Skip to content
Part 41 of 65 in the Series Daga Karshe by Matar J

Tun da Zainab ta amsa kiran Fatima, ba ta bata lokaci ba ta taho gidan.

Ba ta yi tunanin jikin Fatima ya yi zafi haka ba, dalilin da ya sa kenan ta ce Fatiman ta tashi su tafi can gidan Aunty Lami, amma fir ta ki zuwa.

Sai Zainab din ce ta debi jininta, ta tafi da shi can lab, sannan ta taho da duk wasu magungunan da ta san yana da alaka da ciwon Fatima.

Bayan ta iso ba ta bata lokaci ba ta sanya mata ruwa, tun Fatima na jin buruntun Zainab na gyaran dakin har bacci ya dauke ta.

A lokacin Zainab sallahr la’asar take yi.

“Ki cire min fitsari nake ji” In ji Fatima ta fada a hankali idonta a kan Zainab wacce ta idar da sallah.

Cikin kwarewa Zainab ta tsayar da drip din, sannan ta cire mata, sai da Fatima ta watsa ruwa sannan ta fito.

Daga ganin yadda take tafiya, za ka san tana jin jiki, ta zube sosai, ta kara haske.

Kan katifar ta zauna hade da karɓar kofin tean da Zainab ke mika mata.

“Ya jikin?” Zainab ta tambayeta cike da kulawa.

“Da sauki” Fatima ta amsa hade da mayar da kallon ta a kan ledar ruwan da ake kara mata.

“Wai har yanzu ruwan bai kare ba, kodai wani kika sanya?”

“Wani ne” Zainab ta ba ta amsa.

Fatima ba ta ce komai ba, illa sipping tea din da take yi a hankali.
Sai da ta sha rabin cup din sannan ta ajiye. Tana mayar da numfashi a hankali.

“Kin sa damuwa da yawa a ranki Aunty Fatee.” cewar Zainab tana kallon Fatima.

Fatima da kanta ke a kasa, ta dago hade da zuba ma window ido, inda take jiyo hayaniyar su Hassan da alama wasa suke yi.

Wata ajiyar zuciyar ta sake yi, tana fadin “Wannan shi ne bambancin dabba da mutum Zainab. Dabba ce kawai za ta shiga halin da nake ciki yanzu, kuma ba za ta nuna damuwarta ba.”

“Please you have to understand, I don’t mean ki ki damuwa amma ya yi yawa damuwa, look what is happening to you right now, while Shi yana can yana farin ciki cikin ƴan’awanshi. Do you think if you died now za a fasa bikin ne?”

Lumshe ido ta yi, hade da bude su a kan Zainab din” Please just forget, zo ki mayar min da ruwan.”

A yadda take zaunen Zainab ta mayar mata da drip din, yayin da Fatima ke ta kallon ta cike da sha’awa.

Abin da taso yi kenan, Allah bai nufa ba, amma tana fatan nan da dan wani lokaci muryarta ta karade kunnuwan ma’abota sauraron radio.

” Sannu. ” Zainab ta ce bayan ta koma ta zauna.

“Yauwa. Na gode” Fatima ta amsata idanuwanta a kan hannunta mai dauke da allurar karin ruwa.

“Aunty na ta kira fa, amma na fada mata da sauki, ta ce in kwana gobe za ta zo ita ma.”

“Na gode” Fatima ta fada a hankali.

“Ya Mustaphan bai kira ba?” Zainab ta canja hirar tasu.

Ba ki Fatima ta tabe sannan ta ce “I don’t know, my phone is off.”

” Why now, you have to on it, na tabbata zai neme ki.”

Murmushi takaici Fatima ta yi, sannan ta ce “Ya ce min me? Ba ma zai neme ni ba, tun da yaushe rabon da ya yi hakan.”

“Are you serious?”

“I’m very serious. Nawa za a ba Ni Zainab idan na yi mishi karya?”

“Kai! Wonders shall never end.” Zainab ta fada mamaki karara a kan fuskarta.

“Zainab!” Fatima ta kira sunanta a hankali, lokaci daya kuma tana jan bayanta zuwa jikin bango.

“Na yarda da Ya Mustapha, ba wai yardar ba zai taba min kishiya ba not like that, irin dai komai runtsi ba zai watsar da ni ba, haka ba zai taba janyewa daga gare ni ba ko juya min baya ba. Amma abun mamaki Ya Mustapha tun da na shigo garin Katsina da sunan karatu bai taba kirana ba, tsakanin text ne kawai, shi ma ba ko wane lokaci ba. Yana tura min 10k duk sati, amma bai taba tambayata ya karatuna ba, bare ya zo ya ga inda nake, tsawon wata biyu kenan.” Ta kai karshen maganar hade da share hawaye masu dumi.

