Ɗakin taron cike yake da mutane mabambanta. Kowa da abin da yake gudanarwa; amma akasari fuskokinsu cike suke da farinciki mara misaltuwa. Ɗauke kanta ta yi gefe tana jin ƙwalla na taruwa cikinsu, ba ta hanata zuba ba duk da muhimmancin wannan ranar gareta sai dai ba don tana gudun yi wa rayuwarta rinton zunubi ta hanyar butulcewa Ubangijinta ba, da sai ta ce "Ranar ba ta da wani muhimmanci a duniyata."
Kamar an ce ta ɗaga kanta ta hango kawunta, walwala ce cike a fuskarsa, gefansa kuma mutumin da ya zamowa duniyarta katanga ne, bayan zubewar dirkar da ta. . .
I love everything about this application. Thank you