Skip to content
Part 18 of 42 in the Series Da Magana by Khadija S. Moh'd (Matar J)

“Azeez dawo” cewar Aunty a tausashe. Bai dawo din ba, amma ya dakata wannan ya sa ta kuma cewa “sorry, the way you act na san ba kai ne ka fasa glass din ba. Just calm down please”

Bai ce komai ba, amma ina iya hango karfin bugun zuciyarsa ta cikin sports wear dinsa. “Zo ka wuce ka yi abin da ya kawo ka” ta kuma fada cikin sigar lallashi tana kallon shi.

Ya juyo daga rike handle din kofar da ya yi tare da wucewa wajen dakin shi, mu kuma mu ka koma kitchen.

“Aunty me ya sa Hammah ba ya son a shiga a dakin menene a ciki?” na jefawa Aunty tambayar ina kallon yadda take tattare wanke-wanke cikin sink.

“Ban sani ba Maryam, saboda ban taba shiga ba.” Ta ba ni amsa ba tare da ta kalle ni ba. “Me ya sa ba ki taba shiga ba to?” na kuma tambayarta

“Saboda ya yi kashedin ba ya so a shiga Maryam. Don Allah kar ki kara tambaya ta” ta karashe maganar cikin alamun gargadi.

Na dan murmusa kadan ganin yadda ta fusata. A Amarairaice na ce “Aunty to don Allah ki sanya baki, kar Hammah ya kori karen nan, na saba da shi”.

“Ban yi miki alkawari ba gaskiya, saboda ni ma ba na son zaman karen nan a gidan nan, an ce gidan da akwai kare mala’ikun Rahma basu shiga, mu kuma gamu da tarin bukatu da muke son mala’ikun rahmar su mika mana su can sama”.

Shiru na yi ba tare da na ce komai ba, kafin ta kuma cewa “Je ki wurin Azeez ki ji me yake so, na san yana can yana ta kumburi kamar zai yi aman wuta”.

Na fito zuwa dakin na shi, duk da kofar a bude take ban shiga ba kai tsaye sai da ya ba ni iznin shiga.

Kwance yake kan gado ko takalman bai cire ba yana taba wayarsa.

“Dama Aunty ce ta ce, tuwo aka yi, ko akwai abin da kake so a yi ma?” Ba tare da ya kalle ni ba ya ce “Wace irin miya ce?”

“Miyar wake ce, Hammah ne ya ce ita yake so. Ba ki ya tabe kafin ya ce” miyar ganye nake so idan akwai, amma ni tuwon semo nake so. Sai pepersoup na kayan ciki idan akwai”.

Na jinjina kai hade da juyawa da zummar tafiya na ji ya ce “zo nan” Na juyo da sauri saboda jin yadda ya yi maganar kamar a fada ce.

Ganin shi tsaye kan kafafunshi ya sa na kara nutsuwa. “Me kika nema a can dakin da har kika fasa glass aka dora min laifin?”

Na zazzaro ido a tsorace kafin in lalubo abun fada ya kuma cewa “Me kike nema na ce?” a tsawace ya yi maganar.

Cikin in-ina na ce “Dog ne na ga yana yawan kallon dakin yana haushi”

“To me ye a ciki din?”

“Babu komai” na fada a tsorace.

Ya zuba min ido, yayin da zuciyarsa ke nuna alamun baya tare da ni.

“Je ki.” ya ce ba tare da ya kalle ni ba.

Da sauri na fito dakin, sai kuma na koma na ce “Don Allah Ya Azeez kar ka fadawa Hammah ko Aunty ni ce na fasa glass din”.

Kai kawai ya jijjiga min, ni kuma na juya zuwa kitchen.

Lokacin da na shiga har Aunty ta gyare kitchen din tsab, kamar ba a yi girki ba.

“Me ya ce yana so?”

“Tuwon, amma na semo miyar ganye” na ba ta amsa

Baki ta tabe kafin ta ce “Idan ba zai ci wannan din ba ya bari, shi ya faye fi’ili tuwo kam ba duk tuwo ba. Kin dawo daga school ko hutawa ba ki yi ba, mu ka fara aikin nan, yanzu kuma shi ne zai kara dora miki wani, daga an tambaye shi.”

Na dan murmusa kadan “Ba damuwa Aunty zan yi mishi, tun da ba sallah nake yi ba.” “Ke ce kika aje wannan?” ta yi tambayar hade da miko min wata bakar leda.

Na karbi Ledar ina tattabawa ba tare da na kwance ta ba. Sai da tsoro ya dan kama ni, saboda jin duwatsun Aunty Adama da na kwashe, amma sai na daidaita nutsuwata na ce “Eh. Wani aiki zan yi da shi a school”

Ba tare da ta ce komai ba ta fice, ni ma sai na bi bayanta zuwa nawa dakin, cikin jakar makarantata na na jefa ledar dutsen kafin na koma kitchen domin girkawa Ya Azeez abin da yake so.

Can cikin bacci na rika jin haushin dog, ko ban fita ba, na san Hammah ne ya kai wa dakin shi ziyara, amma haka nan na mike zuwa falo na yaye labulen window ina kallon waje.

Wasu mutane ne ke kwashe kayan da ke dakin suna kaiwa part din Hammah, ina ta tsaye a wurin har suka gama kwashewa suka rufe kofar suka nufi part din Hammahn

Wannan ya sa na koma dakina cike da rashin jin dadin kwashe kayan ba tare da na gano amfaninsu ba.