” Zainab na so daurewa da kawar da kai, hade share duk wani lamarinsa, amma zuciyata ta kasa yin hakan, wani daci da zafi nake ji a nan dina. ” ta kai karshen maganar cikin rawar muryar kuka, hade da nuna kirjinta da hannunta.

“Please don Allah ki yi hak’uri Aunty Fatima, I’m very sorry, Komai zai wuce sha Allah”

“Kafin ya wuce fa Zainab? Ya Mustapha a cikin garin Abuja, zai rayu da wata ba ni ba, ke duniya.”

Duk sai suka yi shiru, jin kukan Hussain a waje.

Zainab ce ta leka, Abida ke sanar mata faduwa ya yi, shi ya sa Zainab din ta dawo daki hannunta dauke da shi.

Abuja

Blessing kwance a kan gado tana jiyo hayaniyar ƴan’awanta a waje, da kuma wasu a cikin daki, maganarsu dai ba ta wuce ta fasa yin Shuwa day din da aka yi, duk sun ji haushi, shi ya sa kowa da albarkacin bakin sa.

Ita kam Blessing tana tuna maganar da suka yi da Momynta ne a waya, inda ta shaida mata Mustapha ya ce ba zai je wajen taron ba, sannan ta fadawa Momy cewa Mustapha yana damuwa ne saboda Fatima ba ta zo ba, kuma ba ta daga wayar sa don tun jiya ta fahimci wa yake kira. Ta kara da fadawa Momyn tata Mustapha yana son Fatima sosai da alama ita zaman je ki na yi ki kawai za ta yi a gidan.

Cike da kwantar da hankali Momyn ta ce “This will not happen my daughter, yarenmu basu zama kamar bola a gida, ladabi, biyayya, ki rike yaransa da kyau, ki kawar da kai, ki girmama matarsa, iya abinci da tsafta, za ki sha mamaki, sannan ki dage da addu’a.”

Za ta yi duk yadda Momyn ta fada mata. Ita ma sai ta, zama wata tauraruwa mai haske da Ikon Allah.

Mustapha kam dai, kasa daurewa ya yi, ya tambayi Aunty Hauwa ko no Fatima na zuwa, ita ta shaida mishi ta kira ba ta tafi ba, haka ma Ummi ta shaida mishi.

Koda Aunty Hauwa ta tuntubi Ummi, sai Ummin ke shaida mata ai Fatiman ba ta lafiya, ruwa ma take kara mata, amma kar a fadawa Mustapha.

A hankali rashin lafiyar Fatima ta zagaye kunnen ƴan’awanta, ba sai an tambaya ba, sun san damuwa ce, su ma sai suke jin kamar basu yi mata adalci ba, yadda suka kwashe suka taho wurin bikin, amma kuma ya suka iya, Mustapha ya cancanta, idan basu zo ba, za ace kishi suke taya Fatiman.

Tun safe kuwa suka biyo mata sai Katsina, ko fansar amaryar basu jira an yi ba, karfe daya a lodge din su Fatima ta yi musu.

Ba laifi ta dan ji sauki a lokacin, zaune take ita da Zainab da kuma Aunty Lami da ta zo tun safe.

Hira suke yi kadan-kadan, ma fi akasarin hirar a kan yadda maza ke butulcewa mata ne, bayan sun samu kumbar susa.

A daidai lokacin ne su Aunty Hauwa suka kwankwasa kofar. Zainab ce ta bude, suka shigo dukkansu idanuwansu a kan Fatima da take kinshigide, duk kuma surutu da hayaniyar da suke bai sanya ta tashi ba, ko ta ce musu wani abu ba.

Har zuwa lokacin da hankalinsu ya koma kanta, Aunty Hauwa ce rike da haba ta fara cewa “Ke Lami, ki ce ciwo sosai, yo kalli yadda Fatiman ta zama”

“To sosai hwa, ledar ruwa uku ta shanye” Aunty Lami ta ce tana kallon Aunty Hauwa.

“Subhanallah!Fatitti babbar masoyiyata, Allah sarki sannu”
Cewar Aunty Aisha tana zama a gefen Fatiman.

Karon farko da Fatima ta yi murmushi, amma ba ta ce komai ba

Daya bayan daya suka rika yi mata sannu, hade da nuna tausayawarsu gare ta.

Daga nan kuma hirar bikin suka shiga, irin kayan da Blessing ta sanya masu tsada, dukiyar da aka tsattsaga mata, irin yanayin familynta, rawar kan da Mustapha ya yi, duk Fatima na jin su, idan ba neman ta suka yi da magana ba, Sam ba ta son yin ta.

Saboda maganganunsu kara jefa mata tsoro suke yi, ta ya za ta iya kishi da Blessing, macen da ta shi cikin kudi, kuma tsakiyar birni, ga ilmi lallai akwai kalubale a gabanta.

