Skip to content
Part 4 of 28 in the Series Canjin Bazata by Maryam Ibrahim Litee

Na fasa kuka. Ummu da ke zaune ta tasa cikinta gaba take tambayata, “Taa… aa rasu! Ummu mun rasa Amina, Amina ta rasu Ummu! Sai da nayi da na sanin gayawa Ummu dan halin da ta shiga ga tsohon ciki.”

Kwanakin da suka biyo baya sun zo mana a tsanance kwarai, koda yaushe za ka same mu shiru da Ummu da Salma, wani lokacin kuma mu yi ta kuka, Gamu mu kaɗai a gida, Sai da aka yi sati sannan mutanen gidan su ka dawo, ciki har da yayarmu.

Mutuwar ta taɓa kowa a gidan, dan lokaci zuwa lokaci za ta aiko mota cike da kayan abinci a raba duka gidan, hatta sutturu zata aiko ta ce a raba wa masu bukata, hadda kuɗi aba magidantan su yi cefane.

Wani zance mara daɗi ana zaman makokin aka sace kit ɗinta da take adana gwala_gwalanta. Sai na riƙa tuna zuwanta na ƙarshe inda ta ce ma innarmu “In sha Allahu innarmu in dai na rabu da cikin nan lafiya ya zama dole in sai da wasu gwala gwalaina, in zo in bada aikin gyaran gidan nan.”

Ban mantawa innarmu murmushi ta yi. Ta ce, “Ke ai da wuya kuɗinki su yi auki, kullun kuɗinki na cikin hidimta mana, ubangiji dai ya yi albarka ya raba ku da cikin nan lafiya, tare da kowace musulma me ɗauke da shi.”

Su innarmu basu dawo ba, babanshi ya roƙi su zauna har tayi arbain dan ƴan gaisuwar kullun ƙara zuwa suke, ga mijinta ya shiga ruɗani mai yawa, su biyar ne zaune can hada Haj ƙanwar kakarmu.

Ranar da tayi arba’in ƙannan babanmu maza suka yi mota guda suka nufi Abujan da niyyar su ƙara ma juna gaisuwa, sai su taho da su Innarmu haka kuwa aka yi. Washegari sai ga su sun dawo, kallo ɗaya za ka yi wa innarmu ba za ka so ƙarawa ba, yadda duk ta bi ta yamutse. Uwar ɗakanta kawai ta wuce ta hau gado, rufe ta muka yi muna ta kuka masu shigowa yi mata gaisuwa suka yi ta bamu haƙuri.

A ranar cikin dare ummu ta haihu cikin ƴar gajeruwar naƙuda ta samu santalelen yaro, Innarmu ta fita ta taso Haj kishiyarta da Baba Rakiya, dan da nan suka gyara me jego da ɗanta. ƙarfe biyu suka yi sallama kowace ta koma ɗakinta. Da safe Maijego kamar ba ita ta haihu ba, Allah kenan me yin yadda ya so. Ita Amina ko haihuwar ma bata kai ga yi ba, Allah ya amshi abinsa. Da safe mutane suna ta shigowa barka har dare, Uban ɗan ma a ranar ya iso daga katsina.

Cikin dare na farka na ji motsin innarmu da na saurara sai na ji sautin kukanta a hankali, da sauri na tashi na zauna kusa da ita, “Innarmu me ya same ki?” Shiru ta yi da farko sai da na maimaita na ce, “Innarmu ki yi haƙuri duk mai rai mamaci ne, Ina so akan wannan ma ki sa haƙuri”. Ta ja numfashi ta share hawayen da ke gudu kan kuncinta, Ba mutuwar uwata nake ma kuka ba, Ina kukan al’amura da dama, Muhimmi cikin su shi ne rasa mahaifinku da na yi a lokacin da na fi kowa bukatar shi, musamman kasantuwar ƴaƴana mata ne, Ina da buƙatar shi kusa da ni.” Na ce, Ki yi haƙuri innarmu Ke ɗin ma ai jaruma ce, da ki ka fi wasu mazan tsayuwa a kan Ƴaƴan su.” ta ce “Shuhaina ki yi haƙuri saboda ke na ke wannan kukan.” Na rufe baki “Na shiga uku! Innarmu me na yi maki?”

Ta ce, “Ki yi haƙuri, amma ba ki yi min komai ba, abinda nake so da ke, idan har ni ce mahaifiyar ki, Ina kuma da ƙima a wurinki, to ki yi haƙuri da abinda zan gaya maki, kuma ki rungumi ƙaddara.”

Na ce, “Na ji, In sha Allah kuma zan yi yadda ki ke so.” Duk da dai cikin ƙarfin hali nake, gabana faɗuwa ya ke, dan na san abinda zai sa ta kuka ba ƙaramin abu ba ne.