Wanshekare na riga Aunty fita, bare Ya Azeez da na san ko sallah ma bai yi ba. Na tare napep zuwa makaranta, sai da na yi nisa da gida sannan na dakko duwatsun da ke cikin jaka ta na kwance su, na rika daukarsu daya bayan daya ina jefarwa har na jefar dasu gabadaya.

Kamar ko wane lokaci karfe shidda na yamma na koma gida, ba karamin mamaki na yi ba, da na iske ana wearing din cctv camera a sashen Hammah ba, a zuciyata na ce kamar wani gidan gwamnati.

Wurin dog na fara zuwa, abun mamaki bai ci abincin da aka sanya mishi da rana ba, da yake muna bar wa Hammawa abincinsu shi da monkey, na tattaba jikin wai ko bai lafiya, na duka sosai kusa da shi na ce “dog ba ka da lafiya ne? Ba ka ci abinci ba.”

Ya yi min kuri da ido kamar yadda na yi mishi. Na kuma shafa jikinsa cike da kulawa na ce “Dog kana lafiya Ko wani abu na damunka, ko abincin ne bai yi maka ba?”

Kallo na kawai yake yi, na juya kan Monkey da yake ta tsalle na janyo shi kusa da ni tare tsugunnar da shi na ce “Me yake damun ɗan’uwanka ba ya son cin abinci”

Ya kalle ni, ya juya ya kalli dog sai ya yi tsalle zuwa wurin shi yana taɓa fuskar da ɗan kukan shi “Uhh – uhh-uhhh”

Na mike zuwa kofar fita, sai da na kai kofa na juya ina kallon yadda suka jeru idanunsu a kaina, na dan murmusa kadan, sannan na fice daga cikin kejin.

Abincin na dauka na zubar a shara, na wanke plate din tas na wuce kitchen, bayan na gaishe da Aunty na ce “A sammana abinci”

“Karen ne ko?”

Na yi dariya mai sauti ba tare da na ce komai.

Ta bude flask din da ta zuba fara ƙal din shinkafa ta zuba min, ni kuma na zuba miya haɗe da sanya mishi katuwar cinyar Kaza, uffan ba ta ce min ba, na fice zuwa wurin dog, abun mamaki sai ya cinye abincin tas har da alamun neman ƙari. Ruwan ne bai sha ba sai da na zubar na canjo mishi wani, sannan ya sha.

Na zube mishi biscuit din da na sawo, shi kuma donkey na ba shi ayaba, kafin na wuce dakina.

Misalin karfe takwas na dare muna zaune a falo Aunty na yi min karin bayani a kan wani darasi da aka yi mana, Hammah ya turo kofar ya shigo.

Daga ni har Auntyn muka zuba mishi ido bayan mun amsa sallamar shi har ya karaso inda muke, na yi mishi sannu da zuwa, ya amsa a lokacin da yake haurawa saman Aunty, muka kuma bin shi da ido, saboda ni tun da na zo gidan ban taba ganin ya haura saman Aunty ba, iyakarshi falo, daga nan ya yi waje. Sai da ya bacewa ganinmu sannan muka dauke ido daga kanshi muka sauke shi a kan junanmu Aunty ce ta fara cewa “To lafiya?”

Kamar mai rada na ce “oho” ta mike a sanyaye zuwa saman. Ni ma a sanyayen na nufi nawa dakin.

Jiki a mace ta tura kofar dakin, sai ta cimma Hammah tsaye yana karewa dakin kallo kamar wani bako.

“Very nice Aisha. Yana daya daga cikin abin da ya sa nake son ki, kina da tsafta, da iya tsara abu, kalli dakinki komai yana aje a inda ya dace ga kamshi mai dadi, I love it.”

Ba ta ce komai ba, kallon shi kawai take yi, ji take kamar mafarki Hammah a dakinta, rabon da ya shigo dakinta an kai shekara goma, ba wai iya dakin ba, hatta kwanciyar aure ta shafe sama da shekaru goma ba tare da ta hada shimfida da shi ba.

“Zo mana.” Ya katse mata tunanin da take yi, a hankali ta ta ko zuwa inda yake, ya janyota sosai zuwa jikinsa tare da rungume ta, a tare suka sauke ajiyar zuciya.

Kamar wasa sai ga Hammah ya kusance ta a karo na biyu tun bayan auransu. Yana kokarin shiga toilet din ta ne aka kira wayarsa, ya dakata daga shiga toilet din yana amsa wayar, Sai da ya yanke kiran ne ya ce

“Ina zuwa Aisha” daga haka ya zira rigar shi ya fice daga dakin.

Ta bi bayan shi da kallo daga inda take kwance, ba tare da ta damu da goge hawayen da ke mata zarya a kan kumatunta ba, Hammah a dakin ta, har ya kusance ta a matsayin matarshi, ta dauka wannan ranar ta wuce har abada kuma ba za ta dawo ba.

Tun rashin zuwan gare ta yana damunta har ta share ta mayar da hankalinta wurin gina kanta, ta rika rayuwarta cikin dan karamin farin cikin da take samu, ko wane lokaci dai tana addu’ar Allah Ya kawo mata karshen duk matsalolinta.

Ta mike zaune tare da dauke hawayen da ke zubo mata, lokaci daya kuma ta dauko rayuwarta ta can baya.

<< Da Magana 17Da Magana 19 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.