Skip to content
Part 1 of 10 in the Series Duniyar El-Dorado by Abubakar Abubakar

Note:

Sau da yawa mutum ya kan wuni lapia, haka kuma ya kwana lapia sai kuma ya wayi gari cikin wani ibtila’in ko gararin rayuwa da tashin hankali ko firgici wanda ka iya kasancewa tabo watau trauma a rayuwar bawan, irin wannan juyin yanayin dake kawo tabbataccen canji na har abada a rayuwa, koda yake dama shi rikicin duniya ai sai da me rai ake yinsa. Masu iya magana sun qara tabbatar da hakan da suke cewa inda ranka zaka sha kallo!

*****

PRESENT DAY

Kirikiri Maximum Security Prison, Apapa, Lagos State, Nigeria

Mai yasa zai zama itace mutum ta farko da zata ziyarce shi in this Godforsaken place?. Yaushe rabon ta da shi? Shin a ina ma taji cewa yana gidan yari? Mai kuma taxo yi ko ji a wurinsa? Wadannan sune ire iren tambayoyin da kwakwalwarsa ke jeho masa tun lokacin da yaji sanarwar cewa ana nemansa  zuwa dakin ziyara, bayan yabi diddigine a gun wani gandiroba daya bayyana masa cewa mace ce baquwar tasa wanda jin hakan ne kuma yasa ya nemi gandiroban daya siffanta masa ita.

A irin wurin da ya tsinci kansa watau gidan yarin na Kirikiri, komai biya ake, ciki kuwa harda dukkan bayanan da yake samu a wurin wannan gandiroban mai suna Kunle. Kunle dai kakarsa ce ta yanke saqa saboda a cikin kwana hudu kacal da kawo fursunan ya samu fiye da naira dubu goma sha biyu wurin wannan baqon fursunan wanda kai da ganinsa duba daya zakai masa kasan ya gama jiquwa a cikin naira kai harma da dalar amurka a cewar shi Kunle din, kuma yana fata wannan fursunan ya jima nan cikin gidan, abin nupi yana so baqon fursunan ya dade a gidan yarin tunda zuwa yanzu, ajiyarsa kawai aka kawo kafin ma a fara zaman kotu, lallai wannan laifinsa babba ne! Kunle ya fada a zuciyarsa, yana mai sake gamsuwa bayan ya tuna labarin da aka bashi a safiyar ranar da aka kawo baqon.

Duk mugun fatan nan da Kunle keyiwa baqon fursunan ba domin komai bane ba sai don a cewarsa, Seema yarinyar da yake matuqar so, ta fara bashi fuska daga jiya tunda ya bude mata bakin aljihu a ire iren kudaden da yake samu a wurin shi wannan fursunan, aduk lokacin daya nemi wata buqata.

*****

Kyakkyawar matashiyar budurwa ce ajin farko wacce bazata wuce shekarun haihuwa ashirin da hudu zuwa da biyar ba, amma yanayin hutu, wayewa da budewar ido a mu’amalolin rayuwa sune abu na farko da zasu ja hankalin mutum zuwa gareta walau da namiji walau diya mace yar uwarta.

DEEJAH, wacce ke amsa sunan haihuwa Khadijah Muhammad Lamido ta kasance irin nutsassun ‘yanmatan nan ne marasa hayaniya. Mace ce ita mai sanyin hali, mace ce kuma mai aji bi ma’ana class.
Ban da kyawun fuska, diri da zazzakar murya da Allah Yayi mata baiwa dasu, da’da’dan lafuzan ta ga wanda takewa magana kadai sun isa su saka daruruwan talikai maxa rububin samun ta a rayuwa.

Doguwar rigar da akewa laqabi da abaya ce a jikinta, amma ba irin wacce ke fito da surar jikin mace ba domin janyo hankalin maza ga fadawa fitina ba.

Idanunta boye suke saboda qaton gilashin ido baqi na rana wato (sun glasses) da take sanye dashi duk kuwa dama dai ta jima da baro cikin ranar, tana zaune ne kan kujera a dakin baqi na ziyara a gidan yarin na Kirikiri dake jihar ta legas. Gilashin nata ya taimaka kwarai wurin tona asirin dogon siririn hancinta da dan tsukakken bakinta me dauke da cute pink lips inji turawa..

