Skip to content
Part 42 of 65 in the Series Daga Karshe by Matar J

Rai bace ya aje wayar bayan ya tabbatar da yanke kiran ta yi, ta kuma kashe wayar gabadaya.

Har yanzu ta kasa gane ita mai laifi ce, maimakon ma hakan kara damalmala lamarin take yi.

Ta san dai banza ba zai dauki tsawon wannan kwanakin ba tare da ya ganta ko jin muryarta ba, amma har yanzu ba ta gane fushi yake yi ba.

“Anya Fatima na sona kuwa?”
Ya yi ma kansa tambayar, da kansa kuma ya ba kansa amsa.

“Ba na jin akwai soyayyata a kirjinta, soyayya ita ke kawo kishi, ban taba ganin Fatima ta yi wani abu mai kama da kishi a kaina ba, ko lokacin da aka fada mata zan yi aure ko a jikinta, hasalima ni ne hankalina yake tashe ba na ta ba, lokacin da bacci ya kaurace mini da damuwar maganar auran, ita zuwa na yi na same ta hankalinta kwance tana baccinta” a bayyane ya yi maganar cike da kunar zuci.

Tun daga lokacin da aka tsayar da ranar auran zuwa yanzu bayan auran ba ta taba tanka shi ko nuna bacin ranta ba, hasalima tana fushi da shi ne, saboda bai nuna goyan bayanshi a kan makarantarta ba.

Shi kuma gani ya yi ya kamata ta yi shawara shi kafin ta yi komai musamman abu babba da ya shafi karatu.

Haka yay ta sakawa yana kwancewa, ga ni yake Fatima amfani kawai ta yi da shi, wurin ganin ta kaucewa auran Jamil, ya yi mamakin yadda bai gano hakan ba sai yanzu.

Wannan daren da ku san tunanin Fatima da kuma hukuncin da ya kamata ya yi mata ya cinye sa.

Katsina

Bayan ta kashe wayar kasan pillow ta tura ta, hade da jan siririn tsoki, ban da miji, miji ne, yana da girma a idanunta, yau da maganganun da za ta fada mishi, ai ko cikin labarinsa ya ji an ambaci sunan ta sai ya yi waige-waige.

To shi din mijinta ne, yana da girma ila idanunta, bai cancanci baƙar magana, ko ya rika fada tana fada ba

Amma kam Mustapha ya koya mata darasin rayuwa, ba za ta kara yarda hade sakankancewa da kowa ba, zuwa yanzu da kanta kadai take jin za ta rika yarda, don ta san ba za ta ci amanar kanta ba.

Amma mutum ta yi fama da shi, da dadi ba dadi, lokaci daya ya gudu Abuja ya yi auransa ya manta da lamarinta, sai yanzu daga sama ya zo yana wani ba ta umarni wai su hadu ranar Juma’a a gida.

“Ya yi min me?” ta yi tambayar hade da mikewa tsaye, lokaci daya kuma ta amsa tambayarta

“Ni! Allah Ya sawake min, wannan kwadon, a kwana da wata ni ma a zo a Kwana da ni. Ba zan iya ba.”

Ta kai karshen maganar daidai tana shiga kitchen.

“Idan ba namiji ma da rashin ta ido ba, shi yanzu bai jin kunyar hada ido da ni, wai ya kwana da wata macen bayan ni.”

Haka tai ta surutanta ita kadai, har zuwa lokacin da bacci ya dauke ta.

******

Fushi ya yi da ita sosai, shi ya sa ko ƴar 10k din da yake tura mata duk karshen sati wannan satin bai turo mata ba.

A lokacin ne ta san kudin na da matukar amfani a wurin ta, don ko pampers din yara ba ta da, dalilin da ya sanya ta zuwa gidan Aunty Lami dole, a can ta wuni sannan ta samo yan kudi ta dawo.

Abin da ta daukarwa ranta, idan za a shekara sha Allah ba za ta tambayi Mustapha komai ba, ta kwammace ta siyar da duk abin da ta mallaka da dai ta tambaye shi, to tururuwa ma ta yi jeren banza bare ranar garar ƴarta.

Bikin Zainab dama ta cewa Ummi a cikin ribar da suke samu ita a tara mata 10k, za ta ba Zainab gudummawa ne.

Kuma Ummin ta ce an samu 10k din, shi ya sa hankalinta kwance tana da abun gundumawa, dinkunan biki kam yayyunta da Mama duk sun yi mata ita da Hana, Ziyad ne da Yan biyu ba ta san an yi musu ba ko a’a.

Ita dai ba za ta cewa Mustapha ya yi ba, sai dai su ci bikinsu da tsaffin kaya, kuma ko a jikinta.

Ana saura kwana uku daurin aure, ta bi tawagar amarya wacce Aunty Lami ta jagoranta.