Ta ce, “A jiya da hantsi za mu taho an hallara a falon mahaifin Ahmad ana ƙarawa juna gaisuwa sai Babanku ya’u ya matsa kusa da shi ya ce, ‘A madadina da yan’uwana mun yanke shawarar ba Ahmad ƙanwar mariganyiyar, uwarsu ɗaya ubansu ɗaya, kuma watanni kaɗan suka rage ta kammala karatunta.’ Nan da nan Alhajin ya shiga godiya. Ya ce idan ba damuwa a faɗi sadakinta tunda akwai jama’a sai a ɗaura, Babanku ya faɗi sadaki dubu hamsin, nan take Alhajin ya biya, aka ce jama’a su shaida aka ɗaura maki aure da mijin ƴar’uwarki.”

Ya zuwa lokacin da ta kawo nan kuka nake iya ƙarfina, ina fyace hanci na buga kaina a bango ina cewa, “Yau na san ni marainiya ce, na rasa mahaifina, dan da shi ne nasan ba zai min haka ba, ya ba wanda bai ce yana so na ba.” Ihu na yi da ƙarfi ina, “Wayyo na bani ya ma za’a yi in auri mijin Amina?”

Ban ankara ba sai dai na ji Innarmu ta make baki na. “Yi mana shiru, ba ki da hankali? Ba ki san dare ba ne, ki tado mana jama’a? Ashe ke ba za ki yi haƙurin da kike cewa in yi ba? Ba sai mu bar wa Allah komai ba ya warware mana?”

Daga haka Alwala tayo ta haye sallayarta, “Ni kuma zama nayi na jingina da bango na haɗa kai da gwiwa, Kuka na ke wanda zuwa safiya fuskata ta kunbure, ko kokon da na dama ban sha ba, ban ma da niyyar zuwa makaranta. Baba ya’u ya yi sallama a ƙofar ɗakinmu, sai da ya zauna muka gaishe shi ya gaisa da Innarmu, ya ce “Fatima ba ki ce komai ba kan sadakin shuhaina.” Wani ɗan murmushin da bai kai zuci ba ta yi, “Ni kuma a taƙaice wace hujja gare ni ta cewa a bani sadakinta? ya ce” In na lura Fatima sai in ga kamar fushi ki ka yi.” Ta girgiza kai “Ko ɗaya, tunda an riga an ɗaura to me kuma za ka ce?

Ya ce, “Ato bare duk wanda rai ya yi wa daɗi baran me shi ne, Na ga wannan gata ke nayi mawa, don idan ta samo kan ta tuna da ni sai ta fara kawo maki, yanzu ba ga Zinatu ba wane faɗi tashi ne ban yi ba kafin yuwuwar auren ta? amma yanzu wa ta sani idan ba uwarta ba, har makka ta kai ta ni kuwa ko sansanin alhazan ban je ba.”

Innarmu ta tari numfashinsa, “Abinda nake so ka gane, kar mu sa wani hange cikin wannan aure, mu riƙe shi da zuciya ɗaya, Mu yi addu’ar Allah ya sanya masa albarka Amma wata niyya tamu ta daban ba wannan ba, za ta iya janyo mana matsalar da idan ta zo ba za tayi mana daɗi ba.”

Ya ce, “Haka ne” ya tashi ya fita Ummu ta dafe baki, “Yanzu fa shi kenan ya riƙe sadakin nan ba zai bayar ba? “Innarmu ta ce Uhum! kawai Baba sani ya shigo yana ta ba Innarmu haƙuri.

Ya ce “Shi tsoron da yake ji masu kudin nan ba’a yi masu irin wannan karan tsayen. ta ce “Ba komai Allah ya sa hakan ya zama alheri.” Ranar suna yaron Ummu ya ci suna Najib. Na ci gaba da zuwa makaranta ta. Satin Ummu uku da haihuwa Baba ya’u ya shigo gidan cikin sauri, ya ce a ba shi tabarmi ga uban Ahmad nan da mutane. Ya ɗan jima da zuwa aka kira Innarmu su gaisa, ya yi mata godiyar karamcin da aka yi masu.

Ya ce ya zo ne ya ƙara yin godiya, kuma a account ɗin Amina, an samu dubu ɗari biyar da ashirin, mijinta ya ce ya yafe sai suturunta duk an zo da su, Kuma shi ma Ahmad ɗin wai yana nan zuwa dan yanzu haka ba ya ƙasar, kan wani aiki da ya taso masa, kuma ya ce kar a sayi wani kayan ɗaki, dan ba zai iya zama gidan da ya zauna da Amina ba, ya koma cikin asibitin da yake aiki nan za’a kai ni. Ina jin muryar Baba ya’u ya na cewa,

“Ina Shuhainar ta gaida surukinta? Karkashin gado na shige. Ya shigo har ciki yana ce wa Ummu, “Ina shuhainar? Ta ce, “Ai ko ta fita.” Tsaki ya ja ya juya, Mahaifin Ahmad ya cika mutanen gidan da kudi sannan ya tafi. Zo ka ga fara’a wurin Baba ya’u, ya samu abun san shi. Har Ummu tayi arba’in ta koma, ba Ahmad ba labarinsa. Ga gulmar da ta fara yawo a cikin gidanmu, Wai ai dama kwaɗayi ne, In ba dan an ga kuɗi ba Ƴaƴa take da su, ballantana ace zata riƙonsu, Ko shi bai santa ba? ba za a jira ya ce yana san ta ba. A yanda ma ake bada labarin wai Innarmu ce ta roƙi ya aure ni, Wata aminiyar ta ta ƙut da ƙud Haj Baraka ta zo tana tambayar Innarmu gaskiyar maganar. Ta ce mutanen gidanmu ke zuwa gidansu da labarin idan an tabbatar da ba ta nan, Ita kuma idan ta dawo sai mutan gidan su su gaya mata.

