Skip to content
Part 24 of 27 in the Series Falsafa by Haiman Raees

TSUMAYIN SO 

Sarai a rai kin ka buɗe kundi na sonki ki barni a maye,

Farin tsimi ciki na so a tulin giya da tarin kwallaye..

Garai-garai walƙiyar wushiryarki don ta na kwana tsimaye,

Ina ta dakon ƙasa ta ɗan jijjiga da kin saka sawaye.

Jiran maraicen dare nake tunda na bi jinsin kuraye,

Ina jiran wai cikin sahara in hangi hudar jan ganye.

Ƙwarai idan kin ka ba ni damarki zan riƙe babu alaye,

Narai-narai nai da zuci duk dubi sanki yai mata jirwaye.

Iyo nake ƙorama ta kwarmin ido kamar za ya tsiyaye,

Saboda kuka a kanki launin ido ya koma koraye.

Abin fahar ne a sonki ai min naɗi na sarkin dolaye,

Katoɓarar so idan na tafka a sa ni layin wawaye.

Jiɓi jiki dukka ya jiƙe don ɗumin kwaranya ta hawaye,

Ki zam garen guguwa ki ɗauken in daina kwanan soraye.

Ki ban alama ta cin budurci a ba ni sunan angwaye,

In rayu nan duniyarki tamkar baru a jejin tsuntsaye.

Taɓara ya ta ɗan yaye!

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Falsafa 23Falsafa 25 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×