Gidan Mama ta sauka, inda gidan yake cike da ƴan’uwa, sai farin ciki ya cika ta, duk lokacin da ake wani taro ta ga gidan cike kuma dukkansu ƴan’uwa ne sai ta ji wani irin dadi mara misultuwa.

A ranar ma Jamil ya iso, amma bai zo da gimbiyarsa ba. Wai cikinta ya tsufa

Ya kara cika, da zama dangayu jin dadi da hutu duk sun bayyana a jikansa.

Ranar kam an sha hirar zumunci, har wajen biyun dare basu yi bacci ba.

Washegari laraba da misalin karfe hudu na yamma gidan gonar Hikimi cike yake da ƴan’uwa da kawayen amarya, inda za a yi kauyawa day, shagalin ya yi kyau, ya kayatar hade da nishadantarwa, kasancewar duk abin da aka yi a wajen da kuma abin da aka ci na gargajiya ne.

Fatima kam ta ci rawa kamar ba gobe, da ma ita da rawa 5&6 ne.

Sai bakwai na yamma suka tashi, da yawansu gidan Mama suka yada zango, tun da ta shigo Sandamu har yanzu ko hanyar gidanta ba ta bi ba, gidan Ummi kadai ta dan leka dazu da zasu tafi kauyawa day.

Misalin karfe tara na dare duk sun baje a tsakar gidan suna ta hira, yara kuma wasu duk sun yi bacci, ciki kuwa har da su Hassan da Fatima take barinsu a wurin Mama ta tafi sabgoginta, saboda ba ta taho da Abida ba.

Aunty Ayyo ce ta ce “Wai Mustapha kam ba ya zuwa?”

Sai da Fatima ta gama hamma sannan ta ce “Oho.”

“Yo ba ku yi waya ba?” Aunty Ayyon ta ta kuma tambaya, bayan ita ma ta gama hamma

“Ba mu yi ba.” Fatima ta amsa ta.

“Amma kam ai ya kamata ya zo?” Aunty Aisha ta tsoma bakinta a hirar.

“Ba fa dole, me ye hadin kifi da kaska, na ga dai ba dan’uwanku ba ne, ba kuma na Hakimi ba, idan bai zo ba me ye laifi?”

“Ji wata maganar banza…” Aunty Sadiya ma ta tsoma nata bakin.

“Maganar banza ko ta gaskiya, me kuka hada da shi?”

“Ai ko mu muka hada komai da shi, tun da mun wanke ƴa mun ba shi, kuma ta haihu da shi, ko yaƙi ko ya so, jininmu na yawo a jikin jininsa.”

“To! Kun ji wata shiga uku da kalar dangi. Don Allah ku ji fa Aunty Sadiya da wata ƙissa, wannan jone-jone har ina.

Aurena fa kawai yake yi, to ni kaina muna da wata alaka da shi ne bayan ta auran? In yanzu na har auran na shi me ye hadina da shi kuma, ƴaƴa fa kawai na haifa mai, bayan nan kuma me ye yi saura? “

“Uhhh! Fatima dai har yanzu hakkilo wala am, in ji Fulani” cewar Aunty Aisha

“Bai zo ba” Fatima ta fada, hade da gyara kwanciyarta.

“Hankalin ne bai zo ba?” Aunty Sadiya ta kuma tambaya.

“Eh.” Fatima ta amsa

“To Allah Ya kawo shi”

“Amin” ta amsa a lokacin da take yin wata hammar.

Aunty Ayyo ta ce “Amma idan har abun na kai da kitso ne ai ya kamata ya zo, mu muka kwashi kafarmu har Abuja”

Mikewa Fatima ta yi zaune “Ai kuma rashin kishi ne ya kai ku da nuna rashin son ƴar’uwarku, ai wlh dama a nan dina kuke( Ta nuna makogoronta) idan ba ku ba a ina aka taba yin haka, ana yi wa ƴar’uwarku kishiya, sai kawai ku kwashi jiki ku tafi wurin biki, ni ban san ma a matsayin da kuka je ba”

Duk suka saki dariya a tare, kafin Aunty Aisha ta ce “to ba mun gano gari ba, gari ya gan mu. Duniya ai ido take”

“Ke kyale ta ma, ubanwa ya hana ta dawowa a yi bikin, ai har cewa ya yi ta je Abujar ta ki zuwa. Da ta dawo gida me zai kai mu wata Abuja.” Cewar Aunty Sadiya.

“Ban zuwa, ni ba mayyar Abuja ba ce, kuma ni ba zan je in zauna a gidan alfarma ba.”

Aunty Ayyo ta ce”To su waye mayun Abujar?”

Fatima ta saki dariya ba tare da ta ce komai ba.