“Why are you here?.

Tambayar da ABOU ADEM ya maka mata kenan tun bai kai ga zama ba.

“Calm down!

Ta fadi  cikin siririyar muryarta daga zaune tana me fuskantarsa.

“Don’t!.
“Don’t you dare tell me to calm down..
Ya fada cikin fushi kuma cike da gajiyawa.

“In bed, I just ask what’s her mileage?
In return with fear she’s asking what is my aim?

“This is a statement I wrote, said, published and sold out. Damn every penny I made let it cost me!..
But I didn’t do it.

Ya qarasa maganar tasa a hankali kamar mai rada, ankara da yayi cewar hankulan sauran mutanen dake wurin ya dawo kansu.

“Dakata!..

Deejah tayi qoqarin tsayar da bakin baturen kyakkyawan saurayin watau Abou.

“You’re a writer. We both know that, but we also know that you are more than a writer. At least me and you know that.

Deejah ta fada tana me zare gilashin idanunta.

“Don’t go there.
Abou Adem ya fada yana kallon ta ido cikin ido.

” Khadijah are you threatening me?..

Abou Adem ya jefowa Deejah tambayar bazata bayan ya tsaida idanunsa a kanta yana nazari na wasu ‘yan daqiqu da baza su wuce biyar ba.

Batason irin wannan kallon nasa, domin akwai effects din da kallon nasa yake dasu a gareta.

“I’m not threatening you, we are only talking don’t let it be a threat my dear..

Deejah ta amsa masa tana mai miqewa domin tana ankare da yanayin kallon da Abou din yake binta da shi, sa’an nan shima gandiroban dake tsaye gefen su wato Kunle, tun shigowarta dakin ziyarar gaba daya bata yadda dashi ba.

“Goodnight. I’m.. “Khadijah why are you here?..

Ya katse mata bankwanan da take qoqarin yi masa da dai wannan tambayar farkon da yayi mata tun fitowarsa, wacce kuma bata amsa masa ba.

“I’m here to pay you a simple visit
Ta fadi tana kallonsa with all sincerity

“In prison?!.. Ya tambayeta in total disbelieve

“Yes.. Ta sake amsa masa

Shiru yayi ba tare da ya sake cewa komai ba.

“I’m off! Goodnight

Deejah tace, tana mai qarasa tattare kayanta dake kan teburin dake girke a gabansu. Bayan ta rataya handbag dinta, ta sake saka hannu ta dauki gilashin ta da makullin mota, ta sake duban Abou Adem

“I’ve a night shift..

“You still freelance?..

Ya tambayeta da mamaki a tone dinsa (wato amon muryarsa)..

“Is there anything wrong with that?

Deejah ta mayar masa da amsarsa da tata tambayar.

Wani murmushin rainin hankali ya saki wanda ba Deejah ba hatta Kunle abin ya bashi mamaki domin murmushin, murmushine irin mai nuna ” bana cikin matsala” din nan.

Da yake ta saba da ire ire rainin hankalinsa kawai sai ta basar.

She looked at him with a death glare as she almost gave up to his lustful stare. (Wannan wani sirri ne a tsakaninsu) Sirri da suka saba kashewa su haqa rami su binne, yayin da suka ga dama kuma, su haqe abinsu su sabuntashi su sake mayarwa su rufe.

“Good night
“Sai da safe.

Tace masa, tana mai juyawa tayi ficewarta daga dakin ziyarar, a yayin da yake zaune still yana mai qurawa bayanta idanu har saida ta bacewa ganinsa.

Yana sane yaqi bari su zanta sosai da ita, yasan Deejah yasan halinta. Yanzu he need answers and very quick ones for that matter.

Me taxo yi?..

Ya sake maimaita tambayar a ransa. Koma waye ya fada mata an kamashi isn’t important tunda ai dama akwai few mutanen da suka sanshi da ita. Watau duk da tabarshi it means tana bibiye da rayuwarsa? Wata tambayar ta sake fado masa, tsaki yayi yana mai miqewa da barin dakin don komawa ciki.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.1 / 5. Rating: 13

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Duniyar El-Dorado 2 >>

23 thoughts on “Duniyar El-Dorado 1”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.