Suka saki hirar Mustapha aka shiga ta bikin Zainab wanda za a yi sati hudu masu zuwa, ita dai jin su kawai
take yi, abun dariya ta dara wani lokaci kuma ta dan tofa wani abun.

Zainab ce ta yi musu abinci, suka ci sannan suka shiga shirin tafiya.

A lokacin ne su kai ta, kwantar mata da hankali hade ba ta, shawarwarin zama da kishiya, da yadda za ta karkato hankalin mijinta a kanta.

Sai misalin biyar suka bar gidan, har da Zainab aka tafi.

Haka ta lallaba ta shirya duk wani abu da za ta bukata gobe a wurin lecture, kamar yadda Aunty Ayyo ta ce, ya kamata ta fuskanci gaba, ita ma ta gina rayuwarta, kar ta bari ginin da ta faro ya lalace, to ta daura aniyar fuskantar gaba, tare da ba ginin da ta faro foundation mai kyau, ta yadda ita ma za ta zama madubin wasu a nan gaba.

Lokacin da su Aunty Hauwa suka zayyanewa mama labarin yadda biki ya kayatar da kuma rashin lafiyar Fatima sosai ta ji zafin abun, gani ta ke yi tamkar dai Mustapha ya ci moriyar ganga ne, amma idan har haka ya ce zai yi, ba za ta amince ba, ba za ta yarda a wulakanta mata yarinya ba.

Tun da suka bar gidan Mama ke gwada layin Fatima amma baya tafiya, sosai take son jin muryarta ko ba komai za ta fi samun nutsuwa idan ta ji muryarta.

Layin Zainab ta kira, ta shaida mata lallai gobe ta koma wajen Fatima ta hada su a waya tana son magana da ita.

Abuja

Sosai Mustapha baya cikin nutsuwarsa, saboda rashin samun Fatima duk da Blessing tana kokari wajen kwantar mishi da hankali.

Blessing mace da ta amsa sunanta mace, bangaren girki, tsabta, iya tarairayar miji, abu ma fi muhimmanci da burgewa a gare ta shi ne yadda ta kawo mishi budurcinta, wannan ya kara tabbatar mishi da a ko wace irin kabila, addini tabbas ana samun na gari.

Ko don wannan bajintar ita din ba ta cancanci wulakanci ba, uwa uba yadda ta shigo addini da kyakkyawan zaton ta akan musulmi yana son ta sami musulunci fiye da yadda ta yi tsammaninsa

Da yawan masu shiga musulunci su kan yi kuka da yadda ake goronta musu, rashin taimaka musu, da kuma yadda wasu mazan kan wulakantasu bayan sun auresu, saboda yadda suke ganin basu da mafita, ko sun koma wajen ƴan’awansu ba zasu karbe su ba.
Shi ya sa wasu ke tsoron karbar musulunci.

So yake ya goge wannan tunanin a zuciyar Blessing ta san ba duk aka taru aka zama daya ba.

Shi ya sa yake iya kokarinsa wajen ganin bai yi mata wani abu da za ta yi danasanin shigarta musulunci ba.

Katsina

Sai misalin karfe shidda na yammacin Litinin mashin ya sauke Fatima ita da Abida kofar gida.

Ko wace Monday haka ne yake faruwa da ita, lectures tun daga safe har yamma.

Tana kokarin bude daki ne Zainab ta turo gate din ta shigo

“Lafiya?” Fatima ta yi saurin tambaya bayan ta dakata da bude kofar da take yi.

“Ƙalau”
Zainab ta fada Lokacin da take zama a entrance din kofar.

Ita ma Fatiman sai ta zauna, bayan ta budewa Abida kofar, ta kuma ba ta umarnin shiga tare da su Hassan.

“Wai ku haka wannan gidan kuke kamar Mayu kowa a daki, sai ka ce ba students ba?”

Tabe baki Fatima ta yi kafin ta ce “Ke ma dai kya fada, tun ban saba ba har na, saba, wlh akwai wadanda har yanzu ni ban taba ma ganinsu ba. Wadanda ma na ganin gaisuwa ce kawai tsakaninmu. Amma da zarar kin nemi taimako za a yi miki.”

“Mama ce fa ta dame ni tun jiya da dare, lallai in kawo miki waya.”

Murmushi Fatima ta yi hade da faɗin “Allah sarki uwata, uwa daban ce, kira min ita.”

Zainab ta mika mata wayar bayan ta shiga, sai da ta kusa katsewa sannan aka daga, Zainab ta ce “Yanzu haka wayar na cikin kwagiri.”

Fatima ta dan kai mata duka, yayin da Mama ke fadin “Ki ce mata uwata ce kwagirin.”