Daga ni har Innarmu mun shiga halin takura a cikin gidan, Ina dai zuwa makaranta ne, amma gani nan ne har muka fara zana jarabawar (WAEC) ɗinmu, da ƙyar na sa ma zuciyata salama na fuskanci jarabawar.

Ranar da muka kammala paper karshe ina dawowa gida, Sujjada nayi ma ubangiji da na ɗago idona na malalar da hawaye, Innarmu wadda ke zaune tana yankan ɗinki ta dube ni, “Ki yi haƙuri Shuhaina kowane bawa da irin ƙaddarar shi a rayuwa, haka idan Allah ya shirya rubutaccen al’amari baya kankaruwa, an ɗauke alƙaluma kuma takardu sun bushe, Matar mutum kabarinsa.”

Daga haka ta ci gaba da yankanta. Wasa wasa sai da aka ƙara wata guda, Ranar na dawo islamiya da hantsi mota na gani galleliya tana ta sheƙin ɗauke ido, cikin hasken ranar da ya fara ɗagawa, Ƙwarai na yaba kyan motar a raina, Na wuce cikin gida, abinda na lura mutanen gidan sai kallona suke, ban damu ba, na wuce ɗakinmu, Innarmu na samu kan sallayarta, na san ita ɗin ma’abociyar sallar walha ce.

“Innarmu na dawo, Yusuf ɗin ya kawo cefanen kuwa? Ina son yi da wuri, gidan Ummu za ni in gano Najib.” Cikin sanyin murya ta ce, “Bar girkin nan Shuhaina, je ki yi wanka.” Na ce “Nayi kafin in tafi makaranta.”

Ba tare da ta dube ni ba ta ce, “Na ce ki je ki ƙara yi.” Ban saba musu da ita ba sai na wuce, Sai da na dawo wankan, ta ce in yi kwalliya me kyau, zama nayi nayi kwalliyar ta ce in ɗauko kayana sababbi in saka, Ba musu na yi yanda ta ce, Hijab ta umartan in saka.

Gwoggo Rakiya ta leƙo, “Yawwa ta kammala? Sai ta juya, tare suka dawo da hajiyar mustafa kishiyar innammu, Suka ce ma Innarmu, “Sai ki sa mata albarka dan suna jiranmu su yi mata faɗa.”

Ta ce, “Allah ya yi maki albarka, ya bada sa’a” ta sa kai ta shiga uwar ɗakanta, Sai sannan na fahimci abinda ke shirin faruwa da ni, Kawai sai na sa kuka. Za su kama ni mu fita na ce, “Zan ɗauki wayata” hada ƙaramin Al-ƙur’anina na na ɗauko, da hisnul muslim, ɗakin gwoggo ladi aka kai ni, Inda muka samu duka ƙannen babana sun hallara, faɗa suka yi min, da nasihar in bi aure. Baba ya’u ya ce, “Duk mun fita, bin mu aka yi, aka ce mu zo, Mijinki ya turo mota a tafi da ke.

A raina na ce, “Ka ji wai direba dan rashin galihu.” Da muka fito direba ya taso da sauri ya buɗe ƙofofin motar, Mu huɗu ne a baya, Baba Ramu a gaba, da yake ita tana da jiki, Ƙannen babana duk suna tsaye, Mutanen gidan ma duk sun leƙo suna ta ɗaga hannu, Wani ƙududu na ji ya taso ya tokare ni, ko ƴan’uwana ba a bari sun zo mun yi sallama ba. Dai dai da salma bata nan, Yusuf kuma cikin dare ya iso daga kano, inda yake karatu, bamu gan shi ba sai da safe, leƙowa kawai ya yi ya gaida Innarmu, ya ce Bari ya je yayo cefane ya dawo, ya ce min “Akwai labari Shuhaina, bari in dawo. Kafin ya dawo na tafi makaranta. Sai dai idan ya dawo ace mashi an tafi da ni. Kuma dangin uwata ko ɗaya basu tsaya an ɗauka ba, duk da yake sune dangin nata, amma ai da ko Haj an aika mawa.

Mun iso marabar jos, nayi ƙoƙarin tsaida hawayen da ke bin fuskata, Na dubi su Baba Rakiya, barci duk ya yi awon gaba da su. Tunanin babana yana ta bijiro min, da kuma tarihin shi da aka bani.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.5 / 5. Rating: 4

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Canjin Bazata 3Canjin Bazata 5 >>

2 thoughts on “Canjin Bazata 4”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×