamusu, a samu wasu su bude group suna haɗa litattafan kuɗi wurin biyar ko sama da haka suna siyarwa a naira ɗari biyu kacal.
Tambaya: Marubuta da yawa sun fi karkatar da akalar jigon rubutunsu akan soyayya shin kema haka ne?
Amsa: Kamar sauran, ni ma rubuta na taɓa soyayya ba kaɗan ba, sai dai ban fiye maida ta irin ɗari bisa ɗari ita ce jigon labarina ba. Nakan taɓo matsaloli da dama na rayuwa wanda ya kyautu ace iyaye sun sanya ido ko kuma yara maza da mata sun kula da shi sun yi taka-tsan-tsan.
Tambaya: Shin kin taɓa shiga wata gasa, idan eh ne amsar, shin ko kin taɓa yin nasara? Sannan wasu irin nasarori ki ka samu a rayuwa game da harkar rubutu?
Amsa: Babbar nasarar da na samu a rubutu shi ne na hadu da mutane da dama masu kirki wadanda da yawa mun haɗu ido da ido mun sada zumunta. Hakanan na samu karramawa daga ƙungiyar HAF wanda ina alfahari da hakan duk sa’adda na kalli certificate ɗin. Kamar yadda na samu gayyata daga ANA a filin su na hira da marubuci.
Batun gasa kuwa, na shiga gasar BBC Hikayata a shekarar 2020 na zo ta uku, sai gasar Aminiya ita ma shekarar da na yi ta BBC, na zo ta ɗaya. Na shiga gasar Tsuburin Gobir wanda Alan Waƙa ya ɗauki nauyinta na zo ta uku. Na kuma shiga gasar ɗangiwa na Katsina, na zo ta biyu.
Tambaya: A duk cikin taurarin labaran da ki ka rubuta wanne ki ka fi so, kuma me ya sa?
Amsa: Na fi ƙaunar Ramlat, tauraruwar labarina ta Karfen Kafa, saboda ta ga rayuwa sosai. Na farko ta bijirewa iyaye saboda son zuciyarta, ta shiga hali na nadama da da na sani. Tabbas ta girbi abin da ta shuka sosai kafin daga baya ta samu sauyi a rayuwa.
Tambaya: Akan samu wani lokaci da kan marubuci ke cushewa har ya kasa rubuta komai. Shin kin taɓa shiga irin wannan yanayin? Kuma ta wace hanya ki ka bi wurin magance hakan?
Amsa: Eh na taɓa samun hakan ba ma sau ɗaya ko biyu ba, hanyar da nakan bi bai wuce haƙura da rubutun da ma tunanin a wannan lokacin ba, daga baya idan na dawo sai komai ya warware min.
Tambaya: Mene ne abin da ki ka fi so game da rubutu?
Amsa: Karin magana. Ina matuƙar son na ga rubutu mai cike da karin magana.
Tambaya: Me ki kan yi a duk lokacin da ki ke da sarari?
Amsa: Bakomai sai ko tunanin rayuwa sai kuma wasu lokutan sarrafa wayata.
Tambaya: Wace karin magana ki ka fi so? Kuma me ya sa?
Amsa: Dukan ruwa, ba zai hana gwarje amo ba. Ina son karin maganar saboda ya na nuni da cewa duk fa abin da zai je ya zo, ba zai hana abin da ƙaddara ta zo da shi faruwa ba.
Tambaya: Waɗannae irin shawarwari za ki bawa sabbin marubuta don ganin sun yi rubutun da zai karɓu a wajen jama’a duba da yadda makaranta suke rububin rubutunki?
Amsa: To rubutu dai baiwa ce. Amma ina shawartar duk wani marubuci ko marubuciya su dinga duba da abinda ke faruwa yau da kullum na rayuwa. Babu hanyar isar da saƙo da gaggawa kamar hanyar rubutu. Wani ƙarya da saka maƙudan kuɗaɗe ko soyayyar da hankali ba zai ɗauka ba, ba shi ne mafita ba. Mafita shi ne, mu yi duba da abinda ke faruwa a rayuwarmu, mu fuskanci wannan matsalolin. Mu yi aiki da baiwar da Allah Ya bamu mu isar da saƙon da ya kamata. Yin rubutu na batsa ko makamancinsa ba namu bane. Ba inda kuma zai kaimu. Allah Yasa mu dace.
Tambaya: Wadanne irin shawarwari za ki bawa marubuta masu kwaikwayon rubutun junansu, musamman wajen sunan littafi ko salon labarin duk ya zama iri ɗaya, abun ya zama kamar anko. Har makaranta suna korafi akan hakan.
Amsa: To wani abun za ki ga arashi ne kawai, abin nufi wacce ta yi rubutun ba lallai ta san ko da rubutun wata ba balle marubuciyar. Wata kuwa da saninta za ta kwafi wani ɓangare na rubutun wata don kawai ta samu mabiya da kuma yabo. Wasu ma su kwafe labarin Fim, musamman na Korea ko Hindi. A ganina wannan ci baya ne a harkar adabi. Ba abinda zai ƙara maki. Shawara kuma ya dace ace marubuta mu haɗa kanmu, ganina wannan shi zai kawo raguwar hakan. Sannan game da suna ya zo ɗaya kuwa, ni ban ɗaukeshi abin tada hankali ba, tunda sunan marubutan daban, ba lallai kuma marubuciya ta san da zaman ita waccan ɗin ba.
Tambaya: Wacce irin gudummawa rubutun littafi ya ke bayarwa a yanzu?
