"Wai ni kike cewa na taimake? Yanzun ke dan jakanci duk darasin da na dinga baki ba ki kiyaye ko guda ba? Ba ki tuna ranar da na baki ƙyalle ba? Na baki ne da niyya biyu shiyasa har na ambato miki malami ne ya bani ayi asirin da kuɗi zasu dawo. A zatona kalmar asiri da na ambata zai sa ki tsorata ki gujeni ko da na dawo miki duk abinda zan furta miki ba za ki ji ƙaina ba balle ma ki sake saurarata, da ace kin yi haka da yanzu ba na nan inda kike. Kina. . .