“Yar rainin wayau, kuma maganar gida, nata daban na ki daban, don dai suna kan layi daya ne, ita tsohonta ne ya ba ta, ya ce su zauna har sai Mustaphan ya gina nasa, na ki kuwa wanda aka ba shi ne a wurin aiki.”

Tabe baki Fatima ta yi, duk kuwa da ba ganinta suke yi ba, hade da komawa ta kwanta.

Yayin da take jin su suna ci gaba da hirarsu

Yau ma hira sosai suka yi, kafin bacci ya dauke su.

Safiyar Alhamis aka kuma tashi da shagalin biki, inda amarya da kawayenta maza da mata zasu yi party a gidan Ya Basheer da yamma.

Gidan Hakimi kuwa uwar amarya ce da gayyarta suma zasu yi nasu shagalin (mothers day)

Tun safe mai kunshi ta zo, ta rika watsawa amarya, kawayen amarya da daginta kunshi.

A lokacin da ake wa Fatima lalle ne wayarta da ke kan cinyarta ta yi kara, ganin sunan Mustapha ba karamin mamaki ta yi ba, saboda rabon da su yi yawa, tun da ya ce su hadu a gida, ita kuma ta ki zuwa.

Har kiran ya yanke ba ta daga ba, kamar minti daya sakonshi ya shigo, inda yake shaida mata ya iso yana gida.

Bayan ta karanta sakon sai ta goge, ko ba lalle ake mata ba, ba ta jin za ta je, bare ma ana mata lalle ne.

Tun Mustapha na jiran tsammanin zuwan Fatima, har gaji da tsugunno a kofar gida ya buge (ƙwage) kwadon kofar gidan, ya kuma buge na dakin Inna Blessing ta shiga da kayanta.

Yanayin yadda ya ga gidan ya tabbatar masa Fatima ba ta leko gidan ba.

Duk sai ya buge kwadunan gidan, har da na bangaren Fatima yadda ya ga kura ta mamaye dakin ya ƙa tabbatar masa da zarginsa.

“Wani abu sai Fatima.” ya fada a bayyane, yayin da wani murmushin da shi kansa bai san na menene ba, ya bayyana a kan fuskarsa.

Sosai ta canja, yanzu kam ta koma mishi asalin Fatimarta ta da.

Abun da take ganin shi ne daidai a wajenta shi take yi.

Kayan jikinsa ya rage ya shiga gyaran gidan, yayin da Blessing ke taimakonsa, cikin awa biyu suka gyara gidan fes, kafin suka shiga neman abin da zasu ci.

Bangaren su Amarya kuwa misalin karfe biyar gidan Ya Bashir a cike yake, yayin da sauti ke tashi da sowar matasa, shagali kawai ake sha kowa fuskarsa cike da farin ciki.

A lokacin ne kuma Mustapha ya tsaya kofar gidan yana laluben wayar Ummi, don ya tabbata tana cikin gidan.

Blessing kuwa tana gidan Aunty Hauwa, inda ake ta rakashewa da kidin ƙwarya.

Sai da Ummi ta koma gefe, sannan ta iya jin me Mustapha ke cewa. Fada mata yake, ta fito mishi da Fatima yana kofar gida.

A lokacin Fatima cikin fili take suna ta cashewa, Ummi ta lalubo hannunta hade da janyo ta daga cikin filin zuwa waje.

Fatima bin ta take yi, tana tambayar “Wai ina za ki kai ni, lafiya kike ta Jana kamar kin sawo akuya?”

Ba ta dakata ba, sai da ta shigo zauran gidan inda Mustapha ke tsaye hannayensa zube cikin aljihunsa.

Take ta canja fuskar ta hanyar hade girar sama da ta kasa, musamman yadda Ummi ta fita daga zauran ta bar su

Kallon ta yake cikin ankon atamfar Java ja da digon fari, riga da siket ne da suka fito mata da kyan surarta, kunshi da aka yi mata ya kara haska farar fatarta.

Yar ramar da ta yi, sai ta kara mata tsawo kadan, hade fitar mata da siririyar fuskarta.

Ko dan ya jima bai ganta ba, sai ta yi mishi kyau sosai, kewar da yake ji tata ta karu, tun ba yadda din kin ya fitar mata da shape din kirijinta da kuma kwankwasonta ba.

“Wuce mu tafi gida” ya yi maganar bayan ya janye idonsa daga kallon kurillar da yake mata.

Sai da ta tura baki sannan ta ce “ai ba a tashi ba.”

“A nan ma gardamar za ki yi min?”

Shiru ta yi hade da turo baki.

“Ki wuce mu tafi, idan ba haka ba, Fatima zan shayar da ke mamaki, zan nuna miki karyar rashin kunya kike yi, wlh zan dauke ki a hannuna, daga nan har gida.”

Ta dago hade da kallon sa, sanye yake cikin yadi baki mai walkiya, wanda aka yi wa kwalliya da jan yadi a dai Saman kirjinsa da kuma aljihun rigar.