Dariya Fatima ta yi hade da gaishe da Maman.

Ta amsa cike da kulawa hade da tambayarta ya jikinta

Ta amsa mata da sauki, sannan Maman ta ce “Ina wayar ta ki, sai ai ta kira ba ta shiga?”

“Tana nan.”

“To ki kunna ta, ba na son in kara kira in ji wai a kashe, kina son kashe kanki ne ke daya a daki? Ai ba Mustaphan ne kawai ke kiranki a wayar ba.”

“Sha Allah zan bude Mama.” ta fada a ladabce

“Yanzun nan” cewar Mama da muryar bayar da umarni

“To.” ta kuma amsawa

“Kuma ki tabbatar an yi bikin Zainab da ke.”

“In sha Allah”

“Sannan idan har ni na haife ki Fatima ban ce ki kara sanya damuwar Mustapha a ranki ba, ki fuskanci abin da ke gabanki, dan halak dai baya manta alkairi, na san kuma bai manta da duk wata sadaukarwa da kika yi mishi ba. Idan zai auri mata dari, gaba kika yi suka biyo bayanki, kuma duk yaran da zasu haifa mishi naki ne dai manya. Kuma mu talakawan nan, mune muka fara mishi rana kafin masu kudin.”

Fatima ta murmusa kadan, don dama ta, san Mustapha a wuyanta yake, cikinshi gare ta, neman wurin da za ta haife shi take yi.

A hankali ta ce “In sha Allah Mama ba zan kara damuwa ba.”

“Yauwa, ki kuma bude wayar na dai fada miki.”

“Yanzu kuwa sha Allah.”

Da haka suka yi sallama ta kokawa Zainab wayar, tana fadin “Mama fa ta hau sama.”

Zainab ta yi murmushi “Ba dole ba, an taba mata masoyiyarta. Amma Aunty Fatima don Allah ku rika kyautatawa Ya Mustapha zato, haka ma su Aunty ke tsigarshi uwa tafasa.”

Mikewa Fatima ta yi “Don Allah Malama ki yi ta kanki, idan abin da ya kawo ki kenan, to ni zan shige ciki in yi sallah.”

“Inyeee!” cewar Zainab a lokacin da ita ma take mikewa tsaye “Dole fa ki ce haka mana, tun da na gama dura miki ruwa kin farfado.”

“Zo ki kwashe abun ki.”

“Za ki faɗi komai yanzu, tun da kin samu kishi bai kashe ki ba.”

Da sauri Fatima ta kai mata duka tana fadin “Uwar kishi ma.”

“To karya na yi?” Zainab ta tambaya tana hararar Fatima

Tsoki Fatima ta yi hade da bude kofar ta shige, ta bar Zainab tsaye a waje.

Ita ma Zainab sai ta nufi gate kawai, tana dariyar mugunta, saboda ta san ta yi wa Fatima 1-0.

Sai misalin karfe goma na dare ta kunna wayar, a lokacin kuwa ta gama komai na al’ada.

Ko minti daya ba ta yi da budewa ba, kiran Mustapha ya shigo.

Sai da ya yi mata kira uku sannan ta daga, hade da canja murya irin ta mai bacci.

“Ina kika ajiye wayar?”
Abin da ya fara tambaya kenan bayan ta daga.

“Bacci nake yi.” ita ma ta amsa shi da muryar baccin.

“Ina nufin tsawon kwanakin nan?”

Shiru ta yi har sai da ya kara maimaita tambayar sannan ta ce “Na kai gyara ne.”

“Ina son mu hadu a gida ranar Juma’a”

Wani murmushin takaici ta yi sannan ta ce “Ba zan samu zuwa gida ba sai bikin Zainab, saboda C.A Test muke yi.”

“Fatima a matsayina na mijinki, umarni nake ba ki, ba wai alfarmarki nake nema ba.”

“To!” ta fada hade Mikewa zaune, yau take ganin karfin hali wai sata lahira.

“Amma ni ma na fada ma uzurina, lokacin da ka yi naka karatun goyon baya na rika ba ka, ba, tirsasa ka yin abin da zai kawo matsala a karatunka ba.”

“Na san babu wata test, kamar yadda wayarki ba ta lalace ba. Kawai kina wasa da hankalina ne. Saboda haka mu hadu a gida ranar Friday.”

“Ya Mustapha gaskiya na fada ma, ni da gida sai nan da sati uku, saboda ina da abubuwan yi a makaranta, ban matsa dole sai ka yarda da duk wani abin da zan fada ba, amma gaskiya ta na fada ma, sai an jima.”

Ba ta jira me zai fada ba, ta kashe wayar gabadaya.

Matar J✍🏻

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Daga Karshe 40Daga Karshe 42 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×