Ko da suka bugama Salim wani sanda nan take ya zube ƙasa warwas, babu ƙarfi a tare dashi, sun sa masa hannu a aljihu sun kwashe duka kuɗin da ke ciki suna shirin ɗaukar wayan ne a ɗayan aljihu sai wasu mutane suka zo gurinsu da gudu suna ihu ɓarayi. Nan suka saki Salim suka ruga ana kare.
Ko da suka duba Salim sukaga basu ji masa rauni ba kaɗai buga masa sanda ne da suka yi akansa wanda har gurin ya ɗan kumbura. Ɗa gasa sama suka yi tare da bashi kayautar ɗari biyu ya je ya. . .