Ya fito da kirarsa ta lafiyayyen namiji, mai tashen kuruciya, yayin da hutu sosai ya bayyana a fatarsa.

Shiru ya ratsa wajen, kafin ya katse shirun da “You’re wasting my time madame.”

Sai da ta tura baki, sannan ta zo ta wuce shi kamar za ta hankade shi “Better” ya fada hade da bin bayanta.

Ita ce a gaba yana bin ta a baya, kallo daya za ka yi mata, ka fahimci ba da son ranta take tafiyar ba.

Daga can kuma su Aunty Ayyo ne da Blessing suka baro gidan Aunty Hauwa zuwa gidan Ya Bashir nan ma su kashe kwarkwatar idonsu.

Aunty Aisha ce ta, fara tuntsirewa da tana fadin “” “Wai me ye can a gabanmu nake gani? Allah Rahimi in ji Aunty Hauwa.”

Lokaci daya suka mayar da kallon su kan su Fatima da suke tahowa.

Aunty Sadiya ma dariya ta saki kafin ta ce “Kai Allah muna ganin Ikon ka, ji yadda ya taso ta gaba, kamar wani ubanta, irin ta yi laifin nan ya kamo ta to ko lafiya oho musu”

Aunty Ayyo ma cikin dariya take fadin “Alhamdulillahi da na zo a zuriyar Alhaji Musa Lawan jika, da ace ban zo a ciki ba, Lallai da na yi missing din abubuwa da yawa.”

Blessing dai yake kawai take yi, Allah Ya sani tana kokarin danne kishinta ne kawai a kan Fatima, amma ko makaho ne ya lalubo zai gano irin zallar soyayyar da Mustapha ke yi mata.

Tun da suka iso ta fahimci hankalinsa baya jikinsa, ma ce ta tafi wajen wata uku, ta dawo ba ta sauka a gidanta ba, ka kira ta cewa ka iso, amma ta ƙi daga kiran sai dai ta shanyaku a waje, daga karshe ka buge kwadunan gidan, sannan ka fada gyara mata gida, kuma kai ne za ka je ka taso ta. Tana cika tana batsewa, anya kuwa za ta iya jure wannan zaman.

Lokacin da suka iso wurinsu Fatima wuce su kawai ta yi ba tare da ta tanka su ba. Mustapha ne kadai ya tsaya suka gaisa da su Aunty Ayyo hade da yi musu Allah Ya sanya alkairi. Kafin ya bi bayan Fatima.
Ita ko Blessing dama ba ta tsaya ba, gaba kawai ta yi abun ta.

Lokacin suka isa kofar gida sai da ta jira ya bude kofa, dalilin da ya sanya kenan ya riga ta shiga.

Shigar ta ya yi daidai da janyo ta jikinsa, hade da tura kofar gidan ya sa sakata.

“Yanzu fada min, wa kike turawa baki?”

Kara tura bakin ta yi, hade da kokarin kwacewa.

Ya tura ta jikin bango, hade da kama lebenta na sama ya ciza a hankali.

“Fada min Fatima kina sona kuwa?”

Ta Yi saurin janye idanuwanta a kan nasa, saboda abin da ta gani a cikinsu.

“Ina jin ki”

Ganin ba ta da niyyar magana, sai ya kuma matse ta da bangon sosai.

Ta Yi yar kara kadan.

“To ina jin ki fada min.”

“Ni ma ban sani ba” sai da ta bata rai sannan ta yi maganar.

Ya dan rage matsewar da ya yi mata, yana fadin “Ba kya sona, kawai kin yi amfani da ni ne, yanzu kuma kina zaune da ni don yaran ki. Almost 3 months Fatima ko a jikinki ba ki ji kewata ba, da alama ko za a shekara ba za ki damu, kin zo amma ko gidanki ba ki waiwaya ba. Kodai ina miki wani abu ba daidai ba ne? “

Shiru ta yi, yayin da jikinta ya saki, shi kansa ya fahimci hakan.

Ba ta nuna alamun za ta yi magana ba, shi ya sa ya ja hanunta ya na fadin” Let me show you how much I missed you.”

Duk irin borin da take yi, na ba zai hada shimfida da ita ba, ita ba ta shirya ba, bai saurareta ba, dole ta koma rokonshi, a kan don Allah ya yi mata hakuri, ba ta sha komai ba, kuma ba ta son yin ciki yanzu saboda karatunta, maimakon ya ji rokon nata, sai maganar ta tunzura shi, ita yanzu babu komai a gabanta sai karatunta, karon farko da ya bukace ta ta yi mishi gardama saboda karatunta. Addu’ar shi Allah Ya sa ta samu ciki a yau din nan.

Matar J

<< Daga Karshe 41Daga Karshe 43 >>

1 thought on “Daga Karshe 42”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×