Amsa: Rubutun novel wanda ba batsa ba shiririta yana bada gudunmuwa sosai wajen gyara ga al’umma. Wata za ki ga ba ta san ta tarairayi miji ba, ba ta san abubuwa da dama na gyaran gida ko yaranta ba, sanadin abinda ta karanta sai ki ga ta gyara. Hakanan a ɓangaren shugabanci ko siyasa, ko ma makaranta, rubutu ba ƙaramin taimakawa yake ba ga matasa wajen ƙaruwa da ilimin abinda ya shafi zamantakewarmu na yau da kullum.
Tambaya: Wacce irin illa rubutun batsa ya ke haifarwa a cikin al’umma?
Amsa: Rubutun batsa babbar illah ce ga al’ummar mu duba da yadda kafofin sadarwa suka zama ruwan dare. Kowane yaro ko yarinya ta san ta ɗauki waya ta karanta. Idan har ba’a gyara ba yaranmu na cin karo da waɗannan shirmen, gaskiya nan gaba ba zai haifar da ɗa mai ido ba.
Tambaya: Waye ubangidanki a marubuta?
Amsa: Ni duk wanda zai min gyara a harkar rubutu, ina daukarsa uban gidana. Ban ware wani ko wata na keɓance na ce shi ne ko ita ce ba.
Tambaya: Wanne irin kira za ki yi wa ‘yan uwanki marubuta?
Amsa: Su kasance masu haƙuri da kuma sauƙin kai. Kar su zama masu girman kai. Domin idan har suka sanya girman kai abin tunƙahonsu, to za su rasa ilmuka da dama wurin manyanmu. Farko abinda ya kamata su saka a ransu shi ne, rubutunsu ba iyakar su zai tsaya ba, duk ranar da suka yi rubutu suka sake shi, zai iya kai wa inda ba su zata ba ko da babu ransu. Don haka mu san irin rubutun da ya dace mu yi. Mu kuma yi ƙoƙari wurin sanin ƙa’idojin rubutu ta hanyar koyo wurin masana.

Tambaya: Wacce irin rawa adabi ya ke takawa a cikin al’umma?
Amsa: Adabi na da matuƙar tasiri don kuwa ta hanyarsa cikin sauƙi mutum kan isar da dukkan saƙon da yake so. Ko da ba’a sanka ba, abinda ka rubuta ko ka faɗi zai kewaya har inda ba ka tsammata ba.
Tambaya: Me kika fahimta game da sayar da littafi a online shin wanne hange kika yo kan lamarin,ci gaba ne ko ci baya?
Amsa: Siyar da littafi online shi ma ci gaba ne. Hakan kuma ba yana nufin ya danne siyar da littafi offline ba. Sai dai siyarwa online yana da ƙalubale da yawa ba kamar waɗanda ke buga labaransu ba.
Tambaya: Shin kin taba cinkaro da masu satar fasaha, wanne mataki kuka taba dauka a kansu? Wadanne marubuta ne rubutunsu ya ke birge ki, kin taba kai musu ziyara?
Amsa: Eh mun taɓa cin karo da su, amma bamu taɓa ɗaukar matakin hukunci ba, sai dai mukan bi mutum mu yi mishi gargaɗi wanda ba lallai su ji ba. Hakanan mukan yi wasu dabaru kamar daina saka lamba (numbering) yanda mutum zai rikice idan ba wanda ke bibiyarmu ba, da ma dai sauransu.
Gaskiya akwai marubuta da dama da ke burge ni a fannin rubutu. Kamar su Takori, Halima K/Mashi, Anti Bilki, Zulfau Aliyu, Fauziyya D. Suleiman da dai sauransu. Ba wacce na taɓa kaiwa ziyara. Kuma zan so na kai.
Tambaya: Shin ko akwai wani labarin da ki ke rubutawa a yanzu haka da masoyanki za su yi tsumayin fitowarsa?
Amsa: Akwai labarin da na fara sai dai ban masa suna ba, in sha Allahu ina fatan kawo shi bayan sallah.
Tambaya: Mene ne burinki a harkar rubutu?
Amsa: Babban burina a rubutu bai wuce kafa tarihi mai kyau ba. Duk inda aka ambaci Rufaida Umar, makaranta su mata kyakkyawar shaidar ba ta rubutun batsa. Ina jin matuƙar daɗi na ji ana yaba min da sauran ‘yan’uwa irina waɗanda ba ma rubutu littafin da zamu ji kunyar wani babba ya karanta. Hakan ma babban nasara ce a rubutu. Fatan mu, Allah ya sa sanadin rubutunmu, mu sauya rayukan mata masu munanan tunani game da zamantakewarsu da iyalinsu da ma al’umma. Ba mata kaɗai ba, har da mazan in sha Allahu.
Tambaya: Me za ki iya cewa game da Hikaya?
Amsa: Hikaya babu abin da zan iya cewa game da ita sai fatan alkhairi, tabbas kuna iyakar ƙoƙarin ganin kun ɗaukaka rubutu da marubuta ta fuskoki daban-daban. Kuma sannu-sannu haƙarku zai cimma ruwa. Fatanmu wannan cigaba da ake ta samu, ya amfanar da ku da mu baki ɗaya. Marubuta muna godiya kwarai dagaske. Allah ya saka da khairan.
An yi wannan hira ne da Rufaida Umar ne a ranar Talata, 20 ga watan Oktoba 2020; 10am – 6pm kai tsaye a dandalin Bakandamiya (soshiyal midiya). An kuma sake sabunta hirar a ranar 24 ga watan Maris 2024.
Tsara tambayoyi da gabatarwa: Maryam Haruna tare da Hauwa’u Muhammad.
Tacewa da sabuntawa: Jamilu Abdulrahman (Haiman Raees)